Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Nigeria ta fara shari'ar 'dubban 'yan Boko Haram'
A ranar Litinin din nan ce aka fara yi wa wasu dubban mutanen da ake zargi 'yan kungiyar Boko Haram ne shari'a a Najeriya.
Wata majiya a ma'aikatar shari'a ta shaida wa BBC cewa alkalai hudu ne suka fara yi wa mutanen shari'ar a asirce a wata cibiya ta sojoji da ke garin Kainji a jihar Neja da ke arewacin kasar.
Ana sa ran yi wa kashin farko su kimanin 1,670 shari'a cikin makwanni da ke tafe, daga bisani kuma a yi wa wasu kimanin dubu biyar nasu shari''o'in a nan gaba.
Wannan ne karon farko da ake yi wa mutane da suka kai wannan adadi shari'a kan zargin alaka da Boko Haram.
Ministan shari'ah na Najeriya, Abubakar Malami ya ce ba karo guda za a gurfanar da duk mutanen da ake zargin a gaban kotu ba.
"Ba za su bayyana tare lokaci guda a gaban shari'ah ba. Kowanne mutum shi kadai za a yi masa shari'arsa daban, sai dai fa idan ya aikata laifin da ake zarginsa ne tare da wani."
Hukumomi kuma sun ce za a yi wadannan shari'o'i ne a cibiyoyin tsare mutanen da ke sassan kasar, maimakon a kotuna.
Wani Barista Muhammad Alhassan na daga cikin lauyoyin da suka taba tsaya wa mutanen da aka zarga 'yan kungiyar Boko Haram ne a gaban kotu cikin 2010 ya ce sun yi kokari su tabbatar da kare 'yancin mutanen a matsayinsu na bil'adama.
Ya ce tsarin mulkin kasa ya ba mutanen kariya, a matsayinsu na wadanda ake zargi.
"Ba yadda za a yi a ce don kawai an kama mutum, a tabbatar da laifin (da ake zargin)sa da shi, sai dai fa idan an gurfanar da shi a gaban kotu."
Barista Muhammad Alhassan ya ce a shekara ta 2010 ba a tuhumi mutanen da ake zargi da aikata ta'addanci ba, don kuwa babu kalmar a cikin tsarin mulki.
"Ai babu ma wannan kalmar a cikin dokokin Najeriya, daga baya ne aka yi wannan doka da ake kira terrorism act."
Kimanin mutum 7,000 ne da ake tsare da su a cibiyoyi daban-daban a Najeriya, bisa zargin su 'yan Boko Haram ne.
Wani da aka taba tsarewa kan zargin shi dan Boko Haram ne ya fada wa wakilin mu Ishaq Khalid cewa tsawon shekara uku da aka kama shi, dangi da iyalansa ba su iya sanin inda yake ba.
Ya ce "Babbar matsalar ita ce, a tsawon rayuwar duka, ba za ka gana da kowa ba, kuma wani bai san inda kake ba. Kai kadai ne kawai ka san kana raye."
"Wallahi wannan al'amari ya sa rayuwata ta tabarbare, in ji mutumin wanda ya bukaci a sakaya sunansa.
Ya ce daga baya an sake shi, bayan kammala bincike, inda aka bayar da shi beli kuma har yanzu hukumomi ba su sake waiwayarsa ba.
Irin wannan shari'ah da aka taba yi cikin jihar Bauchi a shekara ta 2010, ba ta yi nasara ba, saboda daga bisani wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun fasa gidan yarin Bauchi kuma suka kubutar da wadanda aka fara yi wa shari'ar.