Chelsea ta mayar da hankali kan Maignan, kocin Brighton ya gargadi Baleba

Watakila hankalin Chelsea ya sake karkata kan golan Faransa da AC Milan Mike Maignan mai shekara 30 a kasuwar cefanar da 'yan wasa ta badi sakamakon jan katin da aka bai wa golanta Robert Sanchez dan kasar Sfaniya mai shekara 27 a karawar da suka yi da Manchester United. Maignan zai iya rattaba hannu kan sabon kwantiragi a watan Janairu ya yin da kwantigarinsa na yanzu zai kare a bazarar badi kuma Chelsea ta so daukarsa alokacin bazara . (Daily Express), external
Kocin Brighton Fabian Hurzeler ya yi kira ga dan wasan tsakiya Carlos Baleba ya ci gaba da taka leda a kungiyar duk da cewa ana rade- radin cewa zai bar Brighton inda Manchester United ta nuna sha'awar daukar dan wasan kasar Kamaru mai shekara 21 a bazara (Daily Mirror), external
Everton na tunanin daukar dan wasan baya Sergio Reguilon mai shekara 28 wanda ba shi da kwantiragi da wata kungiya, duk da cewa tsohon dan wasan Tottenham Hotspur full- na son ya koma ya mahaifarsa. (Football Insider), external
Har yanzu Spurs na nazari kan dan wasan Sevilla, Ruben Vargas mai shekara 27, a matsayin dan wasa mai kai hari da take son dauka a watan Janairu badi. Kocin kungiyar Thomas Frank watakila ya maida hankali kan dan wasan tsakiya, sai dai dan wasan kasar Switzerland shi ne ya fi jan hankalin kungiyar. (Football Insider), external
West Ham United na nazari kan wanda za ta dauka a matsayin sabon kocinta ya yin da Graham Potter ke cigaba da fuskantar matsin lamba bayan da kungiyar ta sha kaye a hannun Crystal Palace a ranar Asabar. (Sky Sports), external
Liverpool da Manchester United da Chelsea na son daukar dan wasan Juventus da Brazil d Gleison Bremer mai shekara 28. (Teamtalk), external
Ana kyautata zaton Crystal Palace za ta yi watsi da duk wani tayin da za a yi wa dan wasan tsakiyar Ingila Adam Wharton mai shekara 21, a kasuwar sayar da 'yan wasa a watan Janairu inda Liverpool da Real Madrid duk suna sha'awarsa. (Football Insider), external
Dan wasan Bayern Munich da Faransa Dayot Upamecano, mai shekara 26, na son ya koma taka leda a Real Madrid idan kwantigarinsa ya kare a badi (Marca - in Spanish), external
Tottenham Hotspur na son ta maida dan wasan Bayern Munich dan kasar Portugal Joao Palhinha mai shekara 30 da aka bata aro ya koma dan wasan din -din. (TBR Football), external














