'Yan sandan Netherlands sun kama 'yan wasan Legia Warsaw

Asalin hoton, Getty images
Firaministan Poland Mateusz Morawiecki, ya ba da umarnin ɗaukar matakin diflomasiyya cikin gaggawa bayan da aka kama 'yan wasan Legia Warsaw biyu bayan rashin nasarar da suka yi a gasar cin kofin Europa a AZ Alkmaar ranar Alhamis.
‘Yan sandan ƙasar Holland ne suka ɗauke Radovan Pankov da Josue Pesqueira daga motar bas ɗin tawagar bayan sun yi arangama da jami’an tsaro kuma a halin yanzu suna tsare a ƙasar ta Netherlands.
Shugaban ƙungiyar Legia Dariusz Mioduski ya ce ya sha bugu a lokacin da yake ƙoƙarin shiga tsakani, inda rahotanni suka ce ‘yan sanda sun ki barin motar bas ɗin ta bar filin wasan har sai an tsare ɗan wasan Portugal Josue da ɗan wasan bayan Serbia Pankov.
'Yan sandan ƙasar Holland sun tabbatar da kama wani mutum ɗan ƙasar Serbia mai shekaru 28 da kuma ɗan ƙasar Portugal mai shekaru 33 bayan an kammala wasan bisa zargin aikata ba daidai ba.
Ƙungiyar ta Poland ta bayyana abubuwan da suka faru bayan wasan a matsayin abin kunya, kuma Mioduski zai yi taron manema labarai a filin wasa na Ƙungiyar.
Tun da farko dai an tura ‘yan sandan kwantar da tarzoma kafin a fara wasan a lokacin da gungun magoya bayan kungiyar Legia suka kutsa cikin wata kofar shiga filin wasan.







