Bikin baje kolin ado da kwalliya a sassan Afrika cikin hotunan Afrika na mako

    • Marubuci, Natasha Booty
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 3

Wasu daga cikin zaɓaɓɓun hotunan Afrika na wannan makon.

Mata biyu kusa da bishiyoyi. Kayan da suka sanya sun ɗauki hankali sosai da kuma annurin fuskar su. An ɗauki hoton ne ranar Asabar 7 ga watan Disambar 2024.

Asalin hoton, John Wessels / AFP

Bayanan hoto, Masu tallar kayan ado suna baje kolin al'adunsu a taron makon kayan ƙawa na birnin Dakar a ƙasar Senegal.
Adama N'Diaye ta baje kolin ta a birnin Dakar na ƙasar Senegal.

Asalin hoton, Cem Ozdel / Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Asabar ɗin kuma shahararriyar mai tallar kayan ƙawa ƴar asalin Senegal da ta koma Faransa, Adama N'Diaye ta baje kolin ta.
Wata mata sanye da kayan ado da manyan ƴankunne, sanye da jan-baki da sauran kayan ado a birnin Dakar na ƙasar Senegal, a ranar Asabar 7 ga watan Disambar bana.

Asalin hoton, Cem Ozdel / Getty Images

Bayanan hoto, Kayan da ta baje kolin su a wajen sun ɗauki hankali kuma sun ƙayatar sosai.
Mata sun tsaya a kan layi. An ɗauki hoton su daga ƙugu zuwa ƙafafu, suna sanye da siketi da wanduna da aka ɗinka da atamfofi. An ɗauki hoton ne a wajen bikin makon baje kolin kayan kwalliya na Najeriya da aka yi a Lagos.

Asalin hoton, Emmanuel Adegboye / EPA

Bayanan hoto, A ranar ne kuma aka yi wani taron baje kolin ado da kwalliya a jihar Lagos ta Najeriya inda ƙwararru suka nuna ƙwarewar su.
Wasu mata biyu cikin murmushi suna nuni da alamun zaman lafiya, a wajen bikin na Afirka ta Kudu.

Asalin hoton, Sharon Seretlo / Getty Images

Bayanan hoto, Haka nan dai, a ranar Asabar ɗin ne masoya waƙoƙi suka halarci bikin da aka yi a yankin Kroonstad na Afirka ta Kudu.
Wasu masu rawa su uku sanye da jajayen kaya a wajen bikin na ƙasar Kenya.

Asalin hoton, Luis Tato / AFP

Bayanan hoto, A birnin Nairobi na ƙasar Kenya ma wani bikin baje kolin kayan ƙawa da al'adun aka yi a ranar Asabar.
Themba Gorimbo ya zana taswirar Afirka kuma ya ɗaga tutar ƙasar sa ta asali Zimbabwe, a Vegas, ranar Juma'a 6 ga watan Disambar 2024.

Asalin hoton, Chris Unger / Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Juuma'a, ɗan wasan damben Amurka wanda ɗan asalin Zimbabwe ne, Themba Gorimbo ya ɗaga tutar ƙasar tasa a Las Vegas.
Mutane sun sha baƙin fenti a jikinsu, wasu kuma ɗauke da makamai a wani biki a Foumban na Kamaru, a ranar Lahadi, 8 ga watan Disamban 2024.

Asalin hoton, Daniel Beloumou Olomo / AFP

Bayanan hoto, An kuma yi wani baje kolin na nuna ƙarfi a Kamaru, a ranar Lahadi, na al'adun Mguon. An ce bikin ya samo asali ne daga ƙarni na 14, kuma a bara Unesco ta amince da bikin ranar a hukumance.