Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Fargabar ɗiban kuɗin-cizo a birnin da zai yi baƙin fita kunya
- Marubuci, Daga Hugh Schofield
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC daga Paris
Wata annobar kuɗin-cizo ta auka wa birnin Paris da sauran biranen Faransa, wanda ya zama wani abin damuwa na samuwar mamayar waɗannan ƙwari, abin da ya jefa shakku da tambayoyi game da lafiyar jama'a a lokacin da za a gudanar da wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na Olympics a shekara mai zuwa.
Wannan shi ne batun da ake ci gaba da tattaunawa a ƙasar kuma a yanzu ya mamaye kafafen watsa labarai na duniya.
Duk da wani ɓangare na labarin akwai ƙamshin gaskiya a cikinsa sai dai wani ɓangaren akwai saɓanin haka.
Abin damuwar shi ne yadda ake samun ƙaruwar waɗannan ƙwarin na kuɗin-cizo a makonnin da suka wuce - wanda ya zama tamkar an koma baya a 'yan shekarun da suka gabata.
''A duk ƙarshen damina muna samun yawaitar kuɗin-cizo" in ji Jean-Michel Berenger, wanda masani ne a kan rayuwar ƙwari a babban asibitin Marseille da ke Faransa.
"Wannan kuwa bai rasa nasaba da yadda mutane ke yawan tafiye-tafiye a watannin Yuli da Agusta, kuma ana ganin ƙwarin kan maƙale ne a jakunkunansu."
"Kuma a kowace shekara, adadin da kan ƙaru ya zarta na wadda ta gabace ta."
A birnin Paris, akwai fargaba sosai kan wannan musamman tsakanin mazauna (kamar yadda alƙaluma suka nuna duk mutum ɗaya cikin 10 da suka taɓa fuskantar irin haka a shekara biyar da ta wuce) sun daɗa bayyana yanayin abin da ya jefa sabuwar fargaba.
Kwanan nan, an ga irin waɗannan rahotannin da ba a tabbatar da su ba a gidajen sinima, amma kuma an ɗauke su da matuƙar muhimmanci.
Haka ma akwai iƙirari daga jama'a cewa kuɗin ya cije su lokacin da suke tafiya a jiragen ƙasa.
A yanzu dai ana ci gaba da kiran mahukuntan birnin Paris da gwamnatin Emmanuel Macron da su ɗauki mataki a kan lamarin.
Ya dai danganta daga yadda suka ɗauki batun - da kuma yadda suke hanƙoron kare martabar birnin Paris daidai lokacin da ake tunkarar wasannin a 2024 mai zuwa - ta yadda ba su ɗaukar kowa ne matakin da ke nuna zancen bazuwar kuɗin-cizo a matsayin shaci-faɗi kawai a kafafen sada zumunta.
A wannan zamani ana samun labarai masu ban tsoro da ke yaɗuwa cikin sauri a shafukan intanet da ke bayar da bayanai a kan muhimman batutuwa da suka shafi rayuwar mutane da kuma suka zarta na jaridu a baya.
Masu gidajen sinima sun fara nuna damuwa saboda ƙarancin masu zuwa kallo kuma sun damu tun daga lokacin da aka samu wasu hotunan bidiyo da ke yawo inda a ciki aka ga ƙwari nau'in gara a saman kujerun zama.
Inda fasinjoji a tashohin jiragen ƙasa suka soma binciken jakunkunansu yayin da wasu suka gwammace su yi tsaye a maimakon zaunawa.
"A wannan shekarar an samu wani sabon abu - wanda kusan ya zama babbar damuwar al'umma" in ji Mista Berenger.
"A wani ɓangare batu ne mai muhimmanci saboda zai sa mutane su farga ta hanyar lura da matsala, kuma su soma yaƙar kudin-cizo da wuri shi ne mafi dacewa.
"Amma a ƙashin gaskiya an yi ƙarin gishiri a labarin wannan matsala."
A zahiri take dai kuɗin-cizo ya sake dawowa, duk da yake ya daɗe a ƙasar kusan shekara 20 ko 30.
Amma wannan ba Faransa kawai ya shafa ba kusan lamari ne da ya karaɗe duniya.
Akwai abubuwa da dama waɗanda dunƙulewar duniya wuri ɗaya da kasuwanci da yawon buɗe ido da kuma ƙaurar jama'a suka haddasa.
Amma sauyin yanayi ba ya ciki. Kuɗin-cizo ya zama wata halittar da aka saba da ita, akan same ta duk inda ɗan'Adam ke rayuwa.
Haka ma yanayi bai cikin abubuwa da ke haddasa yaɗuwarta.
Bayan da Yaƙin Duniya na Biyu ya zo ƙarshe kuɗin-cizo - kamar dai sauran halittu - ya ragu matuƙa sakamakon samuwar wani maganin kashe ƙwari na DDT.
Bayan wasu shekaru aka hana amfani da maganin DDT da wasu magungunan kashe ƙwari saboda an gano suna da lahani ga mutane.
Hakan ya sa an samu wani nau'in ƙwarin da suka ɓulla bayan da aka kashe kakanninsu da wancan magani na DDT.
Amma waɗannan suna jure wa sinadaran da ke kashe irin waɗancan ƙwari.
A cewar Mista Berenger, a ƙasashen da suka ci gaba, za a ga mutane na matuƙar tsoron kuɗi saboda har an manta da su. Amma a wasu sassan duniya kuma, sun zama jiki.
Dalili na uku kuwa ya yuwu saboda an samu ƙarancin kyankyasai ne waɗanda ke kashe kuɗin-cizo.
Sai dai fa a lura babu mai son cika gidansa da kyankyasai domin su kashe masa kuɗin-cizo.
A ƙashin gaskiya kuɗin-cizo babbar barazana ce - sai dai haɗarin ya fi shafar tunani fiye da lafiya kuma abu ne da ake matuƙar fargaba sai dai ba ya baza cuta. Ana ƙyamar cizonsa amma shi ma zafin cizon ba ya jimawa a jiki.
Halitta ce mai sauya jikinta lokaci zuwa lokaci, takan bar kashinta barkatai da za a gan shi baƙi-baƙi (tamkar nason jinin), da ta ji warin mutum takan dinga motsi maras daɗi, kuma tana iya kwashe shekara ɗaya cur ba tare da cin abinci ba. Duka dai labarai ne masu ban tsoro da za ku iya hasashensu.
Amma babban lahanin da take da bai wuce saka damuwa a ƙwaƙwalwa ba.
A bara yarona mai shekara 29 ya ga kuɗin-cizo a ɗakinsa. Hakan ya sa ya watsar da shimfiɗar da ke kan gadonsa, ya wanke dukkan kayan sawarsa, ya tsaftace ko'ina amma duk da haka ya kasa ci gaba da bacci a ɗakin. Ya dinga tunanin ga wasu halittu nan na tafiya a jikinsa.
Da hakan ta faru bai samu natsuwa ba sai da wani kamfani da ya shahara wajen kashe ƙwari ya yi feshi a ɗakinsa sannan fa ya samu damar runtsawa. Wasu masu yaƙi da ƙwari masu cutarwa na gano su ta hanyar amfani da karnukan da suka shahara wajen sunsuno abubuwa.
"Samun kuɗin-cizo ba lamari ne da ya dace a yi sakaci da shi ba," in ji Berenger. "Amma akwai labarai da dama da ba a kai gare su ba, game da yadda suke bazuwa cikin sauri daga wannan wuri zuwa wancan".
"A ganina hanyar yaƙi da bazuwar kuɗin cizo ba sai an gayyato kowa da kowa ba, face a nemi fitattun masu feshin maganin kashe ƙwari kawai.
Lokacin da aka nemo mai feshin magani shi da abokan aikinsa sun ga ɗaruruwan waɗannan ƙwari na ta yawo saman juna a cikin taufafi da bayan ƙofofi da bayan hotunan bango, ga kuma ƙwayaye nan birjik."
'A kowa ne lokaci ɗaya daga waɗannan mutane ya bar gidansa tamkar yana baza kuɗin-cizo ne, kuma irin su ne ke matuƙar neman taimako