Ana tilasta wa 'yan ci-rani shiga yaƙin Rasha

Russian men mobilised to fight in Ukraine

Asalin hoton, Getty Images

Wasu rahotonni na cewa ƙungiyar sojojin hayar Rasha ta Wagner ta ɗauki dubban fursunonin aikin soji domin shugar da su cikin yaƙin Ukraine.

To amma saboda yawane mace-mace da raunuka da ake samu ya sa ana wahalar samun masu son shiga yaƙin, ko da kuwa daga gidajen yarin ƙasar

Fursunoni da dama a yanzu na cikin fargabar cewa za a tilasta musu shiga yaƙin, haka kuma 'yan ci-rani ƙasashen Asiya na samun kansu cikin wannan yanayi.

Anuar ya je Rasha domin neman aiki a shekarar 2018. Daga baya kuma aka ɗaure shi a gidan yari saboda laifin safarar ƙwaya, inda aka tura shi gidan yarin Penal Colony Number Six da ke yankin da shugaban ƙasar Putin ya fito. BBC ba za ta ambaci cikakken sunansa da ƙasarsa ta asali ba saboda dalilai na tsaro.

A ƙarshen watan Janairu, ya shaida wa mahaifinsa cewa an tilasta wa wasu 'yan yankin Asiya da kle tsare a gidan yaƙin shiga yaƙin Ukraine ba tare da son ransu ba.

''Akwai 'yan kasashen Uzbekistan da Tajikitans da Kyrgyzstan da dama a cikin gidan yarin. Kuma yanzu suna shirin ƙara tura wasu fursunonin zuwa yaƙin na Ukraine, kuma ɗana na cikin fargabar kasancewa cikin fursunonin da za a tura,'' Kamar yadda Mahaifin Anuar ya shaida wa BBC.

BBC ta samu ganin takardun kotu da wasiƙun Anuar waɗanda suka tabbatar da cewa lallai Anuar na wannan gidan yarin.

Kuma bayanin da ya yi na cewa an tilasta wa wasu fursunoni shiga yaƙin Ukraine cikin watan Janairu ya yi daidai da wani rahoto da diraktar wata ƙungiyar kare hakkin 'yan adam a ƙasar mai suna Olga Romanova.

Iyayen waɗannan fursunoni sun je gare ta domin neman taimakonta.

"Ba a ba su zai ba. Kawai an ce musu su sanya hannu a kan takarda daga nan aka aika da su filin daga kara zube ba tare da samun cikakken horo ba'', in ji Ms Romanova

Olga Romanova

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ta ƙara da cewa tun da farko iyayen fursunonin sun so zuwa kotu domin ganin cewa 'ya'yan nasu ba su je Ukraine ba.

To amma sun ƙi, saboda tsoron horon da 'yayan nasu za su iya fuskanta idan suka ci gaba da zama a gidan yarin.

Gidan yarin Penal Colony Number Six ya yi fice wajen gallazawa fursunoni. Olga Romanova ta bayya shi da gidan yarin muzgunawa''. A gidan yarin ne dai aka tsare fitaccen ɗan adawar ƙasar Alexei Navalny.

Hukumomin gidan yarin dai ba su mayar da martani ba kan buƙtar da BBC ta neme su da su yi kan zarge-zargen da ake yi musu na tilasta wa fursunoni shiga aikin soji, domin kai su fagen daga a yaƙin Ukraine .

Ɗaukar sojoji a gidan yari ya fi sauƙi, to amma amma abubuwa na sauyawa saboda yadda Wagner ke fuskantar asarar sojoji masu yawa a fagen daga.

Ana ɗaukar 'yan asalin yankin gabashin Asiya domin yi wa Rasha yaƙi ta fannoni da dama, ba sai kawai waɗanda ke gidan yari ba.

A gaba ɗaya akwai 'yan ci rani kusan miliyan 10.5 daga ƙasashen Uzbekistan da Tajikistan da kuma Kyrgyzstan da ke aiki a Rasha, kamar yadda wasu alƙaluma daga hukumar ma'aikatar cikin gida ta ƙasar ta bayyana. Wannan kuma abu ne da zai yi wa ƙungiyar Wagner daɗi.

A Wagner centre set up in St Petersburg

Asalin hoton, Getty Images

Hukumomin Rasha sun sun bayar da dama ga mutanen da ke son shiga aiki sojin ƙasar a cibiyar kula da 'yan cirani ta ƙasar da ke birnin Moscow.

Akwai kuma tallace-tallacen shiga aikin soji kyauta a Rasha da ake yi wa 'yan ƙasashen Uzbekistan da Kyrgyztan da kuma na Tajikistan da harsunan ƙasashensu.

To amma 'yan gwagwarmaya na cewa ba koyaushe hakan ke zama kyauta ba.

Valentina Chupik wataq mai rajin kare haƙƙin ‘yan ci-rani ta shaida wa BBC cewa a wasu lokutan a kan tituna ‘yan sanda ke tsayar da ‘yan ci-rani ‘yan asalin Asiya su riƙa razana su kan lallai sai sun shiga aikin soji a ƙasar in ba haka ba kuma a fitar da su daga ƙasar.

Mafi yawan ‘yan ci-rani ba su da takardun izinin zama a ƙasar, dan haka suke zama a wuraren da ba a yi wa rajista ba, ko suka saɓa wa dokokin ci-rani. Dan haka wannan shi ne dalilin da ya sa ake tilasta musu shiga aikin soji cikin sauki.

Aziz (wanda ba sunansa ne a ainihi ba) wanda ke da takardar zama ta ƙasashen Rasha da Tajikistan ya faɗa wa BBC cewa an tsare shi ne a lokacin da ‘yan sanda suka kai mamaye wajen da suke aikin gini.

An ce za a kai shi ofishin ‘yan sanda domin tantance takardun izinin zamansa, amma sai ya tsinki kansa a sansanin ɗaukar soji.

Daga nanne kuma ya fara yi wa ‘yan sandan tsawa yana tambayarsu dalilin da ya suka yi masa ƙarya, sai kawai suka ɗaure hannayensa tare da jefa shi cikin mota.

Daga ƙarshe dai sun sake shi.

To amma mafi yawan ‘yan ci-rani a Rasha na tsaron jami’an tsaro kan tilasta musu shiga aikin soji domin kai su fagen daga.