Barcelona na ci gaba da neman Haaland, Guehi ya fi son komawa Madrid

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan bayan Crystal Palace Marc Guehi, mai shekara 25, ya sanar da masu ba shi shawara cewa ya fi son komawa Real Madrid bayan komawar sa Liverpool a bazara. (Mirror)
Barcelona ta bayyana dan wasan gaban Manchester City Erling Haaland, mai shekara 25, a matsayin wanda zai maye gurbin Robert Lewandowski na tsawon lokaci. (Football Insider)
Zakarun Premier Liverpool na sa ido kan dan wasan Brighton Carlos Baleba. kANA dan wasan na Kamaru mai shekaru 21 yana jan hankalin Manchester United. (Teamtalk)
Tottenham Hotspur da Arsenal na daga cikin kungiyoyin Premier da dama da ke sa ido kan dan wasan tsakiya na Athletic Club da Spain Oihan Sancet, mai shekara 25. (Fichajes)
Manchester United a shirye take ta ba dan wasan tsakiya na Ingila Kobbie Mainoo, mai shekara 20, da kudi domin sayen Federico Valverde na Real Madrid. Sai dai Real din na ganin dan wasan tsakiyar na Uruguay, mai shekara 27, ba na sayarwa bane. (Goal)
Bayern Munich da Manchester United suna sha'awar sayen dan wasan tsakiyar Barcelona Frenkie de Jong, mai shekara 28, yayin da kwantiragin dan kasar Netherlands din zai kare a bazara mai zuwa. (Fichajes)
Fatan Marcus Rashford na komawa Barcelona ya gamu da cikas sakamakon karancin kudi. Dan wasan gaban na Manchester United da Ingila, mai shekara 27 da ke zaman aro a kulob din na Spain na iya fuskantar kalubale a kan duk wani fata na rike shi a matsayin dan wasan kungiyar na din din din. (Daily Mail)
Senne Lammens ya ki komawa Aston Villa a bazara domin ya koma Manchester United. An bayyana golan dan kasar Belgium mai shekaru 23 a matsayin wanda zai maye gurbin Emiliano Martinez idan ya bar kungiyar. (Birmingham Live)
Wakilin dan wasan tsakiyar Spurs Xavi Simons ya ce dan wasan dan kasar Holland mai shekara 22 bai yi nadama ba bayan rugujewar shirin komawarsa Chelsea a lokacin bazara. (Metro)











