Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Klopp ya nace sai Livepool ta kawo masa Amrabat
Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya matsa lamba ga jami'an kungiyar, da su duba yiwuwar sawo masa dan wasan tsakiyar Fiorentina da Maroko Sofyan Amrabat.
Amrabat ya nuna kansa sosai a gasar kofin duniya da aka kammala ta Qatar 2022, inda ya taimaka wa tawagar ta Atlas Lions kafa tarihin kaiwa zagayen kusa da karshe.
Karo na farko kenan a tarihi da wata kasar Afrika ko ta Larabawa da ta taba kaiwa matakin na semi-fayinal.
Baya ga Liverpool, rahotanni sun ce kungiyoyin Tottenham da Barcelona da Sevilla na daga cikin masu zawarcin dan wasan.
Jiya aka bude kasuwar saye da sayar da yan wasa a Turai, kuma tuni wasu kungiyoyin sun fara kulla ciniki da juna.