Matakin rage hakko danyen mai bai shafi Najeriya ba— OPEC

Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur wato OPEC ta yi karin haske kan matakin da ta dauka tare da wasu manyan kasashe masu arzikin man amma wadanda basa cikin kungiyar irin su Rasha, na ci gaba da rage adadin danyen man fetur da ake kai wa kasuwar duniya.

A wannan makon ne bangarorin biyu suka kara wa'adin ci gaba da rage danyen man da watanni tara, bayan karewar wa'adin watanni shida da suka cimma yarjejeniya a kai tun farko.

Alhaji Muhammad Sanusi Barkindo, shi ne Babban Sakataren kungiyar ta OPEC, ya kuma yi wa Is'haq Khalid karin bayani ta wayar tarho:

Bayanan sautiAlhaji Muhammad Sanusi Barkindo, babban Sakataren kungiyar OPEC