Juventus na son Silva, Manchester City za ta nemi Kobbie Mainoo

Bernardo Silva

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bernardo Silva
Lokacin karatu: Minti 2

Juventus za ta yi kokarin daukar dan wasan tsakiyar Portugal Bernardo Silva, mai shekara 31 a kyauta idan kwangilarsa da Manchester City ta kare a bazara mai zuwa. (Tuttosport)

Ita ma Manchester City tana tunanin zawarcin dan wasan Manchester United Kobbie Mainoo, duk da cewa tana iya fuskantar gogayya daga Newcastle da kuma Chelsea kan dan wasan tsakiyar na Ingila mai shekara 20. (Teamtalk)

Chelsea ta ci gaba da zawarcin Morgan Rogers duk da cewa Aston Villa ta sanya farashin fam miliyan 80 kan dan wasan gaban na Ingila mai shekara 23. (Sun)

Karin kudin shiga da Manchester United ta samu a baya-bayan nan ya ba ta damar siyan dan wasan tsakiya na Brighton da Kamaru Carlos Baleba, mai shekara 21. (Mirror)

Liverpool ta shirya bayar da Yuro miliyan 50 (£43.35m) kan dan wasan bayan Barcelona Ronald Araujo, mai shekara 26, duk da cewa Tottenham ma tana sha'awar dan wasan na Uruguay. (Fichajes)

Chelsea ce kungiya ta baya bayan nan da ta nuna sha'awar siyan dan wasan bayan Ingila Marc Guehi mai shekara 25 a lokacin da kwangilarsa da Crystal Palace za ta kare a bazara mai zuwa. (Football Insider)