'Ko a jikinmu': Yadda China ke shirin nuna ƙwanji da Amurka
- Marubuci, Laura Bicker
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, China correspondent
- Aiko rahoto daga, Yiwu
- Lokacin karatu: Minti 6
"Ba mu damu da sayar da kayayyaki ga Amurka ba," in ji Hu Tianqiang a daidai lokacin da wani jirginsa na roba ke shawagi a saman kanmu.
Kantin Hu, mai suna Zhongxiang Toys, yana cikin babban kantin bayar da sarin kayayyaki a birnin Yiwu na ƙasar China.
A kasuwar akwai shaguna sama 75,000, kuma za a iya cewa akwai duk wani abu da ƴankasuwa suke buƙata. Za ka iya wuni ɗaya ba ka karaɗe ɓangare ɗaya na kasuwar ba.
Birnin Yiwu na lardin Zhejiang a gabashin China, yanki ne na masana'antu, wanda akwai aƙalla filayen jirin ruwa guda 30, kuma yankin ke ɗaukar kusan kashi 17 na kasuwancin kayayyakin da China ta fitar zuwa Amurka a bara.
Wannan ne ya sa yankin Yiwu ya zama kan gaba a game da batun takun-saƙar kasuwanci da ke tsakanin Amurka da China.
Shi ma Mr Hu, yana cikin ƴankasuwa masu sayar da kayan wasa na roba kamar motoci da dabbobi, waɗanda kasuwancinsu yake kai na dala biliyan 34 (fam biliyan 25).
Kusan dala biliyan 10 na wannan adadin yana komawa ne ga Amurka. Amma yanzu kayayyakin China na fuskantar harajin kashi 245. Sannan Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yana zargin China da yin kaka-gida a harkokin kasuwancin duniya.
Amma abubuwa sun fara sauyawa tun bayan da aka fara takun-saƙar kasuwanci tsakanin Amurka da China wanda aka fara tun a 2018. Hakan ya sa ƴankasuwa na yankin Yiwu sun koya darasi, kamar yadda Mr Hu ya taƙaice: Wasu ƙasashen ma suna da arziki."
Wannan yarda da kan ne abin da ke zama ruwan dare yanzu a ƙasar wadda ita ce ta biyu wajen ƙarfin tattalin arziki a duniya.
China ta daɗe tana nanata cewa Amurka na tilasta wa ƙasashe shiga yarjejeniyar kasuwanci, kuma ta ƙi janyewa daga takun-saƙar.
Yanzu kamfanoni da ƴankasuwa a ƙasar suna cewa suna da wasu ƙasashen da za su kai kayayyakinsu ba lalai sai Amurka ba. Mr Hu ya ce a baya kusan kashi 20 zuwa 30 na kwastomominsa ƴan Amurka ne, amma yanzu ya canja kwastomomi.

Asalin hoton, BBC/ Xiqing Wang

Asalin hoton, BBC/ Xiqing Wang
"Ba mu damu da kashi 20 zuwa 30 ɗin ba," in ji Hu. "Yanzu mun fi sayar da kayayyakinmu a kudancin Amurka da Gabas ta Tsakiya. Ba kuɗi ƙasarmu take nema ba, muma muna da arziki."
Da muka yi tambaya kan Trump, sai abokin kasuwancinsa, Chen Lang ya tsoma baki: "wasa kawai yake yi da mutane. Kullum cikin wasa yake. A wajensa lafta haraji kamar wasan ba da dariya ne."
Lin Xiupeng ya ce ya lura da ragowar kwastomomi daga Amurka a cikin shekara 10 da suka gabata da ya yi yana kasuwancin kayan wasa na roba.
"A kwanakin baya shagon da ke gabanmu ya samu wani dila daga Amurka da yake son kayan sama da yuan miliyan ɗaya. Amma saboda harajin nan, mai shagon sai ya fasa."
"Suma za su buƙaci harka da China," in ji shi, inda ya ƙara da cewa ƙasar ce kan gaba wajen shigar da kayan wasan yara zuwa Amurka.
"Na san dole akwai wasu ƴan kasuwa da dama Amurka da ba sa jin daɗin wannan abun da ke faruwa."

Asalin hoton, BBC/ Xiqing Wang
Kuma Mr Lin ya yi gaskiya. Wasu masu kasuwancin kayan wasa a Amurka sun rubuta ƙorafi zuwa ga fadar gwamnati, inda suka bayyana harajin da "babban cikas" ga kasuwancinsu.
"Harajin yana shafar harkokin ƙananan kasuwanci a Amurka," in ji Jonathan Cathey wanda yake da kamfanin kayan wasan yara a Los Angeles a zantawarsa da BBC ta wayar tarho.
Ya zuba jarin arzikinsa baki ɗaya na dala 500 a kamfaninsa mai suna Loyal Subjects a shekarar 2009 wanda ya fara daga wani gida na zamani mai ɗaki biyu a yankin West Hollywood. Ya ce yanzu kamfani ya gawurta zuwa darajar miliyoyin daloli, amma ya ce harajin zai iya jawo masa tsaiko.
"Harajin nan zai iya durƙusar da kasuwancin kayan wasa baki ɗaya," in ji shi.
Yaƙin siyasa na Trump
China na cikin manyan abubuwan da Trump ya fi mayar da hankali a kwana 100 da ya yi a ofis.
"Alamu sun nuna yana yaƙin siyasa ne da duniya baki ɗaya," in ji wani tsohon kalan na soji mai ritaya, Zhou Bo, wanda ya yi aiki da rundunar sojin People Liberation Army. "Amma lallai yana da burin yi wa China cin kashi."
Trump ya zargi China da gudanar da hulɗa a yankin Panama, amma ya sha alwashin ƙwacewa. Ya daɗe yana ƙoƙarin neman hanyoyin da zai girbi ma'adinan da ke yankin, waɗanda China ta riga ta yi kaka-gida, amma sai ya sa batun a cikin yarjejeniyar Amurka da Ukraine. Haka kuma yunƙurinsa na ƙwace Greenlad bai rasa nasaba da yunƙurinsa na rage ƙarfin China a yankin Arctic.

Asalin hoton, BBC/ Xiqing Wang
A makon jiya, ya ce za a rage harajin da aka lafta wa China zuwa rabi, sannan ya yi magana kan samar da "yarjejeniya mai kyau da China," da ye ce gwamnatinsa na ƙoƙarin tsarawa.
"Mu a China muna da karin magana da ke cewa - dole mu bar alburushi ya ɗan fita," in ji Kanal Zhou mai ritaya. "Hakan na nufin a yanayi na yaƙi, babu wanda ya san abin da zai faru. Ina tunanin wannan takun-saƙar za ta iya ɗaukar wata ɗaya ko biyu - amma ba na fata ta wuce wata uku."
Ba zai yiwu matsalar nan ta daɗe ba, in ji shi, domin a cewarsa hakan ba zai haifar da ɗa mai ido ba.
Goldman Sachs ya yi hasashen cewa tattalin arzikin China zai ƙaru da kashi 4.5 a bana, wanda ya yi ƙasa da abin da ƙasar ta yi hasashe na ƙashi 5.

Asalin hoton, BBC/ Xiqing Wang
Da BBC ta bincika ko an koma fitar da kaya daga China zuwa Amurka, babu wani bayani gamsasshe da ake samu. Wani ɗankasuwa ya ce yana da kayan sakawa na kusan rabin dala miliyan ɗaya da zai kai Walmart. Sannan wasu ƴan kasuwa da muka zanta da su sun ce wasu yan Amurka sun fara sayen kayayyaki.
Dambarwar da ke tsakanin ƙasashen biyu masu girman tattalin arziki ya shafi harkokin kasuwanci da dama.
Amma kowane irin kasuwanci ne, babu shakka suma ƴan Amurka za su ji raɗaɗi ko dai na rashin ko dai ƙarancinsa ko kuma tsada na kayan na ƙasar China.
Damarmaki a wasu ƙasashen daban
Har yanzu Amurka na ta'allaƙa da China wajen sana'anta wasu abubuwan da ake buƙata a cikin ƙasar - irin su wayoyin salula da kwamfutoci da kayan sakawa da kayan wasa da sauransu.
Kimanin kashi 90 na kayan kwalliyar kirsimeti da ake amfani da su a Amurka daga Yiwu na China suke zuwa, inda masu shagunan suka shaida mana cewa yanzu sun fara mayar da hankalinsu zuwa yankin Amurka ta Kudu.
Kuma da ka shiga kasuwar za ka ga alama domin da sanyin safiya da ka shiga kasuwar ka ji amon kalmar "Shukran," inda wani Balarabe yake koyar da yara yadda za su ce "na gode. Da kuma kalmar "Afwan" a matsayin martani.

Asalin hoton, BBC/ Xiqing Wang
Ana koyar da harsunan ne kyauta. Yawancin ɗaliban mata ne da suke shiga mai kyau domin jan hankalin kwastomominsu.
"Waɗannan matan su ne ƙashin bayan kasuwanci a China," in ji wani mai shago wanda asali ɗan ƙasar Iran ne.
"Suna gasar koyon harsuna domin su wuce sa'anninsu."
Yanzu haka yawancin ƴan kasuwar suna iya magana da Ingilishi. Sun ce burinsu su fara iya magana da kwastomominsu da harshen Spain da Larabci - wanda shi ma alama ce da ke nuna yunƙurin ƙasar na sauya alakar kasuwacinsu.
Oscar wani ɗan ƙasar Columbia ne da muka tsinta a kasuwar wanda ya ce takun-saƙar kasuwancin da ke tsakanin China da Amurka ya buɗe ƙofar damarmaki ga wasu ƙasashen.












