Afcon: Super Eagles ta doke Tanzania 2-1 a wasan farko

Afcon 2025

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 5

Tawagar Super Eagles ta Najeriya ta doke Tanzania da ci biyu da ɗaya a wasan farko na rukuni na 3 a gasar cin kofin nahiyar Afirka da ake bugawa a ƙasar Moroco.

Ɗan wasan bayan Najeriya, Semi Ajayi a minti 36 da fara wasa, dai ɗan wasan Tanzania ya farka a minti 50, sannan da ɗanwasan gaban tawagar, Lookman Ademola ya zura ƙwalla ta biyu a minti 52 da fara, inda aka ci gaba da fafatawa har aka tashi wasan.

A tarihi, ƙasashen biyu sun fara haduwa a AFCON a 1980 lokacin da Najeriya ta shirya wasannin, wadda ta fara karawar farko da doke Tanzania 3-1 a Legas ranar 8 ga watan Maris 1980. Kuma shi ne kofin farko da ta lashe.

Amma kuma jimilla sun fafata a tsakaninsu karo bakwai a dukkan haduwa, inda Najeriya ta yi nasara hudu da canjaras uku, sannan Najeriya ta ci kwallo 11, ita kuwa Tanzania ta zura mata uku kacal

Wasan bayan nan da suka haɗu shi ne a karawar neman shiga Afcon a 2017, sun fara da tashi 0-0 a Dar es Salaam ranar 5 ga watan Satumbar 2015.

Ita kuwa Najeriya ta yi nasarar cin 1–0 a birnin Uyo ranar 3 ga watan Satumbar 2016. Amma kuma Masar ce ta kai gasar kofin Afirka daga tsakanin tawagogin a lokacin.

Mai tsaron ragar Najeriya, Amas Obasogie yanzu haka yana sana'ar taka leda a Tanzani a ƙungiyar Singida Black Stars, inda yake wasa da takwarorinsa da suka hada da Hussein Masalinga da kuma Khalid Iddi.

Abin da ya kamata ku sani game da Najeriya a Afcon:

Super Eagles

Asalin hoton, Reuters

Wannan shi ne karo 21 da Super Eagles ke halartar babbar gasar tamaula ta Afirka

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sau uku Najeriya ta lashe kofin a (1980 da 1994 da kuma 2013).

Najeriya ta kare a mataki na biyu a Afcon sau biyar 1984 da 1988 da 1990 da 2000 da kuma 2023.

Haka kuma ta kare a mataki na uku sau 13 daga gasa 15 baya da ta halarta.

Sau biyu ana fitar da Najeriya a zagayen cikin rukuni (1963 da kuma 1982).

Najeriya ta kai zagayen daf da karshe sau 13 daga gasa 15 baya da ta je tun daga 1988.

Haka kuma duk gasar da aka gudanar a Kudancin Afirka, Najeriya kan kare cikin yan uku a gasa biyar daga shida da ta halarta.

Tarihin da Najeriya take da shi a wasan farko a cikin rukuni a Afcon - ta buga fafatawa 20 da cin 13 da canjaras biyu aka doke ta biyar daga ciki.

Ba a doke Super Eagles ba a wasan farko a cikin rukuni a gasa uku baya ba a Afcon.

Kuma wasa daya ta sha kashi daga 14 a karawar cikin rukuni, inda ta yi nasara 10 da canjaras uku.

Haka kuma ta ci kwallo a wasa shida kowanne a Afcon fafatawar cikin rukuni.

Wasa huɗu aka doke Najeriya a karawa 25 baya jimilla.

Wannan shi ne karo na 105 da Najeriya za ta buga a Afcon, ta uku kenan mai yawan buga wasanni a tarihin gasar.

Haka kuma ta ci kwallo 146 a Afcon, tana neman huɗu nan gaba su cika 150.

Super Eagles ta samu shiga gasar Afcon ta Morocco ba tare da an doke ta ba, kuma Ademola Lookman da Victor Osimhen ne kan gaba a ci mata kwallaye a wasan neman shiga Afcon, kowanne yana da biyu a raga.

Najeriya ta dauki koci, Eric Chelle cikin watan Janairu, wanda ya kai Mali zagayen kwata fainals a Afcon 2023 a Ivory Coast.

Mun mayar da hankali kan Afcon - Chelle

Eric Chelle

Asalin hoton, Getty Images

Ya kamata Najeriya ta mance da dukkan abin da ya faru a wasannin neman shiga gasar kofin duniya a mayar da hankali kan yadda za ta taka rawar gani a gasar cin kofin Afirka in ji kociya, Eric Chelle.

Mai horarwar ɗan kasar Mali ya bukaci ƴan wasa da su mance da takaicin kasa samun gurbin shiga gasar kofin duniya, bayan da Jamhuriyar Congo ta yi waje da su a wasan cike gurbi a cikin watan Nuwamba.

''Muna ta shiryawa kan yadda za mu mayar da hankalinmu waje daya. Na sanar da su cewar su fuskanci abin da ke gaban mu. Wannan shi ne abu mafi mahimmanci a tare da mu,'' kamar yadda Chelle ya sanar da manema labari.

''Muna bukatar mayar da hankali kan kalubalen da ke gabanmu, mu mance da duk surutai da ake yi. Hakika kasa samun tikitin zuwa gasar cin kofin duniya abin bakinciki ne''.

''Mun zo nan ne domin mu lashe dukkan wasannin mu. Za mu kara a gasar nan kenan muna da kyakkyawan fata. Bani da lokacin tuna abin da ya riga ya faru a baya. Na yi shirin fuskantar abin da ke gaba na, kuma abin da na mayar da hankali na kenan''.

Najeriya na fuskantar matsala a baya, sakamkon ƴan wasan da ke jinya ga kuma ƙyaftin William Troost-Ekong ya yi ritaya tun kan a fara Afcon.

Sai dai kuma kociyan Super Eagles, mai shekara 48 ya ce yana da kwarin gwiwa tare da fitattun yan wasan da yake da su a gasar da Morocco ke gudanarwa.

Najeriya, wadda ta buga wasan karshe a Afcon a 2023 a Ivory Coast, za kuma ta fuskanci Tunisia ranar 27 ga watan Disamba, sannan ta karkare da Uganda kwana uku a tsakani a karawar cikin rukuni a Morocco.

Abin da ya kamata ku sani game da Tanzania a Afcon:

Tanzania

Asalin hoton, Getty Images

Wannan shi ne karo na hudu da Tanzania za ta halarci Afcon a tarihi.

Ta fara halarta a 1980 da aka yi a Najeriya, ta kuma je gasar da aka yi a Masar a 2019 da kuma a 2023 da aka yi a Ivory Coast.

Wannan shi ne karo na biyu da take halartar Afcon karo biyu a jere a tarihinta.

Ta kuma buga wasa 10 a gasar cin kofin nahiyar Afirka ba tare da yin nasara ba, inda ta yi canjaras uku aka doke ta bakwai daga ciki.

Ta kuma yi rashin nasara a dukkan wasa uku na farko da ta buga a cikin rukuni.

Sai dai kuma ba a doke ta ba a karawa biyu da ta yi a 2023 da aka gudanar a Ivory Coast.

Wasan da ta tashi 0-0 da Jamhuriyar Congo a 2023, shi ne kadai da ta yi ba tare da ƙwallo ya shiga ragarta ba a Afcon.

Ƙwallo ɗaya kacal ta ci daga wasa hudu baya a babbar gasar tamaula ta Afirka.

Ta samu damar shiga gasar da Morocco ke shiryawa tare da Jamhuriyar Congo.

Ƴan wasanta, Simon Msuva da kuma Feisal Salum sune kan gaba a ci mata ƙwallaye a karawar neman zuwa Morocco, kowanne yana da biyu a raga.