Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An yi wa 'yan matan Amarya lugudan wuta a Yemen
Wasu mata goma da suke halartar daurin aure sun mutu sakamakon lugudan wuta ta sama da aka dora alhaki akan rundunar kawance da Saudiya ke jagoranta.
Wasu majiyoyi a kasar sun ce matan suna tafiya ne a kafa yayin da suka bar wurin bukin daurin auren a tsakiyar Lardin Marib, inda 'yan tawayen Houthi ke gwabza fada da dakarun gwamnati.
Kawo yanzu dai hadakar dakarun kawancen, wacce taimaka ma dakarun gwamnatin Yemen din, ba ta ce komai ba game da lamarin.
Lamarin ya auku ne kwana guda bayan an kashe wasu fararen hula goma sha biyu a wani lugudan wutan ta sama a wata gunduma inda ake kazamin fada.
An kwashe shekaru ana fafata wa tsakanin dakarun gwamnatin Yemen da kuma 'yan tawayen Houthi.
Saudiyya dai tana jagorantar yaki da 'yan tawayen ne.