Amaryar da aka yi wa dirar mikiya ana tsaka da shagalin bikinta

'Yan sandan Uganda sun gurfanar da wasu jami'anta guda hudu bayan dirar mikiya wajen wani bikin aure a karshen mako tare da kama amarya.

An kama amaryar ne bisa zargin sata da kuma nuna rashin da'a ga jami'an nasu.

Mai magana da yawun 'yan sandan kasar, Fred Enanga, ya ce idan aka samu jami'an da laifi a wajen bincike, za a iya rasa aikinsu.

Bayan kama amaryar, sun tafi da ita zuwa wani ofishin 'yan sanda a Mbarara da ke yammacin Uganda, inda suka tsare ta har zuwa washegari.

Sun sake ta a ranar Lahadi. 'Yan sanda sun ce kamen ''bai kamata ba kuma rashin adalci ne''.

A cikin wata sanarwa da mista Enanga ya fitar, ya ce "Ranar farin-ciki a rayuwarta ta koma ta bakin ciki.''

Ana tsare da wani jami'in ɗan sanda da ke da hannu a kamen yayin da sauran guda uku kuma suka buya, a cewar Enanga.

Zargin sata da aka yi wa amaryar ya biyo bayan korafe-korafe daga tsohon wurin aikinta na banki.

An bai wa ɓangarorin sulhunta kansu cikin watan ɗaya, a cewar mai magana da yawun 'yan sandan.

Sashin kwararru na 'yan sandan, na bincike kan yiwuwar haɗa-kai tsakanin jami'an 'yan sandan hudu da kuma mai korafin.

'Ranar farin-ciki ta koma ta bakin ciki'

Sanarwar da rundunar 'yan sandan Uganda ta fitar, na cewa duk da cewa hakkin jami'in ɗan sanda ne na kame tare da gabatar da wanda ake zargi a kotu, amma abin da jami'an suka yi bai dace ba.

Hakan ne ya sa kwamandan 'yan sanda na yankin, Rwizi, ya bayar da umurnin cewa a saki amaryar ba tare da ɓa ta lokaci ba.

Rwizi ya kuma bai wa amaryar da angonta da surukai da abokanai da sauran mahalarta da kuma cocin da aka yi bikin hakuri.

Jami'an 'yan sanda sun kuma bayyana cewa hujjojin da suka tattara, sun nuna cewa a ranar 6 ga watan Yulin 2022, wani mai suna Mirembe Henry, tsohon shugaba a tsohon wurin aikin amaryar mai suna Christine Natuhwere, da ta yi aiki a bankin, ya kai ƙararta kan zargin satar shilling miliyan 8.

Su na bincike kan lamarin, inda suka aike da batun karar zuwa ga babban alkali na jihar, wanda ya ba su shawarar yin sulhu tsakaninsu.

Sai dai wanda ya shigar da karar, ya bukaci a sake duba batun da hukunta wacce ake zargi da yin satar da kuma sake mayar da karar gaban 'yan sanda.

Sanarwar ta ci gaba da cewa a ranar 20 ga watan Augustan 2022, jami'an 'yan sandan sun hada-kai da mai korafin don zuwa tayar da husuma a lokacin bikin auren.

Sun yi dirar mikiya a wajen da ake gudanar da bikin da misalin karfe takwas na dare tare da kama amarya.

Bayan nan, sun saka ta cikin motar wanda ya shigar da karar da kuma tuka motar zuwa ofishin 'yan sanda, inda suka tsare ta a can.

'Yan sanda sun kwatanta kamen da aka yi a gaban angon da 'yan uwa da abokanai a matsayin abin kunya da kuma bai dace a yi ba.