Yadda ake yi wa ƴan takara kisan gilla lokacin yaƙin neman zaɓe a Mexico

- Marubuci, Will Grant
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Mexico and Central America correspondent in Guerrero
Yayin yaƙin neman zaɓe mafi muni da aka taɓa yi a ƙasar Mexico, jihar Guerrero da ke yammacin ƙasar ta zama wuri mafi haɗari ga 'yan takara.
Mutane kaɗan ne suka fi Cinthia Juarez gane hakan.
Ɗaya daga cikin mutanen da aka fara kashewa yayin kamfe shi ne abokinta da suka taso tare, Moises "Moy" Juarez Abarca. Mista Abarca riƙaƙƙen mai kare haƙƙin 'yan luwaɗi ne wanda ya tsaya takarar shugaban ƙaramar hukuma kafin daga baya 'yan bindiga su yi garkuwa da shi.
Daga baya aka gano gawarsa a cikin wani wawakeken ƙabari tare da sauran mutum 16.
"Na shafe shekara sama da 20 a gwagwarmayar siyasa tare a abokina Moy. Wannan ne tashin hankali mafi muni da muka taɓa gani a Guerrero da Acapulco," in ji Cinthia, wadda ta maye gurbinsa a takarar.
Yayin da aka jingine maganar kisan abokin nata a gefe, Cinthia na sane da irin hatsarin da take fuskanta a takarar da take yi a madadinsa. Amma matar maras girman jiki kuma jajirtacciya wadda kuma jagora ce ta ƙungiyar kare haƙƙin 'yan luwaɗi a garinsu, ta ce barazana ba za ta hana ta motsi ba.
"Tabbas ina da fargaba. A tsorace nake da sanin cewa wata rana zan fita amma ba zan dawo ba, kuma saboda siyasa za a yi hakan. Sai dai a ɓangaren siyasa ne kawai za mu iya yin gwagwarmaya, hanya ɗaya da za mu dawo da Acapulco kan turba."
Yayin da zaɓe ke ƙaratowa, tashin hankalin ma na ƙaruwa. Aƙalla mutum 12 ne aka gano gawarsu a Acapulco ranar Talata, ciki har da gawa shida da aka binne a kusa da kasuwa, 'yan kwanaki kafin zaɓen na ranar 2 ga watan Yuni.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wani bincike na baya-bayan nan da wani kamfanin Mexico ya yi mai suna Integralia, ya bayyana munin lamarin. Kusan mutum 200 da suka haɗa da ma'aikatan gwamnati, da 'yan siyasa aka kashe ko aka yi wa barazana, inda aka samu sama da 50 a Guerrero kawai.
'Yan jam'iyyar Morena mai mulki ne lamarin ya fi shafa.
Da alama mafi girman mutum da akakashe a Acapulco shi ne kafin Kirsimeti, inda aka kashe Ricardo Taja, ɗaya daga cikin 'yan takarar magajin gari a jam'iyyar Moreno yana tsaka da cin abinci a wani gidan abinci.
Irin wannan tashin hankali da 'yan ƙwaya ke aikatawa ba sabon abu ba ne a Mexico.
Ganin yadda ake yin amfani da bakin bindiga wajen cire sunayen 'yan takara daga takardun jefa ƙuri'a, hakan zai tilasta wa masu zaɓe zaɓen wanda 'yan bindiga ke ƙauna ba wai wanda mutane ke so ba.
Cinthia Juarez ta nuna wa BBC yadda take yaƙin neman zaɓen tare da Evodio Velazquez, wani tsohon magajin gari wanda ya ce ya sha fama da barazana tsawon rayuwar siyasarsa.
Yayin da yake takarar zama ɗan majalisa, wasu 'yan bindiga sun dira a gidansa kuma suka tilasta masa lallai sai ya gana da su.
Tun daga nan ya haƙura da takarar.
"Gara na tsira da raina ba da takara ba," in ji shi. "Ba ni son shiga alƙaluman matattun 'yan siyasa."

Mista Velazquez ya ce irin wannan bala'in na lokacin zaɓe ya jefa "rashin tabbas a zukatan al'umma" wanda ya ɗora alhakinsa a kan "ƙarancin dokokin kare rayuwa".
Amma duk da haka ana ganin jam'iyya mai mulki ce za ta yi wuf da kujerun a ƙananan hukumomi da kuma jihar Guerrero.
Akwai yiwuwar masu zaɓe su sake bai wa ɗaya daga cikin masu jawo cecekuce a siyasar Mexico dama, wato Sanata Felix Salgado Macedonio.
A 2021 ɗan takarar ya jingine burinsa na neman kujerar gwamna saboda zargin fyaɗe da cin zarafin lalata. Ya musanta zargin kuma daga baya aka dakatar da tuhumar.
Shugaban Ƙasa Andres Manuel Lopez Obrador ne ke mara masa baya tun daga farkon zargin har zuwa ƙarshensa.
Ƙuri'un jin ra'ayin jama'a sun nuna cewa kusan kashi 60 na al'umma sun amince cewa babu zaman lafiya a garuruwansu. Sai dai Sanata Salgado Macedonio na cewa an samu cigaba duk da haka a kan shekarar da ta wuce.
Ya kuma musanta batun cewa salon shugaban ƙasar na yaƙi da matsalar tsaro mai taken “abrazos, no balazos” - wato "a rungumi masu laifi, ba kashe su ba - ya gaza.
"Dole ne a duba salon da kyau. Shugaban ƙasa na nufin muna son ganin 'yan'uwantaka a Mexico ba harsashin bindiga ba. Yana nufin akwai buƙatar mu duba tushen matsalar cikinsu har da maganar talauci da kuma raba mutane da iyalansu."

Da ma tuni jama'ar Acapulco suka sha fama a shekarar da ta wuce.
Wata takwas da suka wuce, Guguwar Otis ta ratsa birnin. Har yanzu ana iya ganin irin ɓarnar da guguwar ta yi a rukunin gidajen kusa da ruwa da kuma gidajen talakawa.
An rasa dukiya mai yawa da kuma rayuka.
Mercedez Sanchez ta yi asarar abubuwa da yawa. Ta yi ta kuka lokacin da take bayanin yadda zaizayewar ƙasa ta binne mahaifiyarta da ɗan'uwanta.

Mercedez ta ce ta gamsu da yadda gwamnati ta tunkari matsalar - inda aka raba kayan abinci, da bayar da kuɗi da suka kai dala 3,000 ga kowane gida, har ma da sauya wa mutane wasu daga cikin kayan amfanin gida.
Yayin da zaɓe ke ƙaratowa, Mercedez ta ce yawan aikata laifukan zai iya sauya mata ra'ayi. Rayuwa na cike da fargaba a inda take.
"Ba mu iya ko fita waje ba tare da fargaba ba. Ko da a ce ba ka tsokani kowa ba za ka iya shiga matsala ba tare da sani ba. Muna cikin haɗari a kodayaushe."











