Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya sa ba za mu saki Zakzaky ba – Osinbajo
Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya Yemi Osinbajo ya kare zarge-zargen da ake yi wa gwamnatin Muhammadu Buhari na take hakkin bil'adama da rashin martaba fannin shari'a.
A wani jawabi na bidiyo da aka wallafa a shafin gwamnati na Twitter, wanda ya yi da jaridar Guardian, Mista Osinbajo ya ce shi mutum ne da ke tsayawa tsayin daka wajen ganin an mutunta umarnin kotu.
Ya nuna cewa dalilin da ya sa gwamnati ba za ta saki shugaban kungiyar 'Yan Uwa Musulmi ta 'yan Shi'a Ibrahim El-Zakzaky ba, shi ne saboda ta daukaka kara kan hukuncin kotun da ya ce a sake shi.
Gwamnatin Buhari na shan suka kan yadda ta ke cigaba da tsare El-Zakzaky, da jagoran 'yan awaren Biafra Nnamdi Kanu da tsahon mai ba da shawara kan harkokin tsaro Kanar Sambo Dasuki.
Mutanen uku sun shafe wata da watanni a hannun hukumomi duk da cewa kotu ta ba da umarnin a sake su a lokuta daban-daban.
Mista Osinbajo ya ce "duk lokacin da kotu ta ba da wani umarni, to ya zama dole a yi aiki da shi.
Sai dai kuma muna da damar da za mu daukaka kara," in ji shi.
A watan Disamban bara ne wata kotu ta yanke hukuncin cewa tsarewar da ake yi wa Sheikh El-Zakzaky ta saba wa doka kuma ta umarci a sake shi cikin kwana 45, sai dai gwamnati ta yi burus da umarnin.
An kama shi ne a watan Disambar shekarar 2015, bayan wani rikici da sojoji suka yi da mambobin kungiyarsa a Zariya, inda aka kashe daruruwan mabiyansa.
Sai dai har yanzu ba a tuhume shi da aka laifin komai ba.
Shi kuwa Nnamdi Kanu yana tsare ne saboda zargin cin amanar kasa da ke da alaka da fafutikar neman kafa kasar Biafra.
Yayin da shi kuma Dasuki ke fuskantar shari'a kan zargin almundahana da cin hanci, zargin da ya musanta yana mai cewa siyasa ce kawai.