Matsalar fyade a Ghana

Asalin hoton, Getty Images
Wata yarinya mai shekara 4 na kwance a asibiti a Ghana cikin halin rai kwa-kwai, mutu kwa-kwai, bayan cin zarafinta da aka yi ta hanyar Fyade.
Mahaifiyar yarinyar ta ce sun shaida wa Mai-unguwar yankin sunan wanda suke zargi da wannan ta'asa.
Amma abin mamaki sai ya ce babu abin da za a iya yi wa mutumin, saboda abin bautar su, ya ayyana mutumin a matsayin mai gaskiya.
Wannan lamari dai ya janwo muhawara a shafukan sada zumunta da gidajen Rediyon kasar.
Matsalar fyade dai tayi kamari a wasu kasashen Afrika, ciki har da Nigeria, inda ake samun batutuwan da suka shafi yi wa yara mata kanana fyade.







