ECOWAS ta amince da ficewar ƙasashen Sahel daga cikinta

Lokacin karatu: Minti 3

Shugabannin ƙungiyar bunƙasa tattalin arziƙin ƙasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS ko CEDEAO sun amince da ficewar ƙasashen yankin Sahel – wato Nijar da Mali da kuma Burkina Faso daga cikin ƙungiyar.

Hakan na nufin daga ranar 29 ga watan Janairu na shekara mai kamawa – 2025 ƙasashen uku – za su daina zama mambobin ƙungiyar ta ECOWAS.

Wannan mataki na shugabannin ECOWAS na amincewa da ficewar da ƙasashen uku da a yanzu ke ƙarkashin mulkin soji na cikin wani ɓangare ne na shawarwarin da shugabannin suka cimma ne a ƙarshen taronsu na ƙoli da suka yi a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja a ranar Lahadi.

A sanarwar bayan taron ƙolin da suka fitar, wadda shugaban hukumar gudanarwar ƙungiyar, Omar Touray ya karanta, jagororin ƙasashen na ECOWAS sun ce suna mutunta wannan matsaya da ƙasashen uku suka ɗauka ta raba gari da ECOWAS.

To amma kuma duk da wannan amincewa da shugabannin suka ce sun yi har yanzu, sun ce ƙofa a buɗe take ga ƙasashen uku na Sahel idan sun sauya shawarar yin adabo da ƙungiyar, suna son ci gaba da zama su yi hakan cikin wa'adin wata shida – daga ranar ta 29 ga watan na Janairu zuwa ranar 29 ga watan Yuli na sabuwar shekarar ta 2025 su koma.

Sanarwara ta ce a tsawon wannan wa'adi na wata shida, kafin bakin alƙalami ya bushe na rabuwar – tattaunawar da kwamitin sasanto ko zawarci na ECOWAS ɗin wanda shugabannin ƙasashen Senegal da kuma Togo ke jagoranta zai ci gaba da zawarcin ƙasashen uku, kan su yi karatun-ta-natsu, game da fitar tasu – idan har ƙasashen suka ga ya dace su yi watsi da matakin nasu na ficewa, to ECOWAS za ta sake maraba da su.

Shugabannin na ECOWAS sun ce matakin nasu yana daidai da tanadin doka ta 91 ta kundin dokokin ƙungiyar da aka sabunta - dokar da ta amince da 'yancin kai na kowace ƙasa, mambarta.

A nasu ɓangaren ƙasashen uku da suka raba gari da ƙungiyar ta ECOWAS, a wani mataki na yakana da kara ga ƙasashen ƙungiyar ta Afirka ta Yamma, tun da farko sun ce sun soke ƙa'idar samun takardar izinin shiga cikinsu wato biza ga 'yan ƙasashen ECOWAS ɗin baya ga haka kuma sun amince da 'yancin zaman 'yan ƙasashen na ECOWAS a cikinsu ba tare da wata takarda ba.

Shugabannin ƙasashen uku da suka yi wa ECOWAS tawaye sun ce sun yi hakan ne da nufin yauƙaƙa abokanta da zaman 'yan uwantaka domin yauƙaƙa daɗaɗɗiyar alaka ta shekaru aru-aru a tsakanin al'ummomin nahiyar Afirka.

Tuni daman ƙasashen uku suka kafa wata ƙungiya tasu ta bai ɗaya mai suna AES, ko ASS a takaice, wato haɗakar ƙasashe ƙawaye na Sahel, kuma suka sanar da yin wani fasfo nasu shi ma na bai ɗaya wanda zai kasance ba da wata alama da ke alakantashi da ƙasashen kungiyar ECOWAS ko kuma CEDEAO ba.