Benfica ta ɗauki Mourhinho - ƙungiya ta nawa zai horar?

Asalin hoton, Getty Images
Benfica ta naɗa Jose Mourinho a matakin sabon kociyanta kan yarjejeniyar zuwa karshen kakar 2027.
Mourinho, mai shekara 62 ya maye gurbin Bruno Lage, wanda aka kora bayan da ya yi rashin nasara a Champions League a gida a hannun Qarabag ranar Talata.
Tsohon kociyan Chelsea ya sake komawa horar da tamaula kasa da wata ɗaya, bayan da ya raba gari da Fenerbahce, bayan da Benfica ta hana ƙungiyar ta Turkiya zuwa gasar zakarun Turai ta Champions League da aka fara.
Mourinho ya fara horar da tamaula a Benfica a shekara ta 2000, amma wasa 10 ya ja ragama, sai ya bar ƙungiyar bayan rashin jituwa tsakaninsa da shugaban ƙungiyar.
"Alkawarin a bayyane yake - zan sake horar da Benfica, don cimma burina," in ji Mourinho.
"Ba ni ne mafi muhimmanci ba - Benfica ce mafi mahimmanci."
A yarjejeniyar da suka ƙulla, Mourinho da ƙungiyar za su zauna don cimma matsaya ko zai ci gaba da jan ragamar ƙungiyar zuwa kakar gaba kwana 10 da zarar an kammala wasannin 2025/26.
An kori Lage daga Benfica duk da wasa ɗaya ya yi rashin nasara a dukkan karawa a kakar nan, kuma Mourinho ya gaji ƙungiyar da take ta shida a teburin Primeira Liga da tazarar maki biyar tsakani da Porto mai jan ragama.
Zai fara da karawa ranar Asabar, inda za su ziyarci AVS, wadda take ta 17 a kasan teburin a babbar gasar tamaula ta kasar.
Ɗan kasar Portugal wanda ya bai wa kansa sunan ''the special one' a 2004 zai ziyarci Chelsea a Champions League da Benfica za ta buga ranar 30 ga watan Satumba.
Kungiyoyin da Jose Mourinho ya horas
Ƙungiya Manyan kofunan da ya lashe
Porto (2002-04) Primeira Liga biyu, Champions League, Uefa Cup da Portuguese Cup
Chelsea (2004-07 da 2013-15) Premier League uku, FA Cup da League Cup uku
Inter Milan (2008-10) Serie A biyu, Champions League da Coppa Italia
Real Madrid (2010-13) La Liga, Copa del Rey
Manchester United (2016-18) Europa League da League Cup
Tottenham (2019-21) Bai ɗauki kofi ba
Roma (2021-24) Conference League
Fenerbahce (2024-25) Bai ɗauki kofi ba

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Mourinho ya yi suna a Porto tsakanin 2002 zuwa 2004, bayan lashe kofi shida har da Champions League da ya ɗauka a 2003/04.
Tun bayan da ya bar kasarsa ta haihuwa a 2004, Mourinho ya horar da Chelsea karo biyu da Inter Milan da Real Madrid da Manchester United da Tottenham Hotspur da Roma da kuma Fenerbahce.
Mourinho ya ce "babu daya daga cikin manyan kungiyoyin" da ya yi aiki tun da ya bar Benfica da ya ji a matsayin "girmama, alhaki ko kwazo".
Bayan da aka kori Lage ranar Talata, shugaban ƙungiyar, Rui Costa ya ce sabon kociyan da zai ɗauka sai mai tarihin lashe kofuna.
Kenan Mourinho ne ya dace, bayan da ya lashe kofi 21 na baya-bayan nan shi ne Conference League a Roma a 2022.
Da kuma Champions League biyu da lik takwas a kasashe huɗu, amma dai kofi na karshe da ya ɗauka shi ne Europa League.
Benfica za kuma ta je Newcastle United, sannan kuma za ta karɓi bakuncin tsohuwar ƙungiyar da Mourinho ya horar Real Madrid a dai Champions League.
Benfica ta kare a mataki na biyu a teburin babbar gasar tamaula ta Portugal a bara, kuma rabonta da kofin tun 2022/23.
Mourinho ya fuskanci takaddama a Turkiya, musammam yadda ya yi ta caccakar alkalan wasa na kasar, lamarin da ya kai ya samu rashin jituwa da su.
A watan Nuwamba, Mourinho ya zargi Fenerbahce da ƙin gaya masa gaskiya kan gogewar alkalan tamaular kasar, amma ya ce Atilla Karaoglan shi ne wanda ya fi gwanninta lokacin da ya yi rafli da suka doke Trabzonspor.
Ya shigar da Galatasaray kara a watan Fabrairu, bayan da suka zarge shi da yin kalaman wariyar launin fata.
'Ina jin an ci amana' a Istanbul - bincike
Burak Abatay
BBC Turkish
Lokacin da aka naɗa Mourinho kociyan Fenerbahce a Yunin 2024, miliyoyin magoya bayan tamaula sun yi kyakkyawan fata. An ɗauki ɗaya daga cikin fitattun koci a duniya wanda zai kawo karshen ƙanfar lashe kofi a shekaru da yawa da cewar ƙungiyar za ta taka rawar gani a gasar zakarun Turai.
Sai dai nan take mafarkin ya kasa zama gaske.
Fiye da shekara ɗaya, wannan mafarkin sai ya koma takaici. Mourinho ya kasa yin nasara a wasan hamayya na Istanbul derby kuma ya kasa ɗaukar kofin babbar gasar tamaula ta kasar.
Yanzu dai ya koma ƙungiyar da ta fitar da Fenerbahce a wasannin cike gurbin shiga gasar Champions League ta bana.
Wasu magoya bayan Fenerbahce na jin an yaudare su. Ba kawai Mourinho ya yadda su ba, ya kuma ɗauke su shashashai.
Gokay cikakken magoyin bayan Fenerbace na har abada ya sanar da BBC cewar ''Tun daga ranar farko Mourinho na sha'awar komai, amma banda ƙwallon kafa.
''Ya kaskantar da gasar tamaula ta Turkiya da horar da Fenerbahce a salo mafi muni a tarihi,''











