Zan kakkabe tsattsauran ra'ayin addini a Saudiyya - Yarima

Yarima mai jiran gadon masarautar Saudiyya, Mohammed bin Salman, ya ce dawo da sassaukan ra'ayin addinin musulunci na daga cikin shirye-shiryensa na zamanantar da kasar.

Ya shaida wa manema labarai cewa kashi 70 cikin 100 na al'ummar kasar 'yan kasa da shekara 30 ne, kuma sun fi son rayuwa irin wacce "addinin musulunci ya bayyana yadda za a zauna da juna lafiya".

Yariman ya sha alwashin kakkabe duk wani abu da ke da alaka da tsattsauran ra'ayin addinin musulunci nan ba da jimawa ba.

Sai dai Yariman bai yi wani karin bayani kan abin da yake nufi da 'tsattsauran ra'ayin addinin musuluncin' da ya ke son kawar wa ba.

Wadannan kalaman nasa ka iya bude sabon babi a muhawar da ake yi na irin salon da kasar ke son dauka a nan gaba.

Ya yi wadannan kalamai ne bayan da ya sanar da zuba jarin dala biliyan 500 don gina wani sabon birni a kasar.

Birnin mai suna NEOM zai kasance ne a yankin arewa maso yammacin gabar kogin maliya, kusa da iyakar Masar da kuma ta Jordan. Girman wajen kuma zai kai mita 26,500.

A Saudiyya dai yana daga cikin dokar kasar a tabbatar da cewa mutane sun yi shiga ta kamala kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

A shekarar da ta gabata ne Yarima Mohammed ya kaddamar da wani faffadan shiri na samar da sauye-sauye a zamantakewa da tattalin arziki a kasar wanda aka yi wa lakabi da "Vision 2030".

A bangaren wadannan shirye-shirye dai, yariman mai shekara 32 ya gabatar da bukatar sayar da wani bangare na kamfanin man fetur na kasar, Saudi Aramco, da kuma kirkirar asusun ajiyar rarar kudi na kasa saboda bacin rana mafi girma a duniya.

A watan Satumba ne kuma mahaifinsa Sarki Salman, ya sanar da janye dokar da ta haramta wa mata tukin mota daga shekara mai zuwa, duk kuwa da kin goyon bayan hakan da wasu malaman kasar suka yi.

Gwamnatin tana kuma son zuba jari a bangaren shakatawa.

A yanzu haka ana sa ran nan ba da jimawa ba za a sake bude gidajen rawa da gidajen kallo na sinima a kasar.

Yarima Mohammed ya kare wadannan sauye-sauye a wani taron tattalin arziki da aka yi a Riyadh ranar Talata, wanda aka yi da masu zuba jari da manyan mutane.

"Muna dab da komawa yadda muke a baya - kasar da ke bin matsakaicin ra'ayin addinin musulunci mai kyawun mu'amala da ko wanne addini, da al'adu da mutane a duk fadin duniya," a cewarsa.

Ya kara da cewa: "Muna son mu yi rayuwa kamar kowa. Rayuwa wacce addininmu ya bayar da damar yin kyakkyawar mu'amala da kowa."

"Kashi 70 cikin 100 na al'ummar Saudiyya 'yan kasa da shekara 30 ne, kuma maganar gaskiya ba za mu bata shekara 30 masu zuwa wajen fama da akidun da za su rusa mu ba. Za mu ruguza su a yau kawai."

Yariman ya kuma jadda cewa Saudiyya ba haka take ba a shekarar 1979, lokacin da aka yi juyin-juya hali na musulunci a Iran, kuma mayakan sa kai suka mamaye Masallacin Harami na Makka.

Bayan wannan lokaci ne aka haramta duk wani abu da ya danganci nishadi a Saudiyya, kuma aka bai wa malamai damar kula da abubuwa kan rayuwar al'umma.