'Gara na zama manomi da na koma makaranta'

Yaro zaune a kan buhuna

Asalin hoton, Gift Ufuoma/BBC

    • Marubuci, Azeezat Olaoluwa
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Journalist Reporter, West Africa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Maryam mai shekara 14 na zaune a kofar gidansu bayan ta dawo daga makarantar allo, tana cike da burin sake komawa makarantar boko.

"Ina matukar baƙin ciki saboda rashin zuwa makarantar boko tsawon lokaci, amma ina fatan wata rana zan koma," in ji ta.

Maryam sanye da hijabi tana rike da littafi a gaban gidansu

Asalin hoton, Gift Ufuoma/BBC

An sace Maryan tare da wasu ɗalibai aƙalla 279 daga makarantarsu a garin Kuriga da ke jihar Kaduna, a arewa maso yammacin Najeriya, a watan Maris na 2024.

An riƙe su har na tsawon kwana 17, kafin daga bisani ɓarayin su sake su.

Tun daga wannan lokaci Maryam da abokan karatunta ba su sake komawa makarantar ba.

Najeriya ita ce take da yaran da ba sa zuwa makaranta fiye da kowace ƙasa a duniya, kuma matsalar rashin tsaro da yawan satar mutane domin karɓar kuɗin fansa da ke karuwa a ƙasar sun ƙara ta'azzara matsalar.

Wani magidanci Idris Alhassan

Asalin hoton, Gift Ufuoma/BBC

Bayanan hoto, An fara sace Idris Alhassan kafin daga baya a sace 'yarsa daga makaranta

A wani rahoto da asusun kula da yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF ya fitar, ya ce kimanin yara miliyan 18 da dubu 300 ne ba sa zuwa makaranta a Najeriya, wannan kuma shi ne adadi mafi yawa da aka taba samu a duniya.

Kuma yawancin yaran a arewacin ƙasar suke, inda talauci da rashin tsaro suka kasance daga cikin matsalolin da ke janyo wannan matsala.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Cristian Munduate, jami'in UNICEF ne a Najeriya, ya ce akwai buƙatar ƙara zage damtse domin magance wannan matsala ta karuwar yaran da ba su zuwa makaranta.

A wani rahoton da hukumar ta UNICEF ta fitar a shekarar da ta gabata ta ce a hukumance an kai irin wannan hari a makarantun boko don satar dalibai, har sau 19 a 2022 da 2023, lamarin da ya tilasta rufe makarantu 113 a jihohi uku na arewacin Najeriyar - Borno da Yobe da kuma Adamawa

satar daliban da aka yi masu yawa a Kuriga na daya daga cikin irinta mafi girma a Najeriya a sama da shekara goma - tun lokacin da aka sace dalibai mata na Chibok a 2014, lamarin da ya girgiza duniya.

Tawagar BBC ta ziyarci garin na Kuriga, inda ta samu damar shiga makarantar da aka sace daliban tare kuma da ganawa da wasu daga cikinsu.

Tafiyar tana da wahala da hadari, inda muka wuce wuraren bincike na jami'an tsaro akalla tara a tafiyar ta kusan sa'a biyu.

A hanyar babu sabis na waya hatta ma a garin na Kuriga, 'yansanda sun gaya mana cewa yankin na daya daga cikin mafiya hadari a jihar ta Kaduna.

Kauyuka da dama a hanyar sun zama tamkar kufai mazauna su sun gudu saboda yawan hare-hare da miyagu ke kai musu.

Mahaifin Maryam, Idris Alhassan, ya yanke shawarar kwashe iyalinsa ya bar garin na Kuriga, kuma ya yi alƙawarin cewa ba zai sake komawa garin ba.

"An sace ni daga garin tun ma kafin sace daliban makarantar. An rike ni tsawon kwana hudu amma Allah ya ba ni sa'a na tsere. Kwana kadan bayan na tsere 'yanbindigar suka sake dawowa garin suka sace ƴata da sauran wasu yara," in ji Alhassan a tattaunawarsa da BBC.

"Wannan shi ne dalilina na barin garin da iyalina, mu je inda za mu zauna lafiya. Mun bar Kuriga mako daya bayan harin makarantar - sai da aka sako su na dawo domin na dauki Maryam mu tafi. Ba na jin zan sake komawa garin."

Yanzu dai Maryam da iyayenta da 'yan'uwanta suna zaune ne a Rigasa - da ke wajen garin Kaduna, saboda matsalar tsaro da ke addabar jihar.

Ba su da wani gida na kansu ko gona , wanda wannan ya sa suke faɗi-tashin rayuwar yau da kullum.

Hakan na nufin Maryam da kannenta ba su ci gaba da zuwa makarantar boko ba.

"Rayuwa a Rigasa na da wahala sosai. Ba aiki, ba abinci, ba ilimi ga ƴaƴanmu, ballantana ma batun kula da lafiya.

Babu makaranta a kusa, kuma muna tsoron kai 'ya'yanmu nesa saboda har yanzu muna cikin fargaba," in ji mahaifin Maryam.

Azuzuwan makarantar Kuriga da aka gyara.

Asalin hoton, Gift Ufuoma/BBC

Bayanan hoto, A nan aka sace dalibai kusan 200 a watan Maris daga nan ne aka gyara makarantar

Yayin da manyan ƴaƴan ke tafiya - sana'ar baban-bola, masu ƙananan shekaru irin su Maryam suna zama a gida ne, sai makarantar allo ko Islamiyya suke zuwa.

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta sauya wa yara sama da 300 makaranta saboda matsalar ta tsaro.

"Lokacin da muka hau mulki a 2023, sama da makarantu 800 ko dai suna rufe ko kuma an yi watsi da su a jihar saboda matsalar tsaro, '' in ji gwamnan jihar kaduna a tattaunawarsa da BBC .

Ya ce, ''mun gaji kusan yara 736,000 da ba sa zuwa makaranta. Kuma zuwa yanzu mun mayar da kusan 300,000 makaranta."

Duk da yunkurin gwamnatin jihar har yanzu da dama daga cikin makarantun suna rufe, kuma da yawa daga cikin daliban suna tsoro su koma makarantar.

Wani yaro, Auwal Adamu, mai shekara 16 ya gaya wa BBC cewa, " Bana son komawa makaranta saboda ina jin tsoro har yanzu don ina tuna abin da ya faru da mu."

"Ina fargabar cewa 'yanbindigan za su iya sake komowa su sake sace mu. Ni kadai na san irin wahalar da na sha lokacin da aka sace mu, muke hannunsu. Na sha wuya sosai. Mun yi tafiya mai tsawon gaske ba hutu ba kuma abinci. Gara na zama manomi da na koma makaranta."

mahaifiyar Auwal, Hussaina Adamu, tagoyi bayan shawarar dan nata kuma ba za ta yarda ta yi kasada da rayuwar dan nata da yake shi kadai ba.

Ta ce : "Duk da cewa gwamnati ta sake bude makarantar, gara dana yana tare da ni a gida saboda ina jin tsoron cewa wadannan 'yanbindiga za su iya kara dawowa su sake sace yaran."

matashi Auwal Adamu zaune a kan buhuna

Asalin hoton, Gift Ufuoma/BBC

Bayanan hoto, Auwala Adamu na son fara sana'ar noma ba ya son sake komawa makaranta tun bayan da barayin suka sako shi

Wakiliyar asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, Cristian Munduate, na son ganin gwamnati ta kara dagewa domin mayar da yara irin su Maryam da Auwal, makaranta.

"Akwai bukatar hukumomi su bullo da dabaru daban-daban, wadanda za su iya sa iyaye su mayar da 'ya'yansu makaranta," in ji jami'ar.

Gwamna Sani ya ce babban abin da ya sanya a gaba shi ne ganin yaran da suka bar makaranta sun koma azuzuwansu".

Maryam da sauran yara da ke Rigasa, wadanda har yanzu suke da burin komawa makaranta suna cike da fatan ganin hukumoi tare da iyayensu za su lalubo hanyar da za su mayar da su makaranta nan ba da dadewa ba.

"Burina shi ne na zama lauya ko likita a nan gaba; shi ya sa nake son komawa makaranta domin cimma burina,'' in ji Maryam.