Tashin farashin man fetur ya sa kasashen OPEC darawa

OPEC ta ce farashin man fetur ya tashi ne saboda karin bukatar man a kasuwannin duniya

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, OPEC ta ce farashin man fetur ya tashi ne saboda karin bukatar man a kasuwannin duniya

Farashin danyen man fetur ya yi tashin da bai taba yi ba cikin fiye da shekara biyu a duniya, inda ya kai dala sittin a kan kowacce ganga.

Faduwar da farashin man ya yi a baya ta haddasa koma-bayan tattalin arzikin kasashe masu arzikinsa irinsu Najeriya, lamarin da ya jefa al'ummominsu cikin kunci.

Babban sakataren kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta duniya wato OPEC, Alhaji Muhammadu Sanusi Barkindo, ya shaida wa BBC cewa, kasuwa na kara bunkasa a hankali, su kuma suna kara damara.

A tattaunawa tsakanin kasashen da ba sa cikin kungiyar kamar Rasha don lallai su tabbatar cewa an tsaya a kan yarjejeniyar da aka cimma, in ji shi.

Ya ce abin da ya sa farashin man fetur din ya tashi shi ne yadda aka yi amfani da yarjejeniyar da aka cimma da kasashen kungiyar da ma wadanda ba sa cikinta.

Yarjejeniyar ta kunshi rage samar da ganga miliyan daya da dubu dari takwas, sannan kuma a watanni shida da suka wuce an samu karuwar bukatar man a kasuwannin duniya.

Muhammadu Sanusi Barkindo, ya ce wani karin dalilin kuma shi ne, shugabannin kasashen kungiyar OPEC din da na Rasha, na kara gargadin cewa lallai a guji sake faruwar abin da ya faru a shekarun da suka wuce.