Macron ya zaɓi matashi ɗan shekaru 34 a matsayin firaiminista

Macron

Asalin hoton, LUDOVIC MARIN/AFP/POOL

An naɗa Gabriel Attal a matsayin sabon firaiministan Faransa, a ƙoƙarin shugaba Emmanuel Macron na farfado da gwamnatinsa.

Dan shekaru 34, ya zama mutum mafi karancin shekaru a tarihin Faransa da ya riƙe wannan mukamin.

Mista Attal ya maye gurbin Elisabeth Borne wadda ta yi murbus bayan watanni 20 a kan kujerar.

A tsawon lokacinta, ta yi fama da rashin rinjaye a majalisar dokokin ƙasar.

Gabriel Attal, wanda a yanzu haka shi ne ministan ilimin Faransa zai jagoranci gwamnati a yayin da ake shirin zaɓen ƴan majalisar dokokin Turai a cikin watan Yuni.

Ya kasance mutum na farko dan luwaɗi a bayyane da zai riƙe wannan muƙamin.

A zaɓen 2017 ne ya zama ɗan majalisar dokoki kuma ɗaya daga cikin ɗan ga-ni-kashe-nin Shugaba Macron.

A lokacin yana ɗan shekara 29, an ba shi muƙamin ƙaramin minista a ma'aikatar ilimi sannan a shekara ta 2020 ya zama kakakin gwamnati.

Bayan da shugaba Macron ya yi tazarce, sai aka naɗa shi ministan kasafin kuɗi kafin ya koma ministan Ilimi.