Tinubu ya yi gum kan batun albashi mafi ƙanƙanta

Asalin hoton, kano state Govt House
Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta aike da ƙudiri ga Majalisar Dokokin ƙasar wanda zai kunshi adadin abin da aka amince da shi ya zama albashi mafi ƙanƙanta ga ma'aikata a "matsayin wani ɓangare na "dokokinmu" a shekaru biyar ko ƙasa da haka masu zuwa.
Shugaban wanda ya faɗi hakan ne a yayin jawabinsa ga ƴan Najeriya albarkacin ranar dimukraɗiyya, ya ce lallai yana sane da halin matsin tattalin arzikin da 'yan najeriyar ke ciki. To sai dai ya nemi "yan ƙasar da su tallafa wajen cimma "dimukraɗiyyar da za ta tabbatar da cigaban tattalin arziki."
Ƴan Najeriya dai sun yi fatan jin ƙarin albashin da suka samu daga bakin shugaban nasu a jawabin nasa na safiyar Talata.
A ranar Litinin ne dai kwamitin mutum 37 da aka kafa kan albashin mafi ƙanƙanta ya miƙa rahotonsa bayan kwashe kimanin watanni biyar da kafa shi.
Wakilan gwamnatin tarayya da na masana'antu masu zaman kansu dai da ke kwamitin na shugaban ƙasa domin tattauna batun albashin sun amince da naira 62,000, inda su kuma wakilan ƙungiyoyin ƙwadago suka kafe a naira 250,000.
Batun tsadar rayuwa da na ƙarancin albashi ya sa ma'aikata a Najeriya rashin nuna sha'awarsu ga bikin ranar dimukraɗiyya na bana da ake yi a ƙasar.
Abubuwan da Tinubu ya faɗi a jawabinsa

Da farko dai shugaba Tinubu a jawabin nasa na yi jinjina ga jerin wasu mutane da ya ce su ne suka dasa harsashin ranar dimokradiyyar da yau ake bikinta, inda ya bayyana su da 'yan gwawarmayar zaɓen watan Yunin shekarar 1993. Ga jerin sunayen mutanen kamar haka:
- MKO Abiola wanda shi ne ɗan takarar zaɓen shugaban kasa a jam'iyyar SDP wanda kuma ake karramawa a yau.
- Kudirat Abiola
- Janar Shehu Musa 'Yar'adua
- Pa Alfred Rewane
- Anthony Enahoro
- Abraham Adesanya,
- Commodore Ɗan Suleiman,
- Arthur Nwanko
- Chukwuemeka Ezeife,
- Admiral Ndubuisi Kanu,
- Frank Korori
- Bola Ige
- Adekunle Ajasin
- Janar Alani Akinrinade
- Farfesa Bolaji Akinyemi
- Farfesa Wole Soyinka
- Ralph Obioha
Daga ƙarshe shugaba Tinubu ya yi bayani kan batutuwan da suka shafi tattalin arziƙi da 'yancin ɗan adam da siyasa da dai sauransu.
Mece ce ranar bikin dimukraɗiyya ta June 12?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Larabar nan, 12 ga watan Yuni ce ranar da yan Najeriya ke murnar zagayowar ranar Dimokuradiyya a kasar, da aka fi sani da June 12.
Wannan rana ce da tarihin kasar ba zai manta da ita ba saboda a ranar ne aka gudanar da zaben Najeriya na 1993, wanda ake kallo a matsayin mafi tsarki, ko da yake a zahiri ya bar baya da ƙura.
Tsohuwar gwamnatin ƙasar ta shugaba Muhammadu Buhari ce ta sauya ranar, daga 29 ga watan Mayu, ranar da aka fara gudanar da mulkin farar hula zuwa 12 ga watan Yuni, ranar da aka gudanar da zaben na 1993.
Albarkacin wannan rana gwamnati ta ayyana Larabar nan a matsayin ranar hutu, don gudanar da bukukuwa, kana shugaba Bola Ahmed Tinubu zai gabatar wa yan kasar jawabi na musamman.
Ana kyautata zaton cewar ɗan takarar jam'iyyar SDP, wato Moshood Olawale Abiola ne ya lashe zaɓen bayan da ya kayar da abokin takararsa na jam'iyyar NRC Bashir Othman Tofa.
An dai ki sanar da sakamakon zaben ne saboda soke zaben da gwamnatin mulkin soja a karkashin mulkin Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta yi.
Sai dai a bana ranar ta zagayo a lokacin da yan kasar da dama ke fama da matsaloli iri-iri, musamman na tsaro da tashin farashin kayan masarufi.
'Yan Najeriya na mantawa da wannan rana'
Mannir Dan-Ali, tsohon ma’aikacin BBC, kuma mai sharhi kan lamuran yau da kullum a Najeriyar, ya ce akwai takadama a kan wannan rana, inda wasu da dama ke mata kallon wani kokari da jama'ar yankin Yarbawa ke yi na fifita al'amuransu da kuma gwagwarmayar da suka yi.
''Masu rajin wannan rana bayan da suka kafa gwamnati tare da Buhari ne suka yi kokarin sauya ta zuwa ranar 12 ga watan Yuni, amma kwai mutane da dama da ke ganin cewa ranar da aka fara mulkin dimukradiyya karkashin farar hula, wato 29 ga watan Mayu ce ta fi dacewa a matsayin ranar Dimukradiyya'' in ji shi.
Ranar Dimukradiyya ta kara karfi ne zamanin tsohon shugaban ƙasar Muhamadu Buhari, wanda ya sauya ta zuwa 12 ga watan na Yuni.
An soma gudanar da bikin ranar Dimukradiyya a Najeriya ne tun shekarar 2002, haka kuma bayan da tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya hau mulki ya kuma ƙara wa ranar karfi bayan dawo da ita 12 ga watan Yuni.
To amma a cewar Mannir Ɗan Ali “Ga wasu daga cikin ƴan Najeriya da suke fama da tsadar rayuwa babu wani abu da dimokaradiyyar da ma mulkin farar hular suka tsinana musu, bare wannan rana ta June 12, domin ba abun da ke damunsu kenan ba''
Har yanzu dai yan Najeriya da dama na tafka muhawa game da matakin sauya ranar Dimokaradiyyar daga 29 ga watan Mayu zuwa 12 ga watan Yuni, inda wasu ke ganin cewa siyasa ce kawai a cikin lamarin, inji Dan Ali.










