Tottenham na son Rodrygo, Donnarumma na kwaɗayin United

Lokacin karatu: Minti 1

Tottenham na son saye ɗan wasan Real Madrid da Brazil, Rodrygo mai shekara 24, domin maye gurbin ɗan wasanta na Koriya ta Kudu, Son Heung-min mai shekara 33. (AS - in Spanish)

Manchester United ta bi sahun Newcastle a neman daidaitawa da ɗan wasan RB Leipzig da Slovenia, Benjamin Sesko mai shekara 22. (Sky Sports Germany)

Newcastle ta kuma kwaɗaitu da ɗan wasan Paris St-Germain da Portugal, Goncalo Ramos mai shekara 24, idan ta gaza wajen sayo Sesko. (Daily Mail)

Inter Milan na son sayo tsohon ɗan wasan Manchester United da Ingila, Mason Greenwood mai shekara 23 daga Marseille. (Corriere Dello Sport - in Italian)

Mai tsaron raga a Paris St-Germain da Italiya, Gianluigi Donnarumma mai shekara 26, na son tafiya Manchester United. (Teamtalk)

Ƙungiyar RB Leipzig ta Jamus ta yi tuntuba kan ɗan wasa Ingila, Tyrique George mai shekara 19, a lokacin tattaunawa da Chelsea kan ɗan wasanta na tsakiya, Xavi Simons mai shekara 22. (Fabrizio Romano)

Ƙungiyar Al-Hilal ta Saudiyya na harin ɗan wasan gaba a Liverpool da Uruguay, Darwin Nunez mai shekara 26. (Athletic - subscription required)

Ɗan wasan gefe a Manchester United da Brazil, Antony mai shekara 25, ba ya son tafiya Saudiyya, burinsa shi ne komawa Real Betis, inda ya je zaman aro a wancan kakar. (Sport - in Spanish)

Ɗan wasan Manchester United da Argentina Alejandro Garnacho, mai shekara 21, na son zuwa Chelsea inda yanzu yake dakon a shiga tattauna yarjejeniya. (Fabrizio Romano)