Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An kara kashe sojojin Kamaru
Hukumomi a Jamhuriyyar Kamaru sun ce an kashe sojojin kasar hudu a yankin da ake amfani da harshen Ingilashi dake kudu maso yammacin kasar.
Wasu majiyoyin a rundunar soji sun ce an kashe jami'an sojojin ne da sanyin safiyar Laraba a yankin Mamfe.
Hakan ya kara yawan sojojin kasar da aka kashe a yankin zuwa takwas cikin wata guda.
An dai shafe watanni ana tashe-tashen hankula sakamakon zargin nuna wariya daga bangaren da ake amfani da harshen Faransanci da suka fi rinjaye.
An kuma kashe wasu masu zanga-zanga yayin da aka tsare wasu mutane da dama.
Tashe-tashen hankula da ake fama da shi a yankin kan zargin nuna wariya ya haddasa zaman dar-dar, lamarin da ya janyo wasu neman ballewar yankin daga Jamhuriyar Kamaru.
Sai dai shugaba Paul Biya ya yi kakkausar suka akan masu neman ballewar, inda ya sanya dokar takaita zirga-zirga tare da tsaurara matakan tsaro a yankin.