Ba ni da wani zaɓi sai dai na koma Ukraine - Ɗalibi ɗan Najeriya

Hoton dalibi dan Najeriya

Asalin hoton, Olawale

Yayin da yake tafiya cikin garin Legas, birni mafi cunkoso a Najeriya, Oyewumi Azeez Olawale ya kama hanya domin zuwa neman biza.

Shekara guda baya, ɗalibi ne da ke karatun likita, wanda dan asalin Najeriya ne ya yi ta faman yadda zai samu hanya ya fice daga Ukraine, bayan mamayar da Rasha ta fara yi wa ƙasar a ranar 24 ga watan Fabarairu.

Amma duk zaɓin da yake da shi na samun karatu a wasu wuraren ba sa aiki, don haka ya koma Ukraine a cikin shekarar domin wani karatun.

Yanzu yana son ƙara komawa kuma.

"Ina da buƙatar komawa Ukraine saboda ina buƙatar kammala shekarar karatuna ta ƙarshe, in rubuta jarrabawata ta ƙarshe in karɓi shaidar karatuna,''

in ji matashin ɗan shekara 28. “Ba ni da wani zaɓi a nan gida Najeriya,” in ji shi.

Akwai daliban ƙasashen waje 80,000 a Ukraine a 2020, kuma kusan kashi ɗaya cikin huɗu duk daga Afrika suke.

Wasu na ta neman yadda za su koma Ukraine saboda sun gaza samun yadda za su kammala karatunsu.

A wajen Olawale, zaɓinsa mai sauƙi ne.

A watan Yulin 2022, Kungiyar Likitoci ta Najeriya ta ce ba za ta sake karɓar digiri daga jami’o’in Ukraine wanda ake yi a intanet ba. Wani mataki da hukumar ta Ghana ta yi koyi da shi watanni biyu baya.

"Ina buƙatar na kammala digirina," in ji Olawale.

Ya yi nisa a inda yake karatun ya yi nesa da inda ake rikicin.

Inda nake karatu ba ya fuskantar barazana," in ji Olawale.

Wasu kuma ba su yi sa'a ba kamar shi.

.
Bayanan hoto, Jessica Orakpo ta maƙale a Ukraine lokacin da aka fara yaƙin Rasha
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ukraine gida ne mai sauƙi ga masu neman ilimi mai sauƙi a Turai, kasar ta yi fice a wajen bayar da bizarta kai tsaye, babu tsada ga ilimin mai inganci.

Bayan kwashe shekaru suna tara kuɗaɗen da za su yi digiri da su, komawa gida hannu fayau zai zama wani zaɓi marar daɗi ga ɗalibai masu yawa.

Amma lalubo wata makarantar da za su ƙarasa karatunsu ba abu ba ne mai sauƙi.

Jessica Orakpo wata ɗalibar likitanci ‘yar Najeriya wadda ta fuskanci wariyar launin fata lokacin da take neman tserewa daga Ukraine a bara, tana cikin ɗaliban da ke shirin komawa.

Da farko ta tsere ne zuwa Hungary kafin daga bisani ta koma Netherlands inda yanzu take tare da wasu iyali da suka sauke ta.

Bizar da aka ba ta ta wucin-gadi wa’adinta ya kare kan ta samu ɗan aikin da za ta riƙa yi.

Bayan ta kammala makaranta a 2022, yanzu ta zama cikakkiyar likita, amma ta ce neman aiki ba tare da mutum ya iya yaren garin ba, wani babban ƙalubale ne.

"Zaɓin da nake da shi kawai shi ne na ci gaba da zama a nan ko na koma Ukraine.

"Ina da abin da nake neman cimmawa a rayuwata, shi ne na yi aikin likitanci," in ji ta, amma tana cewa matsalar tsaro a Najeriya ba za ta ba ta damar hakan ba.

Samun bizar komawa Turai zai iya zama abu mai wuya a gareta, ganin cewa ta fita daga ƙasar tun 2016, ba ta da asusun banki ko wani tsayayyen adireshi a Najeriya.

,

Asalin hoton, Damilola

Kamar dai sauran ‘yan Najeriya Fehintola "Moses" Damilola wanda yake karatun likitanci a yankin Sumy da ke kusa da iyakar Rasha, na faɗi tashin ci gaba da karatunsa ta intanent, duk da cewa hukumomi sun ce ba sa karɓar digirin da aka yi ta intanet.

"Muna ta faɗi tashi tun daga nan," in ji Damilola.

"Ba na son komawa Unkraine a yanzu,” kamar yadda ya yi bayani. "Maƙalewar da na yi a Sumy lokacin da aka fara hare-hare da wuyar da na sha lokacin fitowa ba na fatan sake faɗawa cikinsu".

Amma duk da haka Damilola ya san wani ɗalibin Indiya da ya koma Ukraine domin ƙarasa jarrabawarsa ta ƙarshe.

Ba a rubuta jarrabawar bara ba saboda yaƙi. Amma hukumomi a Ukraine sun ce za a shirya jarrabawar ne ga ɗaliban da suke Kyiv a ranar 14 ga watan Maris.

Sai dai akwai wani shiri da aka yi wa “waɗanda ba sa son komawa Ukraine” an samar da kwamfuyuta 140 domin gwaji a cibiyoyi da suke faɗin duniya”, sai dai babu cikakken bayani kan hakan.

"A zahiri, ba mu da wani zaɓi a ƙasa,” in ji Damilola.

D

Hukumar ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce, kimanin mutum miliyan takwas ne suka tsere zuwa makotan kasashe da ke Turai.

Hukumar kula da ‘yan cirani ta duniya IOM ta ce cikin wannan adadin akwai mutum 625,000 waɗanda ba ‘yan Ukraine ba, amma ta ce zai iya yuwuwa wasu a ƙirga su sau biyu.

Zaɓi zuwa wasu makarantun na da na shi ƙalubalen da suka haɗa da wahalar biza da matsalar harshe da kuma kuɗin makaranta mai tsada.

,

Asalin hoton, Victoria

Yayin da wasu ɗaliban ke raba daya biyu kan komawa Ukraine, wasu, irin su Victoria Osseme, ita ba ma inda ta je.

‘Yar Najeria na kiran kanta "mace ɗaya baƙa da ta rage a Kharkiv, a Ukraine".

Bayan samun digiri biyu da ta yi, yanzu ta kwashe shekara tara a ƙasar, ta ce ita yanzu ta zama “yar Ukraine”.

"Ba zan iya barin Ukraine ba a wannan mawuyacin lokacin" a cewarta.

"Ya kamata na nuna musu goyon bayana ta hanyar tsayawa tare da su, mu ji raɗaɗin da suke ji tare."

Ta riƙa wallafa abin da ta gani a kafafen sada zumunta tun watan Afrilun 2022, kuma ta ce mutanen Ukraine sun riƙa nuna jin dadi da goyon baya a gareta.

"Iyalina da abokai da ƙawayena suna alfahari da ni da na tsaya nake wakiltar Najeriya."

Ta riƙa fama da sanyi, ga barazanar tashin bam, ga raunuka da ta ji da fashewar gilasan taga.