Agwagi da kifaye da zinare da sauran kayan da Charles zai gada na Sarauniya

Asalin hoton, Getty Images
Sarauniyar da ta fi kowane mai mulki daɗewa a kan karagar Masarautar Birtaniya, Sarauniya Elizabeth ta II, ta yi fice kan irin matuƙar son rayuwa ƙawa da take da ita.
A matayinta na ɗaya daga cikin mata mafiya arziki a Birtaniya, ta gaji fada-fada, da kambin zinare da dama da kuma rukunin gidaje.
Tana kuma mallaki abubuwa na ƙayatarwa da dama, waɗanda a yanzu duk Sarki Charles ne zai gaje su.
Riguna
"Sarauniya da mahaifiyarta ba su damu da zama masu ƙirƙirar ado da kwalliya ba da za a dinga kwaikwayo ba. Wannan abu ne da mutane marasa abin yi sosai suka fi," a cewar wani mai tsara kayan ƙawa Sir Norman Hartnell, a wata hira da ya yi da jaridar New York Times a 1953.

Ya faɗi hakan ne a shekarar da aka yi nadin sarautar Sarauniya Elizabeth. Sai dai bayan wasu shekaru ta sauya tsarin shigarta har hakan ya zamar wa shugabanni mata da dama a fadin duniya abin kwatance.
Tana yawan sa takalmi coge mai tsayin inci biyu da siket wanda ya wuce gwiwarta da kaɗan da aka yi wa kalmasa.
Malafarta kan kasance ƴar daidai da ba ta rufe mata fuska. Da wahala a ga Sarauniya a wani taro na waje babu ɗankwali ko malafa a kanta, sai dai idan a cikin gida take.
Tana son launi mai haske - yawanci tsanwa ko ruwan ɗorawa. Suna mata kyau kuma sun sa takan zama wata ta daban tare da fito da kwarjinin mulkinta.
An yi amannar cewa Sarauniya ta fi son launin shudi, kuma tana yawan saka shuɗayen kaya idan za ta fita wata sabga ko kuma taron wasanni.
A yanzu da ta rasu, ba a san inda za a ajiye rigunanta ba. Ana yawan ganin kayan tsohuwar Sarauniya Victoria da fitattun mutanen masarautar irin su Diana Gimbiyar Wales a gidajen adana kayan tarihi da yawa.
Jakankunanta
Mai yiwuwa ne abin da ya fi yin fice a cikin kayanta ita ce jakar hannu.

Asalin hoton, Getty Images
Ko yaushe za a ganta ɗauke da jakar hannu kuma ko a hoton da ta ɗauka na ƙarshe a rayuwarta sai da aka gan ta da ita.
Wani kamfanin Birtaniya Launer ne yake yi mata jakankunanta, kuma an ce tana da kusan 200, waɗanda dukkansu suke da ɗan tsayin da za ta saƙale su a hannu don ta dinga samun damar yin musabaha da mutane sosai.
Gerald Bodme, mamallakin kamfanin Launer, ya ce Sarauniya "mutuniyar kirki ce mai kwarjini sosai".
"Ta sha gaya min a duk sanda na hadu da ita cewa ba ta taɓa jin cikar kwalliyarta idan dai har ba ta riƙe jaka ba," ya shaida wa BBC.
An daɗe ana yaɗa jita-jita kan ko me take saka wa a jakar. Ko yaushe dai akawai fan biyar da take bayarwa sadaka a coci duk ranar Lahadi, kamar yadda wasu masu sharhi suka ce, sannan akwai janbaki da madubi. Wasu kuma sun ce har ma da wayar salula don kiran jikokinta a duk sanda ta kama.

Asalin hoton, Getty Images
An kuma ce Sarauniya kan yi amfani da jakarta wajen aika saƙo ga ma'aikatanta. Alal misali, idan ta ajiye ta a kan tebur yayin da ake cin abincin dare, to a fakaice tana aika saƙon cewa tana so a kammala taron ne.
Agwagi da kifaye
A bisa doka, dukkan fararen agwagin da ba a san mai su ba a Ingila da Wales to na gidan sarauta ne - majalisar dokoki ta san da hakan daga Hukumar Kare Tsuntsaye ta Masarauta.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Duk shekara, ana yin ƙidayar agwagi na Kogin Thamnes da ke Landan, ana kiran ƙidayar da upping. Tun a ƙarni na 12 aka fara ƙidayar agwagi, a lokacin da masarautar ta ce dukkan agwagin da ke ruwa waɗanda babu mai su, mallakinta ne, don a tabbatar da ana samun isasshen namanta a lokutan taron gidan sarauta. "Sai dai a yau ba a cin naman agwagi, an bar su ne don kiyaye muhalli da amfani da su ta fannin ilimi," in ji babban mai kula da su, David Barber. Shi ne mai kula da agwagin a ƙarƙshin Sarauniya tsawon shekara 30, har zuwa lokacin mutuwarta. Sannan duk wani kifi da ke kilomita 4.8 daga gaɓar teku to mallakin masarautar ne. Tun shekarar 1324 aka amince da batun hakkin mallakar, a lokacin Edward II ne sarki. Dokar ta ce: "Sannan duk wani kifi da ke cikin gaɓar teku mallakin Sarki ne." Har yanzu ana amfani da kuma girmama dokar, don haka dukkan kifaye da agwagin mallakar masarauta ne. A yanzu mutuwar mahaifiyarsa ta sa sabon Sarki Charles ya gaji kifaye da agwagin masu yawa da ke ƙasar.
Dawakai
An sha bayar da labarin ƙaunar da Sarauniya take yi wa karnuka. An ce ta yi karnuka fiye da 30 a tsawon rayuwarta. Baya ga karnuka kuma, tana matuƙar son dawakai, don tana da su da yawa.

Asalin hoton, Getty Images
Sarauniya ta fara koyon hawa doki ne a kan wani doki mai suna Peggy da kakanta George na V ya ba ta a matsayin kyautar taya ta murnar cika shekara huɗu.
Daga baya ta gaji wani ingarman doki na masarutar, wanda ya dinga ciyo mata kyaututtuka ne tseren dawaki.
Wani mai horar da dawaki Sir Michael Stoute, wanda ya a ƙarƙashin aikinsa dawakan masarauta suka yi nasara har sau 100, ya ce ya ji dadin aiki da Sarauniya.
Sarauniyar kan sa wa dawakanta suna don a dinga bambance su - akwai irin su Duty Bound da Constitution da kuma Discretion.
"Wani ƙramin misali da zai nuna yadda ta san harkar dawaki sosai shi ne, ba ta taɓ fesa turare idan ta ziyarci barga don ganin dawakanta, saboda hakan na iya tayar wa matasan dawakan sha'awarsu," a cewar wani ɗan jarida Clare Balding, wanda kakansa da babansa da ɗan uwansa duk sun horar da dawakan Sarauniya. Sau biyar dawakan Sarauniya na ciyo mata gasar tseren dawaki ta Birtaniya.
Motoci
Idan harkokin da suka shafi aikinta za ta, Sarauniya ta fi amfani da keken doki da aka maƙala a jikin motarta ƙirar Bentley, da direba ke tuƙawa.

Asalin hoton, Getty Images
Amma a duk lokacin da za ta iya tuƙi, to ta fi son tuƙa Land Rovers. Tana matuƙar son tuƙa mota a tare da mijinta, Yarima Phillip. Ma'auratan suna son motoci ƙirar kamfanin Juguar da Land Rover - wani kamfanin Birtaniya mai alaƙa da wani kamfanin Indiya Tata. Kafin ta zama Sarauniya, Gimbiya Elizabeth ta yi aikin sa kai na tuƙa babbar mota da kuma aikin kanikanci a Yaƙin Duniya na biyu. A wasu lokutan takan yi amfani da gwanintarta da tuƙa mota ta nishaɗantar da baƙi. A watan Satumban 1998, Sarauniya ta gayyaci Yarima Mai Jiran Gado na Saudiyya Abdullah zuwa Fadar Balmoral don cin abincin rana. Bayan nan ta gayyace shi rangadi a wani rukunin gidaje mai faɗin eka 20,000. Wani tsohon jami'in diflomasiyya na Birtaniya Sherard Cowper-Coles, ya ce daga farko Abdullah ya ƙi yarda, amma daga baya sai ya amince ya shiga gidan baya. Ga mamakinsa, Sarauniya ta zauna a mazaunin direba ta hau babban titin Scotland, "kuma har suka sauka tana yi musu hira." Abdullah ya damu har ya nemi Sarauniya da ta ɗan rage wuta. Wannan abu ya faru ne tun kafin a bai wa mata damar tuƙa mota a Saudiyya. Kafafen yaɗa labaran Birtaniya sun yi ƙiyasin cewa jumullar kuɗin motocinta baki ɗaya zai kai dala miliyan 10, kuma a tsawon rayuwarta ta mallaki fiye da Land Rover 30.
Filaye
A jerin masu arziki na Jaridar Sunday Times an ƙiyasta cewa arzikin Sarauniya na ƙashin kanta zai kai dala miliyan 426. YAwanci sun samu ne daga ƙadarori da gwala-gwalai da tambari da zane-zane.

Asalin hoton, Getty Images
Sarauniya tana kuma da wasu gidaje na sarauta da kuma filaye masu yawa. Ba za a sayar da waɗannan rukunin gidaje ba. Kadarorin sun haɗa da na kan Titin London Regent da Filin Sukuwa na Berkshire Ascot.
Gadon iyali
Haka zalika Sarauniya Elizabeth ta gaji wasu abubuwa na ƙshin kanta daga magabatanta, da aka adana su a Ma'ajiyar Masarauta.

Asalin hoton, Getty Images
Sun haɗa da rigar auren Sarauniya Victoria. Sannan akwai kayan yaƙin sarauta da Henry VIII ya saka. Ya ƙi yarda da matsayar fafaroma inda ya ayyana Cocin Ingila a matsayin mai zaman kansa, ya kuma ce shi ne shugaban cocin. Haka shugabancin ya ci gaba da wanzuwa a kan waɗanda suka gaje shi.
Kayan ƙarau
Da yawanmu da zarar mun yi tunanin Iyalan gidan sarauta, abin da ke fara zuwa ranmu shi ne gwala-gwalai da daiman.

Asalin hoton, Getty Images
Mulkin mallakar masarautar Birtaniya shi ne mafi girma a tarihin ɗan adam, inda ya bai wa iyalan masarautar damar mallakar mafi girma da kyawu na zinare da gwal. Daiman mafi girma na duniya shi ne mai darajar karat 530.2 na Star of Africa. Da shi aka yanka aka yi kambin masarautar. Haka ma daiman mafi shahara na Koh-i-Noor da Birtaniya ta samu bayan da ta mamaye Punjab a 1849. Da farko Sarauniya Victoria ke amfani da shi kamar ɗan maɓalli. Daga baya aka saka shi a kambin Sarauniya Alexandra kana daga bisani aka saka shi a kambin naɗin sarautar Mahaifiyar Sarauniya a 1937. Baya ga kayan ƙarau na masarautar, Sarauniya Elizabeth na da gwala-gwalai na ƙshin kanta da dama da ma duwatsu masu daraja.

Asalin hoton, Getty Images
Sai dai an fi ganin Sarauniyar ne yawanci da ɗan kunneta na dutse mai daraja ɗan manne da sarƙarsa - wanda hakan ya zama kamar wani salon adonta na musamman.
Jana'iza
Ana tsammanin Sarauniya Elizabeth ta miƙa kusan dukkan kayan ƙarau ɗinta ga ɗanta, Sarki Charles. Amma wani ƙwarare kan harkar masarauta ya yi hasashen cewa za a binne ta da wasu setin sarƙarta biyu daga cikin abin da ta mallaka. Lisa Levinson, shugabar sadarwa ta Cibiyar Zinare, ta ce ta yi amanna setin da za a zaɓa ɗin za su kasance zinare ƙirar yankin Welsh na aurenta ne da kuma ƴan kunne biyu na dutse mai daraja.

Asalin hoton, Getty Images











