Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Nigeria - An cire Ali Ndume daga shugaban masu rinjaye
Majalisar Dattawan Najeriya ta sanar da cire Sanata Mohammed Ali Ndume a matsayin shugaban masu rinjaye a majalisar. Inda ta maye gurbinsa da Sanata Ahmed Lawal.
Shugaban majalisar, Bukola Saraki ne ya karanta wasikar sauya shugaban masu rinjayen a zaman majalisar a ranar Talata.
Jam'iyya mai mulkin kasar ta APC ce ta nemi a sauya Ndume da Ahmed Lawal, a lokacin wani taron 'ya 'yan jam'iyyar da ke majalisar.
Sanata Ahmed Lawal dai ya nemi zama shugaban majalisar dattawan, amma bai yi nasara ba.
Lamarin da ya raba kan 'yan jam'iyyar ta APC a majalisar.
Sanata Ndume ya shaida wa BBC cewa ba a tuntube shi a kan sauyin ba, kuma babu wanda ya gayyace shi taron 'yayan jam'iyyar da ke majalisar.
Babu wasu kwararan dalilai da aka bayyana na sauyin.