Me ya sa Shugaba Tinubu ke son yin garambawul a gwamnatinsa?

..

Asalin hoton, state house/facebook

Lokacin karatu: Minti 4

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana cewa zai yi wa majalisar ministocinsa kwaskwarima nan gaba kaɗan, kamar yadda mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya sanar.

"Shugaban ƙasa ya ce zai yi wa majalisarsa kwaskwarima. Ban sani ba ko zai yi hakan kafin 1 ga watan Oktoba amma dai tabbas zai yi.... bai dai faɗa mana lokaci ba, amma tabbas zai yi" in ji Onanuga.

Mista Onanuga ya ce shugaban ya kuma umarci ministoci "da su daina jin kunyar yin magana da kafofin yaɗa labarai" domin tallata ayyukan gwamnatin.

A cewarsa "wasu daga cikinsu na gudun magana a talabijin, ko rediyo. Ya nemi su daina yin hakan, su fita su bayyana ayyukan da suke yi."

Babu tabbas game da dalilin da ya sa Tinubun zai yi sauyin a daidai wannan lokaci.

Dalilai biyar da ka iya sa Tinubu yin garambawul

Masana irin su Dakta Elharoon Mohammad, masanin kimiyyar siyasa kuma malami a sashen nazarin diflomasiyyar ƙasa da ƙasa a kwalejin fasaha da ke Kaduna ya ce dalilai biyar ne yake ganin ka iya tilasta shugaba Tinubu yi wa ministocinsa garambawul.

..

Asalin hoton, Shettima/X

Bayanan hoto, Majalisar Ministocin

Matsin da ƴan Najeriya ke ciki

..

Asalin hoton, Shettima/X

Masanin ya ce tun bayan hawan shugaba Tinubu Najeriya ke fama da matsalar ƙaranci da tsadar man fetur da hauhawar farashin kayan abinci d sauran su wani yanayi da ya jefa ƴan Najeriya cikin halin matsi.

"A matsayinsa na ministan man fetur ya gaza samar da mafita ga ƴan Najeriya dangane da wahalhalun da suke fuskanta a kan man fetur. Sun ce za a cire tallafi amma har yanzu al'amarin bai daidata ba. An ce idan matatar man Ɗangote ta fara aiki al'amura za su gyaru amma abin ma sai ya ƙara rincaɓewa.

Wannan yanayi zai iya saka Tinubu tunanin buƙatar sauya sabon lale ko za a samu sauƙi."

Zargin rashawa da ta'addanci ga wasu ministoci

Dakta Elharoon ya ce akwai wasu daga cikin ministocin Tinubu da ke fuskantar zarge-zargen ta'addanci da ma rashawa da cin hanci waɗanda ƴan ƙasar ke ta kiranye-kiranyen a cire su.

"Wataƙila Tinubu ya fuskanci cewa irin waɗannan ministoci ka iya taɓa ƙimar gwamnatinsa saboda ƴan ƙasa za su ga kamar gwamnatin tana sane da zarge-zargen da ake yi musu kuma tana ba su kariya.

Kenan idan aka cire su daga muƙamansu hakan zai sa jama'a su daina yi wa gwamnatin kallon tana ɗaure wa waɗanda ake zargi da laifuka gindi. To wannan na ɗaya daga cikin dalilan da nake ganin sun tilasta Tinubu yin garanbawul." In ji Dakta Elharoon.

Rashin cancantar wasu ministoci

Dakta Elharoon ya ce akwai ƙorafe-ƙorafe daga ƴan Najeriya dangane da cancantar wasu ministocin musamman bisa la'akari da ma'aikatun da aka ba su.

"Ana ganin akwai ministocin da bai dace a ba su wasu ma'aikatu su riƙe ba saboda rashin ƙwarewa a fannin. To wataƙila yanzu Tinubu ya fahimci hakan shi ne zai yi wannan kwaskwarima."

Sakayyar siyasa

Malam Elharoon ya ce shugaba Tinubu farkon zuwansa ya yi ƙoƙarin yi wa wasu ƴan siyasar da suka taya shi ya ci zaɓe sakayya ta hanyar ba su muƙamin minista kuma bayan shekara guda yake son ya sauya.

"Wataƙila yanzu yana ganin ya gama yi musu sakayya saboda haka yana son kawo wasu daban wataƙila waɗanda za su yi aiki ko kuma wasu ƴan siyasa da a baya ba a samu damar saka musu ba."

Kasafin kuɗi na 2024

"Har yanzu ba a fara sakin kuɗaɗen kasafin 2024 ga ma'aikatu ba. Wataƙila shugaban ƙasa ba shi da ƙwarin gwiwar cewa ministocin nasa za su yi adalci.

Wataƙila shi ya sa shugaban yake so ya sauya ministocin ko kuma a sauya musu ma'aikatu kafin a fara sakin kuɗaɗe ga ma'aikatu." In ji dakta Elharoon Mohammed.

Yi wa majalisar ministoci ko kuma ta kuma kwamishinoni a jihohi ba sabon al'amari ba ne, inda shugaban ƙasa ko gwamna kan sauya wa ministoci ko kwamishinoni ma'aikatu ko kuma maye gurbinsu da wasu sabbi.

Ana dai alaƙanta yin garanbawul ɗin idan shugaba ya fahimci rashin ƙwazo ko kuma rashawa da cin hanci a tsakanin majalisar zartarwarsa.

Sai dai za a iya cewa gwamnatin da ta gabaci ta Tinubu wato ta tsohon shugaba Muhammdu Buhari ba ta yi irin wannan garambawul ɗin ba, duk kuwa da irin ƙorafe-ƙorafen da ƴan ƙasar suka yi ta faman yi.