Ana yi wa masu fyade sassauci — Aisha Buhari

Asalin hoton, Getty Images
Uwar gidan shugaban Naijeriya, Aisha Buhari, ta nuna damuwa game yadda ake sassauta wa masu yi wa mata fyade a Najeriya, tana mai kira da a tsaurara dokokin hukunta wadanda aka samu da laifin.
Uwar gidan shugaban kasar dai ta buga misali da wata shari'ar da aka yi a jihar Kano inda aka ci wani mutum tarar naira dubu goma kacal bayan an same shi da laifin yi wa wata jaririya fyade.
Darakatan watsa labarai a ofihsinta, Alhaji Suleiman Haruna, ya ce daman an san Aisha Buhari da magana kan cin zarafin da ake yi wa yara kanana da kuma mata yana mai kara wa da cewa: "A ce mutum ya yi wannan mummunar ta'asa sannan ace an yanke mishi hukuncin ya biya tara ta naira dubu goma, toh ka ga wannan doka, babu mamaki sanda aka yi ta dubu goma wani abu ne, amma a yanzu kam wanda ya yi irin wannan laifin bai kamata a ce ya bayar da dubu goma ba.
"Shi ne dalilin da ya sa ta ce ya kamata a duba wadannnan dokokin saboda su yi daidai da zamani. "
Alhaji Suleiman ya ce uwar gidan shugaba kasar tana son a gyara dokokin ta yadda duk wanda aka samu laifin cin zarafin mata da kananan yara ba zai sake yin lafin ba.
A Najeriya dai ana fama da matsalar cin zarafin mata da kananan yara ta hanyar fyade.
Karanta wasu labaran masu alaka.

Asalin hoton, Twitter/@AishamBuhari







