Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Manyan ƴan takara biyar da za su ƙalubalanci Biya a Kamaru
- Marubuci, Paul Njie
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News in Yaoundé
- Lokacin karatu: Minti 8
Kotun tsarin mulki ta Kamaru ta amince da hukuncin da hukumar zaɓen ƙasar ta yi na cire sunan jagoran ƴan hamayya ta ƙasar Maurice Kamto daga zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga watan Oktoba.
A yayin da aka ajiye ɗan takarar a gefe, an sahale wa Shugaba Paul Biya mai shekara 92 yin takara a karo na takwas a ƙasar mai arziƙin man fetur da ke tsakiyar Afrika.
Idan aka sake zaɓen shi a wani wa'adin na shekara bakwai, zai iya kasancewa a kan mulki har sai shekarunsa sun kusa 100.
An cire sunan Kamto ne bayan wani tsagi na jam'iyyarsa ta Manidem ta gabatar da wani ɗan takarar shugaban ƙasa, wanda ya bayyana cewa jam'iyyar na fama da rikicin cikin gida.
A jawabin da ya yi karon farko bayan cire shi a yammacin Alhamis, Kamto ya ce matakin da aka ɗauka ya saɓa ƙa'idar tsarin mulki kuma an yi hakan ne saboda dalilai na siyasa.
Su wane ne manyan ƴan takarar?
Cikin masu neman yin takara 83 da suka miƙa buƙatunsu ga hukumar zaɓe, 12 daga cikinsu ne kawai aka amince da su.
Hukumar zaɓen Kamaru (Elecam) ta bayar da dalilan ƙin amincewa da sauran 71 ɗin, kamar rashin cikakkun takardu, rashin biyan kuɗaɗen da ake buƙata, da kuma tsayar da ƴan takara fiye da ɗaya a cikin jam'iyya guda.
Cikin su 12, ana ganin shida daga cikinsu ne manyan ƴan takara.
1. Paul Biya
Shugaba mai ci a yanzu Paul Biya, mai shekara 92, shi ne shugaban ƙasar da ya fi kowanne tsufa a duniya.
Shi ne shugaban ƙasar tun shekarar 1982, kusan shekara 43.
Biya shi ne shugaban jam'iyya mai mulki ta CPDM wadda ta mamaye fagen siyasar ƙasar.
Ƙwararren ɗan jaridar bai taɓa rashin nasara a zaɓe ba tun da ƙasar ta koma tsarin siyasa mai jam'iyyu da yawa a shekarar 1990.
Sai dai ana zargin dukkanin nasarorinsa na cike da maguɗin zaɓe - zargin da jami'yyarsa da gwamnati ta daɗe tana musantawa.
Da ya ke sanar da aniyarsa ta sake yin takara, Biya ya ce a wa'adinsa na takwas, zai mayar da hankali ne kan kyautata rayuwar mata da matasa.
2. Bello Bouba Maigari
Bello Bouba Maigari, mai shekara 78, ƙwararren ɗan siyasa ne da ya fito daga arewacin Kamaru mai ɗimbin ƙuri'u.
Shi ne shugaban Jam'iyyar National Union for Democracy and Progress (NUDP) da aka ƙirƙiro a shekarar 1990. Ya yi aiki a ƙarƙashin gwamnatocin shugabannin ƙasar biyu -Ahmadou Ahidjo da Paul Biya.
A taƙaice ma dai shi ne firaministan Biya na farko, tsakanin shekarar 1982 da 1983.
Tun a shekarar 1997, Bouba Maigari ya kafa wata haɗaka da jam'iyyar Biya ta CPDM wadda ta taimaka musu samun ƙuri'u masu yawa daga arewaci.
Sai dai haɗakarsu ta kawo ƙarshe a watan Yuni bayan matsin da aka yi ta masa daga cikin jam'iyyarsa na yin takara.
A lokacin da ya ke tsaka da aiki a matsayin ƙaramin Ministan walwala da yawon shaƙatawa, Maigari ya miƙa takardarsa ta barin aiki, kuma ya bayyana kansa a matsayin wanda zai yi takara da Biya. A zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 1992 ma ya yi takara da Biya.
3. Issa Tchiroma Bakary
Shi ma wani tsohon makusancin Biya wanda takararsa ta zo da mamaki, shi ne Issa Tchiroma Bakary, ɗan shekara 75 da haihuwa. Shi ma ya fito ne daga arewacin ƙasar kuma ya yi tasiri sosai wajen taimaka wa Biya samun ƙuri'u daga yankin.
Bayan shafe shekara 20 yana aiki a muƙamai da dama na gwamnati, Tchiroma ya ajiye aiki a matsayin ministan ƙwadago da koyar da sana'oi domin shiga takara da Biya.
Tchiroma, wanda shi ne jagoran jam'iyyar Cameroon National Salvation Front (CNSF), ya soki tsarin tafiyar da gwamnatin Biya kuma ya yi alƙawarin bayan yin nasara zai yi wa baki ɗaya tsarin garambawul.
4. Cabral Libii
Cabral Libii, shugaban jam'iyyar Cameroon Party for National Reconciliation (PCRN), ɗaya ne daga cikin ƴan majalisun ƙasar, wanda ke takarar zama shugaban ƙasar a karo na biyu.
A shekakar 2018, ya kasance ɗan takarar shugaban ƙasa mafi ƙanƙantar shekaru, a lokacin yana da shekaru 38, kuma ya zo na uku da kashi 6 na ƙuri'un ƙasar.
Sai dai a wannan shekarar, neman takararsa ya zo da kalubale, inda Robert Kona, mutumin da ya kafa jam'iyyar PCRN, ya kalubalanci halarcin ɗan majalisar wajen jagorantar jam'iyyar.
Sai dai kuma kotun tsarin mulkin ƙasar ta yi watsi da ƙarar da Kona ya shigar, ta amince da hukuncin da hukumar zaɓen ta ɗauka na barin Libii ya tsaya takara.
5. Akere Muna
Akere Muna na ɗaya daga cikin ƴan takara a zaɓen shugaban ƙasar na 2018, sai dai gab da zaɓen ya janye daga takarar domin goya wa Kamto baya.
Sai dai a wannan karon, lauyan da ke fafutukar yaƙi da cin hanci, ya ce shi da kansa ya ke so ya kalubalanci Biya.
Akere Muna, ɗan shekara 72, ya fito ne daga zuri'ar ƴan siyasa- mahaifinsa marigayi Solomon Tandeng Muna ya yi aiki a matsayin Firaminista na yammacin Kamaru bayan samun ƴancin kai, ya kuma yi mataimakin shugaban ƙasa da kuma kakakin majalisar ƙasar.
A lokacin da yake matsayin kakakin majalisa, Solomon Muna ne ya rantsar da Biya lokacin da ya kama aiki a matsayin shugaban ƙasa bayan Ahmadou Ahidjo ya bar aiki.
Muna ya yi alƙawarin kawo ƙarshen cin hanci da kuma abin da ya kira gwamnati mara inganci wanda ya ce ya ɓata wa ƙasar suna a idon duniya.
6. Joshua Osih
Joshua Osih zai sake shiga takarar neman zama shugaban ƙasa karo na biyu kenan bayan ya yi rashin nasara a 2018.
Shi ke jagorantar jam'iyyar Social Democratic Front (SDF) bayan ya gaji jagoran adawa marigayi John Fru Ndi. Jam'iyyar ta kasance babbar jam'iyyar adawa a baya, sai dai tasirinta ya ragu sosai saboda wasu matsaloli kamar rikicin cikin gida da kuma korar ƴaƴan jam'iyyar da dama a shekarar 2023.
Osih, mai shekara 56, ya zo na huɗu a zaɓen 2018 da kashi 3 na ƙuri'un da aka jefa, a yanzu kuma yana fatan zai iya kayar da Biya saboda alƙawuran da ya ɗauka na kawo sauye-sauye a ƙasar.
Wane ne ya fi yi wa Biya barazana?
Tsawon shekaru, shugaba Biya ya yi nasarar kankane mulkin ƙasar, lamarin da ya sa kayar da shi a zaɓe ke da matuƙar wahala.
Da alama matakin da jiga-jigan ƴan siyasa irinsu Bello Bouba Maigari da Issa Tchiroma Bakary suka ɗauka na tsayawa takara ya ɗan rikita hazo, sai dai masu sharhi na ganin cewa ba za su zame wa Biya barazana sosai ba.
Dakta Pippie Hugues, mai sharhi kan manufofin gwamnati a cibiyar nazar ta Nkafu, ya ce alaƙarsu da wannan gwamnatin, ya rage musu karsashi a wurin ƴan ƙasar masu adawa da gwamnatin.
'' Ba ajiye aiki kawai ƴan Kamaru ke buƙata ba domin su yarda da su, suna buƙatar fiye da haka'' in ji shi. '' Dukkaninsu biyu sun daɗe cikin gwamnati kuma suna kallo ƴan ƙasar na wahala.''
Dakta Hagues ya kuma ce akwai yiwuwar ƴan siyasar biyu na arewacin ƙasar na cikin wani shirin siyasa da gwamnati ta tsara.
Sai dai wasu jam'ian jam'iyya mai mulki sun tabbatar da cewa an samu ɓaraka, inda suka ce a yanzu jam'iyyar CPDM za ta ji jiki wajen samun ƙuri'u daga arewaci ba kamar a baya ba.
Sai dai bayan cire Kamto, wanda shi ne babban ɗan adawa a zaɓen 2018, a yanzu Libii wanda ya zo na uku zai iya zama babban wanda zai kalubalanci Biya a wannan shekarar.
Duk da a baya kashi 6 kawai ya samu na ƙuri'u, yanayin siyasar Libii bayan nan na samun yabo.
Ya jagoranci jam'iyyarsa ga samun kujeru 5 a majalisa da kuma ƙananan hukumomi 7 a lokacin zaɓen ƴan majalisu a 2020. Tun bayan zama ɗan majalisa, ya kalubalanci gwamnati kan wasu muhimman manufofin, inda ya yi alwarin kawo sauyi da zarar ya hau kan karagar mulki.
Sai dai Dakta Hagues ya ce Akere Muna zai fi iya shawo kan alummar ƙasar saboda an fi fahimta da gamsuwa da manufofinsa.
''Muna na da ilimi da gogewa a harka da ƙasashen waje da kuma diflomasiyya, kuma abin da ƙasar ke so a yanzu kenan. in ji shi a yayin da ya ke yaba wa manufofin sannanen lauyan na dawo da ƙasar kan turba cikin shekara 5.
Shin ƴan adawa za su iya dunƙulewa?
A tarihin ƙasar, jam'iyyun adawa a rarrabe suke musamman lokacin zaɓe, abin da ya sa masana ke ganin hakan ya daɗe yana cutar da su.
Gabanin zaɓen shugaban ƙasa na wannan shekara, ana ta ce-ce-kuce kan buƙatar ƴan adawar su dunƙule su kuma haɗa dabarun su waje ɗaya domin tunkarar Biya.
Sai dai a yayin da kowane ɗan takasa ke fifita muradun kansa, babu tabbacin idan wasu daga cikinsu, ko kuma dukkansu, za su yi aiki tare duk da barazanar hakan na iya taimakawa shugaban ƙasar.
''Wannan zai iya zama ƙarshen siyasarsu, ko ƙarshen jam'iyyun su, idan ba su haɗe ba,'' a cewar shugaban wata kungiyar farar hula Felix Agbor Balla.
''Dole ne Kamto da sauran sun nemi wani ɗan adawa da zai iya wakiltarsu, kuma wajibi ne su sanya muradun ƙasar a gaba, su ajiye son kai a gefe su nemi wanda zai ja ragamar hamayya ya kayar da CPDM a ranar 12 ga watan Oktoba,'' in ji shi.
Dakta Hagues ya ce Kamto zai iya amfani da tasirinsa wajen neman goyon bayan haɗakar ƴan hamayya tunda a yanzu an cire shi daga takarar.
Ya jaddada cewa ba lallai sai shi Kamto ne zai kawo sauyi ba, amma za a iya samun sauyi ta hanyar sa.
Duk da dai Kamto bai ce komai ba game da hakan a ranar Alhamis, ya ce '' Ina tsaye tsayin daka a tare da ku. Fafutukar ba ta ƙare ba.''
Dakta Hagues ya ce za a iya samun haɗakar ƴan hamayya, inda ya buga misali da wani taron ƴan hamayya da aka yi ranar 2 ga watan Agusta a birnin Foumbam da ke Yammaci.
Prince Micheal Ekosso, shugaban Jam'iyyar USDP, wanda ya halarci taron, ya shaidawa BBC cewa manufar taron shi ne domin shirye shiryen janye wa ɗan takara ɗaya.
Duka da dai zuwa yanzu ba a zaɓi ɗan takarar ba, an shimfiɗa wasu sharuɗɗai na wanda zai cike gurbin.
Muna son mutumin da zai biya buƙatun ƴan Kamaru, wanda kuma zai iya aiki tare da kowa, kuma wanda ke jin harsuna da dama kuma zai iya haɗa kan sauran ƴan takara da manyan ƴan siyasa,'' in ji Ekosso.
A zaɓen shekarar 1992, jagoran hamayya John Fru Ndi ya sami goyon bayan Union for Change, wata haɗakar jam'iyyun siyasa da ta ƙungiyoyin farar hula.
Duk da dai ba shi kaɗai ne ɗan takara ba, masana na ganin haɗakar ta taimaka masa samun kashi 36 cikin ƙuri'un ƙasar, shi kuma Biya a lokacin ya lashe kashe 40.
Wannan ne kaɗai lokacin da wani ya kusa kayar da Biya. A lokacin Fred Ndi ma ya yi ikirarin shi ya lashe zaɓen, sai dai hukumomi sun yi wasti da zargin magudin zaɓe kuma suka tabbatar da Biya a matsayin wanda ya yi nasara.
Mutane da dama na ganin idan ƴan adawa ba su dunƙule ba kamar yadda aka yi a 1992, Biya zai sami sauƙin sake haye wa kan karagar mulki.
'' Ya na da gogewa ya na da ƙarfin yi sannan kuma tsarin da ake kai ya na yi da shi,'' in ji Dakta Hagues.