Saudiyya ta saki Yerima Miteb bayan ya amince ya biya $1bn

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomi a kasar Saudiyya sun saki Yarima Miteb bin Abdullah bayan ya kwashe makonni uku a tsare bisa zargin cin hanci da rashawa.
Yarima Miteb na cikin mutum 200 da suka hada da yarimomi da ministoci da kuma manyan 'yan kasuwa da aka kama a kasar a ranar 4 ga watan Nuwamba, bisa zargin cin hanci da rashawa.
Ya kuma amince ya biya fiye da dala biliyan daya ga hukumomin kasar.
Jami'ai sun ce akwai wasu mutum uku da suka amince su biya gwamnati makuden kudade domin a sake su.
Kawo yanzu dai Yarima Miteb, wanda ake kallo a matsayin daya daga cikin yarimomi da za su gaji saurautar kasar bai ce komai ba kan al'amarin.
Babu tabbaci a kan ko ya na da 'yancin yin walwala ko kuma har yanzu yana zaman daurin talala ne.
Yarima Miteb bin Abdullah mai shekaru 65 na daga cikin fitattun Yarimomi da kwamitin yaki da cin hanci da rashawa ya tsare karkashin jagorancin dan uwansa, Yarima Mohammed bin Salman mai shekaru 32.
Haka kuma Yarima Miteb shi ne tsohon ministan tsaron cikin gida mai kula da dakarun tsaro su kimanin 100,000.
Daga cikin ayyukansa na ministan tsaron cikin gida shi ne samar da tsaro ga manyan sarakuna, sai dai an sauke shi daga kan mukaminsa 'yan sa'o'i kafin a tsare shi.
Wani jami'i cikin masu binciken ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa, an cimma yarjejeniya da Yarima Miteb bayan ya amince akwai hannunsa a wata badakala ta cin hanci.
Kawo yanzu hukumomi ba su bayyana sunayen sauran mutane 208 da babban mai shigar da kara ya ce ana yi musu tambayoyi ba.
Haka kuma ba a bayyana tuhume-tuhumen da suke fuskanta ba, kuma ana kyautata zaton ba a ba su damar ganawa da lauyoyinsu ba.
Rahotanni sun ce an tsare Yarima Miteb ne a Otel din Ritz-Carlton da ke Riyadh tare da dan uwansa, Yerima Turki bin Abdullah tsohon gwamnan Riyadh.
Sauran wadanda aka tsare dasu sun hada da attajirin nan mai zuba jari Yarima Alwaleed bin Talal da Yarima Alwalid al-Ibrahim mai gidan talbijin na MBC.
Akwai kuma Amr al-Dabbagh, tsohon shugaban hukumar kula da harkokin kasuwanci da kuma Khalid al-Tuwaijri, tsohon shugaban kotu.
A wata hira da jaridar New York Times, Yarima Mohammed bin Salman ya ce: ''Kashi 95 cikin 100 na wadanda ake tsare da su sun amince su mikawa gwamnati kudade da kadarori bayan mun nuna musu takardun da muke da su.''

Asalin hoton, Reuters
Wasu 'yan kasar Saudiyya dai sun yi marhabin da matakin yaki da cin hanci da rashawa da aka kaddamar.
Kuma da yawa daga cikin 'yan kasar na fatan cewa gwamnati za ta yi amfani da kudaden da aka kwato don yin ayyukan da za su amfani al'umma.












