An fara daukar matakan kare afkuwar ambaliyar ruwa a wasu jihohin Najeriya

Ambaliyar ruwa

Asalin hoton, Getty Images

Yayin da damunar bana ta fara kankama, hukumomi a wasu jihohin arewacin Najeriya sun fara daukar matakai domin gujewa illolin ambaliyar ruwa a damunar bana a yankunansu.

Jihohi kamar Jigawa da Yobe da Neja da dai sauran su, tuni suka fara gyaran magudanan ruwa da muhallai domin kaucewa afkuwar bala'in ambaliya ruwan a bana.

Jihohin sun yi la’akari ne da irin dumbin asarar da ake tabkawa da ta shafi rayuka da dukiyoyi sakamakon ambaliyar ruwa shi ya sa gwamnoni wasu daga cikin jihohin arewacin Najeriyar suka dauki irin wadannan matakai.

Jihar Yobe wadda ke a arewa maso gabashin Najeriya kuma ta ke da babban kogi na Komadugu da manyan koramu da kuma rafuka, tuni gwamnatin jihar ta dauki matakan kandagarki don kare rayuka da kuma dukiyoyin al’ummar jihar daga masifar ambaliyar ruwa.

Jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin Najeriya kuwa, tuni gwamnan jihar Umar Namadi, ya bayar da umarnin ga kwamishin muhalli na jihar domin ya kai ziyara wuraren da ke da yiwuwar fuskantar ambaliyar ruwa don daukar matakan da suka dace.

Dr Nura Ibrahim Kazaure, shi ne kwamishinan muhalli na jihar ta Jigawa, ya shaida wa BBC cewa, irin matakan da suka dauka don kaucewa ambaliyar ruwa.

Ya ce, daga cikin matakan an kafa kwamitin na masana wadanda za su kawo dauki wajen hana afkuwar ambaliyar inda kwamitin ke amfani da wasu motoci dake shiga wuraren da ke da tarin ruwa don duba ko akwai wajen da kasa ko yashi ya toshe ko hana ruwa wucewa sai motar ta kwashe ta kuma tabbatar da tsaftace hanyar Ruwan.

Dr Nura Ibrahim Kazaure, ya ce,” Muna nan muna kokarin ganin an rufe wuraren da ke da tarin ruwa da aka fasa ake amfani da shi wajen noman rani ko kuma amfani da Ruwan domin ganin abin bai janyo wata matsala ba.”

Kwamishinan muhallin, ya ce mai girma gwamna kuma ya kuma kira kwararrun injiniyoyi da zasu fito da taswirar yadda za a yi maganin afkuwar ambaliya ta dindindin.

A jihar Neja da ke arewa ta tsakiyar Najeriya kuwa, tuni aka yi hasashen cewa kananan hukumomi 12 daga cikin 25 na jihar za su iya fuskantar ambaliyar a bana, abin da ya sa gwamnatin jihar ta dauki matakai na jan hankalin al’umma.