Chelsea ka iya fuskantar tuhuma kan Sterling da Disasi

Raheem Sterling (a hagu) da Axel Disasi (a dama)

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto, A kakar da ta wuce Raheem Sterling (a hagu) ya tafi aro Arsenal kamar yadda Axel Disasi (a dama) ya je Aston Villa, aro
Lokacin karatu: Minti 1

Kungiyar kwararrun 'yan wasa ta Ingila (PFA) na tattaunawa da Chelsea, kan yadda Chelsea din ta yi wa Raheem Sterling da Axel Disasi, na ware su daga cikin tawagarta.

A yanzu 'yanwasan biyu ba sa atisaye da tawagar ta Stamford Bridge bayan da kociyan kungiyar Enzo Maresca ya fito fili ya gaya musu cewa ba sa cikin tsarinsa.

Sterling, mai shekara 30, yana da kasa da shekara biyu da ta rage a kwantiraginsa da Chelsea - a kan albashin kusan fan 325,000-a mako, yayin da kwantiragin dan baya Disasi mai shekara 27 zai kare a 2029.

Kasancewar dukkanin 'yan wasan biyu sun tafi zaman aro a wasu kungiyoyin a kakar da ta gabata, an sa ran za su bar Chelsea a lokacin kasuwar 'yanwasa ta bazara.

To amma kuma dukkanninsu suka ci gaba da zama a kungiyar ta Premier, kuma abu ne mawuyaci wani daga cikinsu ya samu shiga tawagar farko da kungiyar kafin watan Janairu lokacin da za a sake bude kasuwar saye da sayar da 'yanwasa.

Kungiyar ta kwararrun 'yanwasa na son ganin ta tabbatar da Chelsea ta bai wa Sterling da Disasi damar atisaye da tawagarta ta farko - manyan 'yanwasanta duk da cewa ba za ta sa su a wasa ba saboda kar kwazonsu ya ja baya.

Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa tana da tsauraran dokoki a kan ware 'yanwasa daga cikin tawagar kungiya - wanda hakan zai iya kaiwa ga tuhumar kungiya da cin mutuncin danwasa, abin da zai iya sa danwasa ya soke kwantiraginsa a kan wannan dalili tare da samun hakkokinsa.