An samu kan mutane shida da aka daddatse a titi a Mexico

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomi a Mexico sun samu wasu kawunan mutane shida da aka daddatse aka ajiye su a kan wani titi da ke tsakanin wasu jihohi biyu wadanda ba a danganta su da kungiyoyin masu aikata miyagun laifuka.
Zuwa yanzu hukumomin ba su bayar da bayani kan abin da ya kai ga aikata wannan ta'asa ba ko kuma bayyana kungiyoyin bata-gari na kasar ta Mexico da ake ganin sun aikata wannan kisa ba.
An ga wadannan kanun mutane shida ne da aka daddatse aka ajiye su a kan titin da ya hada jihohi biyu masu zaman lafiya na Puebla da Tlaxcala – iadan aka kwatanta su da sauran jihohin kasar ta Mexico.
An gansu ne da sanyin safiyar ranar Talata.
Kafafen yada labarai na kasar sun ruwaito cewa an ajiye wani bargo a kusa da kawunan tare da rubutun wani sako na gargadi ga kungiyoyin 'yan daba da bata-gari da ba sa ga maciji da juna – kuma an nuna alamun cewa wata kungiya ce ta masu aikata miyagun laifi da ake kira La Barredora – sunan da ke nufin mai shara.
Wannan sunan shi ne na wata kungiyar bata-gari da ba a san ta ba sosai wadda ke cin karenta babu babbaka a jihar Guerrero ta yammacin kasar ta Mexico – sai dai ba a tabbatar ba ko 'yan kungiyar ne suka tafka wannan kisan gilla da kuma dalilin yin hakan.
Bayan safarar miyagun kwayoyi akwai kuma hada-hadar satar shigar da mai da kungiyoyin bata-gari ke yi a wannan yanki – lamarin da ke sama musu makudan biliyoyin dala a duk shekara.
Zuwa yanzu dai hukumomin tarayya ba su ce komai ba a kan wannan kisan da aka yi wa mutane aka daddatse kawunan nasu ba.
A watan Yuni ma an samu gawawwakin mutum 20 - hudu daga cikinsu an daddatse kawunansu a jihar Sinaloa, wadda ta yi kaurin suna da tashin hankalin kungiyoyin bata-gari.
Haka kuma an kashe wasu matasa 'yan kasar ta Mexico a wani harbe-harbe da aka yi a lokacin wani biki na Cocin Katolika a jihar Guanajuato da ke tsakiyar kasar a watan Mayu.
Tashin hankali tsakanin kungiyoyin bata-gari ya karu a shekarun nan inda aka kashe dubban mutane wasu dubban kuma suka bace tun bayan gwamnati ta fara amfani da sojojin kasar ta Mexico wajen yakar kungiyoyin 'yan daba a 2006.
An yi wannan ta'annati ne kuwa yayin da gwamnatin Shugaba Claudia Sheinbaum ke daukar matakai na ba-sani-ba-sabo a kan safarar miyagun kwayoyi.











