Dalilai biyu da ke janyo tsaiko ga shari'ar Sheikh Abduljabbar Kabara

Lokacin karatu: Minti 4

A ranar 15 ga watan Disamban 2022 ne babbar Kotun Shari'ar Musulunci ta Jihar Kano ta yanke wa Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samun sa da laifin yin kalaman rashin ladabi ga Annabi Muhammad SAW.

Alƙalin kotun, mai shari'a Sarki Yola ya ce malamin ya na da kwana 30 don ɗaukaka ƙara idan bai gamsu da hukuncin ba.

Sai dai tun wannan lokacin ba a ƙara jin batun ɗaukaka ƙarar ba, sannan ba a ji labarin zartar masa da hukuncin da kotun ta yanke masa ba.

Katsam a ranar 14 ga watan Oktoba sai iyalai da almajiran Malamin suka wayi gari ba su gan shi a inda yake a gidan yari na Kurmawa da ke Kano ba, duk da cewa daga bisani hukumomin gidan yarin Kuje da ke Abuja sun tabbatar da cewa Malamin na hannunsu.

Wannan ya sa wasu ke ta kiraye-kirayen a yi wa malamin adalci na kodai a zartar masa da hukuncin da kotu ta yanke masa ko kuma a sake shi idan ba a same shi da laifi ba, bayan ɗaukaka ƙarar.

BBC ta yi bincike dangane da dalilan da suka hana har yanzu malamin ya ɗaukaka ƙara, kimanin shekaru uku tun bayan yanke masa hukunci, inda ta tattauna da wani lauya da ya lissafa dalilai guda biyu.

'Abduljabbar na faɗa da lauyoyi'

BBC ta tattauna da wani lauya da bai so a ambaci sunansa ba wanda ya ce babban dalilin da ke janyo tsaiko ga shari'ar Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara shi ne rashin lauyoyin da za su tsaya wa malamin.

"Tun a baya a ƙaramar kotu Malam Abduljabbar ya rinƙa faɗa da lauyoyinsa inda ya rinƙa korar su bisa zargin haɗa baki da hukumomi da zamba cikin aminci.

Idan ba a manta ba, akwai lokacin da a kotu ma ya ce lauyan ba ya wakiltarsa.

Sannan ya nemi cewa shi ne mutumin da zai tsaya a gaban kuliya domin kare kansa. Aƙalla ya kori lauyoyinsa fiye da guda uku," in ji lauyan.

Lauyan ya kuma ƙara da cewa to wannan abun da ya faru da lauyoyi tun farkon shari'ar ka iya zama abin da ke bai wa lauyoyi tsoro.

"Wataƙila hakan ne ya sa samun wasu lauyoyi su tsaya masa zai zama da wuya saboda irin abin nan na gani ga wane, ya ishi wane tsoron Allah."

'Tsoron tsangwama'

Babban lauyan ya ƙara da cewa dalili na biyu da ke janyo tsaiko a shari'ar malamin shi ne tsoron tsangwama daga jama'a da wasu lauyoyi ke ji.

"A arewacin Najeriya samun lauyan da zai kare Abduljabbar sai jajirtacce wanda zai toshe kunnuwansa daga abin da al'umma za su faɗi a kansa. Mun san irin barazanar da lauyoyin da suka yi masa aiki suka fuskanta daga gwamnati da al'umma da ma ƙungiyoyin addini."

"An haɗa wasu da iyayensu. An yi wa wasunsu barazanar kisa. Wasu kuma an tsorata da su cewa ba sa son annabi tunda suke kare Abduljabbar. To ka ga zai yi wuya a samu wani lauya daga arewacin Najeriya da zai jure irin wannan tsangwama da za ta iya janyo masa rasa ransa," in ji babban lauyan.

Shawara 6 ga Abduljabbar da al'umma

Babban lauyan ya bayar da shawarwari ga Sheikh Abduljabbar da gwamnati da ma al'ummar Musulmi na jihar Kano da Najeriya baki ɗaya.

  • Dole ne Sheikh Abduljabbar ya yarda cewa lauyoyi ne kawai za su iya tsaya masa domin kare kansa. Idan kuma bai yarda da haka ba to abin da ya faru da Nnamdi Kanu a jiya to shi ne zai faru da shi.
  • Ya kamata lauyoyin arewa sun fahimci cewa shi fa adalci sunansa adalci. Dole ne a samu waɗanda za su fito su nemi a ɗaukaka ƙarar nan domin kawo ƙarshen shari'ar -kodai a zartar masa da hukuncin da aka yanke masa ko kuma a sake shi idan ba shi da laifi.
  • Dole ne lauyoyinmu na arewa su fito su tsaya wa malamin nan kafin ƴan kudanci su farga su kawo masa ɗauki. Mun ga yadda Femi Falana ya tsaya wa Ibrahim Elzakzaky. Sannan yanzu mun ga yadda ɗan gwagwarmayar nan, Omowole Sowore ya kai wa Abduljabbar ziyara a Abuja. Wani yana nuna cewa zai iya samun ɗauki daga ƴan kudu.
  • Ga gwamnatin Kano kuma ya kamata ta rufa wa kanta asiri ta tsame hannunta daga wannan shari'a ta bar Abduljabbar da malaman da suke tuhumar sa.
  • Ga al'ummar Musulmi na Kano da Najeriya, ya kamata su sani cewa kotu ce kawai za ta iya samun mutum da laifi saboda haka zuwa kotun ɗaukaka ƙara da wasu ba sa so ba wai zai sa a saki malamin ba ne illa dai kawai a tabbatar da hukuncin kotin farko ko kuma a soke shi.
  • Iyali da almajiran Sheikh Abduljabbar kuma dole ne su yi bincike su tabbatar da a ina aka tsaya dangane da ɗaukaka ƙarar da aka fara maganar ɗaukaka ƙarar.

Wace dama ta rage wa Sheikh Abduljabbar?

Babban lauyan ya shaida wa BBC cewa duk da cewa an shekara kimanin uku daga ranar da aka yanke wa malamin hukuncin kisa, ba tare ɗaukaka ƙara ba, har yanzu yana da damar yin hakan.

"Ita doka tana da wasu irin damarmaki da yawa. Akwai sassan dokoki na kotun ɗaukaka ƙara misali a umarni na shida na dokokin kotun ɗaukaka ƙara sun bayar da damar saka wasu buƙatu da zai bayani na dalilan da ya sa bai saka takardun ɗaukaka ƙarar ba kuma za a ba shi dama a saurare shi."

Dangane kuma da idan kotun ɗaukaka ƙarar ita ma ta amince da hukuncin kotun farko kan hukuncin kisa, lauyan ya ce nan ma yana da dama ta gaba.

"Wannan ai babban kes ne saboda haka ma bayan kotun ɗaukaka ƙara yana da damar zuwa kotun ƙoli ya ƙalubalanci hukuncin kotu," in ji babban lauya.