Shin kun san alaƙar da ke tsakanin furfura da kuma kansa?

Asalin hoton, Patrik Giardino via Getty Images
- Marubuci, Justin Stebbing
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, The Conversation*
- Lokacin karatu: Minti 3
Akasari ana ɗaukar furfura a matsayin alamu na fara tsufa. Yana tuna mana shekarun da suka wuce da kuma yadda jiki ya sauya a tsawon lokaci.
Sai dai bincike a baya-bayan ya kalubalanci wannan iƙirari, inda ya ce akwai yiwuwar wannan furfura sauyawar jiki ne mai tsarkakiya da kuma watakila ke alaƙa da kansa.
Wani sabon bincike da aka gudanar kan ɓeraye ya bayyana irin yadda jiki ke iya daƙile lahani da za a samu, wani lamari mai muhimmanci ga tsufa da kuma kansa.
Idan mutum ya fara tsufa, ƙarfin ƙwayoyin jikinsa na raguwa da kuma zai iya jawo lahani. A ɓangaren kansa kuwa, matsala a ƙwayoyin jiki kan janyo rashin girma.
Wannan bincike ya bayyana irin alaƙar da ke tsakanin zubar gashi da ƙwayoyin jiki, wanda zai iya janyo rashin girman ƙwayoyin kansa masu haɗari.
Ƙwayoyin jiki na melanocytic su ne ginshikin wannan bincike. Waɗannan ƙwayoyi suna zaune ne a gefen wajen da gashi ke tsira.
A lokacin yanayi mai kyau, waɗannan ƙwayoyi na sake samar da wasu ƙwayoyi wanda ke sa gashi ya girma. Wannan kuma yana saka gashin kai ya samu launi a tsawon rayuwa.
Sai dai, a kowace rana ƙwayoyin jiki na samun lahani ga ƙwayoyin halittar haihuwa daga sassa da dama. Wannan lamari yana sanya jiki ya iya shiga haɗari na samun sinadarai marasa kyau. Abin da zai ƙara janyo tsufa da kuma barazanar kamuwa da kansa, kamar melanoma wanda ya kasance wani nau'i ne na kansar fata.
Har ila yau, wannan bincike ya ƙara yin haske kan abin da zai faru idan ƙwayoyin melanocyte da ke tsakiyar gashi suka samu matsalar ƙwayoyin halitta, ciki har da shiga wani yanayi mara kyau.
Alaƙar furfura da kansa
Ba dukkan matsala ta ƙwayoyin halitta ne ke janyo wannan matsala ba. A gwaje-gwajensu, masu binciken sun sanya ɓerayen da suka yi gwaji da su cikin barazana domin ganin yadda zai kasance.
A nan, alamomi da ke kusa sun ingiza ƙwayoyin da suka samu matsala su sake sabunta kansu da kuma rarrabuwa, duk da matsalar ƙwayar DNA.
Wannan bincike ya bayyana cewa makomar ƙwayoyin jiki na melanocyte yana dogara ne kan irin matsalar da aka samu.
Sai dai karkashin tasirin ƙwayoyin kansa, waɗannan ƙwayoyi da suka samu matsala suna cigaba da kasancewa, inda suke ba da dama ga wasu ƙwayoyi su fita.

Asalin hoton, Kimberrywood via Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Yana da muhimmanci a nanata cewa wannan bincike ya nuna cewa babu wata alaƙa mai ƙarfi tsakanin furfura da kuma ƙwayoyin kansa, sai dai a matsayin abubuwa biyu na wanda ya doshi hanyar tsufa da zimmar daidaito tsakanin sake samar da ƙwayoyin jiki da kuma kaucewa kamuwa da kansa.
Tsufa dai ba abu ne da ke hana kansa ba, illa wani ɓangare da ke kare ƙwayoyin jiki daga barazana.
Sai dai sakamakon wannan bincike yana da iyaka. Saboda an tattara yawancin alkaluman kan ɓeraye. Wannan na nufin cewa akwai buƙatar yin ƙarin bincike a jikin ƴan adam domin gano cewa ko ƙwayoyin melanocyte na aiki irin yadda aka gani.
Bambancin salon rayuwa tsakanin na'ukan dabbobi har ma da ɗan'adam, na nufin akwai tsarkakiya wajen gano alaƙar da ke tsakanin gashi da kuma barazanar kamuwa da kansa.
Labarin furfura dai bai kasance kaɗai kan wucewar lokaci ba ko nasarar da aka samu a tsawon rayuwa. Yana alaƙa da abubuwan da suka faru tun tsawon shekaru da suka shuɗe - daga zamani zuwa zamani.
Wannan gashi zai iya nufin wani abu: cewa, a lokacin gwagwarmaya tsakanin tsufa da kansa, abu ne mai kyau wani lokaci a sadaukar da wani ƙwayar jiki domin tagomashin ɗaukacin jiki.











