Gwamnatin Mexico na karɓar bindiga ta bayar da kuɗi don rage laifuka

Bindiga

Asalin hoton, AFP

Lokacin karatu: Minti 2

Mexico ta kaddamar da wani shiri a fadin kasar inda take bayar da kudi ga mutanen da suka mallaki bindiga, wadanda suka amince su mika makaman, a wani kuduri na rage yawan kisan kai.

Shugaba Claudia Sheinbaum ta ce ta yi hakan ne domin tana son ta ga matasa sun yi watsi da tashin hankali a rayuwarsu.

Shugaba Sheinbaum ta zabi kaddamar da wannan shirin ne na rage bindigogi a hannun jama'a ta hanyar ba wa masu makaman da suka damka wa gwamnati kudade a babban cocin Katolika mai tarihi na babban birnin kasar Mexico City - domin kamar yadda shugabar ta ce majamiu za su taka muhimmiyar rawa a shirin na neman rage yawan kisan kai a kasar.

majamiu dai wurare ne da ke da kima da martaba a yankunan da suka yi kaurin suna wajen aikata miyagun laifuka da tashe-tashen hankali -kamar Guerrero, da Guanajuato, da kuma Chiapas.

Duk mutumin da ya mika bindigarsa za a ba shi sama da dala 12,000, kuma ba tare da an tambaye shi yadda ya mallaki bindigar ba.

Su kuwa yara da su ma aka nemi su mika bindigoginsu na wasa za a ba su kayayyakin wasa na ilimi.

Sai dai kuma masu suka na cewa wannan shiri da shugabar kasar ta bullo da shi ba zai hana manyan masu aikata miyagun laifuka ba samun makamai.

To amma gwamnati ta mayar musu da martani inda ta ce gwajin shirin da aka fara yi a babban birnin kasar, Mexico City, ya rage yawan aikata laifuka ko tashin hankali da ke da nasaba da bindiga sosai.