Iran na takalarmu da yaki - Saudiyya

Lokacin karatu: Minti 2

Yariman Saudiyya Mohammed Bin Salman ya zargi Iran da talakar yaki ta hanyar samar da makamai masu linzami ga 'yan tawayen Yemen.

Yariman ya danganta matakin a matsayin yaki, kamar yadda kafofin yada labaran Saudiya suka ambato shi yana shaidawa sakataren harakokin wajen Birtaniya Boris Johnson ta wayar tarho.

A ranar Asabar an kakkabo wasu makamai masu linzami kusa da Saudiyya.

A nata bangaren, Iran ta musanta zargin bai wa 'yan tawayen Houthi makamai wadanda ke fada da gwamnatin Yemen da ke samun goyon bayan dakarun kawance da Saudiya ke jagoranta.

Ministan harakokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif ya danganta kalaman Yariman a matsayin ma su hatsari.

Wasu kafofin yada labarai da ke goyon bayan 'yan tawayen Houthi sun ruwaito cewa mayakan sun harba Burkan H2, wani nau'in makami mai linzami a filin saukar jirgi na Sarki Khaled da ke arewa maso gabashin Riyadh, wanda ke nisan kilomita 850 daga kan iyaka da Yemen.

Sai dai Saudiyya ta yi nasarar kakkabo makamin, yayin da wasu tarkacensa suka warwatsu a filin saukar jirgin.

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta ce harba makamin mai linzami a tashar jirgin saman da fararen hula suke, ya kasance aikata laifukan yaki.

Yarima Mohammed wanda ya yi Allah-wadai da harba makamin, ya ce yunkurin gwamnatin Iran na samar da manyan makamai ga 'yan tawayen Yemen tamkar mataki ne na kaddamar da yaki akan masarautar Saudiyya.

Minsitan harakokin wajen Iran Javad Zarif, ya yi tir da kalaman na Yarima a zantawar da ya yi da Mista Johnson ta wayar tarho bayan ministan harakokin wajen na Birtaniya ya tattauna da Yarima a ranar Talata.

Iran da Saudiyya sun dade suna yakin cacar-baka musamman kan karfin ikon mulki a Gabas Ta Tsakiya.

Kuma duk da cewa kasashen ba su taba yaki da juna ba amma a fakaice suna yakar juna ta hanyar goyon bayan bangarorin da ke rikici a wasu kasashe.