Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Kuɗin cizo sun hana mu kwana a gidajenmu'
A Harare, babban birnin ƙasar Zimbabwe, hukumomi na fafutikar ganin sun yaƙi ƙananan ƙwarin nan masu shan jinin ɗan'adam, wato kuɗin cizo.
Mazauna unguwar Mbare da ke babban birnin sun shaida wa shirin BBC na Focus on Africa Podcast cewa sun gaji da rayuwar ƙawanya da kuɗaɗen cizo suka musu.
"Yanzu ba ma iya bacci a gidajenmu, da zarar yamma ta yi za ka ji yara na ta ihu saboda kuɗin cizo sun addabe su, ba mu iya ziyaratar ƴan'uwanmu haka nan su ma ba su iya ziyartar mu, duk saboda kuɗin cizo," in ji wata mata da ke zaune a unguwar.
Shi ma wani magidanci cewa ya yi "Wasunmu sun jefar da kujerunsu na gida, mun yi watsi da gadajenmu, mun yi watsi da bargunanmu."
Wannan dai ba shi ne karon farko da unguwar ta yi fama da annobar kuɗin cizo ba, kasancewar an samu irin hakan a shekarar da ta gabata – 2024, kamar yadda hukumomi suka bayyana.
Kuɗin cizo sun sanya darare sun zama tashin hankali ga mazauna unguwar, inda yanzu al'ummar yankin ke neman inda za su sa kansu.
"Yanzu ba ma jin daɗin zama a gidajenmu kwata-kwata, ko ka zauna ka ce za ka kalli talabijin ba za ka iya ba saboda za su yi ta cizon ka, da dama daga cikinmu duk mun yi watsi da kayan ɗakuna da gidajenmu, kwana a tantagaryar ƙasa ma ya fi mana kwanciyar hankali."
Wata babbar matsala da ake fuskanta ita ce yadda kuɗin cizon suka bijire wa matakan da hukumomin birnin suka ɗauka na yaƙi da su ya zuwa yanzu, kamar feshi da zuba magungunan ƙwari.
Yanzu kuɗin cizon na ci gaba da yaɗuwa suna ƙoƙarin mamaye wasu unguwannin baya ga Mbare.
Ba a Zimbabwe kawai ake samun ɓarkewar annobar kuɗin cizo ba, domin an samu hakan a wasu manyan birane na duniya, kamar London na Birtaniya da New York na Amurka da kuma Paris na ƙasar Faransa.
Me ya janyo annobar
BBC ta tuntuɓi Dakta Michael Vere, wanda masani ne kan cutuka masu yaɗuwa da ke aiki a hukumar gudanarwar birnin Harare.
Yana daga cikin waɗanda ke jagorantar wannan yaƙi da ake yi da kuɗin cizon da suke neman karɓe iko da wasu unguwannin birnin.
Dakta Michael ya ce tabbas an shigo da kuɗin cizon ne daga wani wuri zuwa yankin, kafin suka samu gindin zama.
Ya ce "abin da muke kyautata zato shi ne an shigo da su ne ta hanyar gwanjon kayan ɗaki ko na sawa da mutane ke amfani da su.
Ya ƙara da cewa "musamman a unguwar, mun gano cewa ana yawan hada-hada da cinikayyar gwanjo waɗanda ake kawowa daga ƙasashen ƙetare."
"Abin da ke faruwa shi ne ana shigo da waɗannan kaya na gwanjo ba tare da an ɗauki wani mataki na tsaftace su ba."
Sana'ar kayan gwanjo dai haramun ce a dokokin birnin na Harare sai dai mutane na ci gaba da yin ta - musamman a wata kasuwar gwanjo da ta shahara wadda ake kira Mupeta Nambu - sanadiyyar ƙarancin wadata.
Duk da cewa kuɗin cizo ba ya haifar da wata cuta takamaimai, to amma cizon na hana mutane sukuni haka nan yana iya haifar da ƙuraje da ƙaiƙayi da kuma rashin bacci.
Kuɗin cizon, a cewar masana sun fi kuzari ne a cikin dare saboda suna son duhu.
Haka nan kuma ana alaƙanta yawaitar kuɗin cizo da rashin tsafta musamman a wuraren da ake da cunkoson mutane.
Ta yaya mutum zai hana kuɗin cizo shiga gidansa?
- Tabbatar da tsaftar kayan gwanjo da mutum ya saya
- Wanke tufafi da ruwan zafi, wanda ya kai zafin maki 60 a ma'aunin zafi
- Tsaftace gida a kai a kai
- Gyaran gida: kamar sake sabon yaɓe da fenti kasancewar kuɗin cizo na ɓoyewa a ramukan bango
Sai dai Dakta Ver ya buƙaci al'ummarr unguwar su shanya kayan da ake tunanin suna ɗauke da kuɗin cizo a rana, saboda ƙwarin ba sa ƙaunar zafin rana.