Nigeria: 'Kungiyar Boko Haram ta tarwatse'

Boko Haram kungiya ce ta masu dauke da makamai da ke fitowa a lokaci zuwa lokaci a shafin intanet, sannan kungiya ce da ta yi kaurin suna.

Haka kuma kungiyar na ci gaba da ayyukan ta'addanci a arewacin Najeriya, inda hare-haren da take kai wa, musamman ma na kunar bakin-wake ke karuwa, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane a wannan shekarar.

Sai dai BBC ta samu wata dama da - ba kasafai ake samun irinta ba, na bayanan sirrin kungiyar daga bakin wani dan kungiyar da ya tsere a watan da ya gabata.

Ya bayyana cewa kungiyar ta warwatsu, abin da ke nuni da cewa kungiyar na cikin matsala.

Wakiliyar BBC Stephenie Hegarty ta gana da mutumin wanda aka sauya wa suna zuwa Mohammad, saboda daililan tsaro a birinin Maiduguri, birnin da ya yi suna a yakin da ake yi da Boko Haram, kuma inda kungiyar ta yi barna matuka kafin a kore ta daga cikin birnin.

Muhammed na hannun jami'an tsaro tun bayan da ya gudo daga maboyar kungiyar da ke dajin Sambisa a watan jiya. Ya kwashe tsawon shekara uku tare da Boko Haram kuma an kai hare-hare shida tare da shi. Amma ya ce shi kurtu ne a kungiyar.

Tun da fari dai sun zauna ne a mahaifarsa wato a garin Banki, inda yake sayar da wayoyin salula. Amma wata daya bayan ya shiga kungiyar ne kuma aka tursasa musu komawa Sambisa.

Muhammad ya zamo mai bai wa matar wani babban kwamanda kariya, ta hakan ne ya san sirrin kungiyar.

Ya bayyana cewa a matsayinsa na kurtu bai taba ganin shugabansu Abubakar Shekau ba, saboda Shekau na turo 'yan aike ne daga inda yake boye zuwa wajen kwamandojinsa.

Aikin Muhammed dai shi ne kare Aisha matar kwamandan, amma ba sunanta na gaskiya ba ne.

Sai dai Aisha ta fahimci cewa Muhammed daban yake da sauran 'yan kungiyar.

Ta gane cewar yana da tausayi da saukin kai. Saboda haka sai ta gaya masa cewar tana son ta gudu daga dajin.

Shi ma ya shaida mata cewa yana son ya tsere, daga nan ne suka fara shirya yadda za su yi.

Muhammed yana tsoron cewa idan ya mika wuya sojoji ba za su barshi ba, amma Aisha ta gaya masa cewa babu komai.

Rannan suna cikin shirin tserewa, sai aka kama su aka kuma daure su.

Amman Aisha ta samu ta kwance kanta, sannan suka gudu kuma suka mika wuya ga sojin Najeriya.

Aisha da Muhammed sun ce sun samu tserewa ne saboda kungiyar ta watse.

Mamman Nour wani babban kwamanda ne kuma yana daga cikin jiga-jigan kungiyar.

A cewar Mohammed kwamandan ya bar kungiyar ne saboda babbancin akida. Kuma ya tafi da wasu kayayyakin yakin kungiyar.

Mohammed ya ce Mamman Nur ya bar Shekau ne saboda bai yarda da irin hare-haren kunar bakin waken da yake sawa ana kai wa fararen hula ba.

Sai dai a lokacin da Aisha da Mohammed suka tsere daga dajin Sambisa ba su kadai bane. Akwai wani kyakkyawan yaro da ya biyo su.

Aisha ba ta san sunan yaron ba, amma ta tuna cewa ta taba ganinsa tare da mahaifiyarsa.

Yayin da take magana da BBC, Aishar da Mohammed suna kallon yaron cike da kauna, tashin hankalin da suka fuskanta ya sa sun zamo tamkar iyali guda.