Trump zai ƙera katafariyar garkuwar tsaron sararin samaniya a Amurka

Hoton Trump da katafariyar garkuwar samaniya

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

Shugaba Donald Trump ya bayyana taswirar sabuwar katafariyar garkuwar makamai masu linzami ta sama da Amurka za ta kera domin kare kanta.

Daman tun da farko ya sanar da aniyarsa ta kera garkuwar da ya kira ''Golden Dome'' lokacin da ya sake hawa mulkin kasar a farkon shekarar nan -2025, kuma ya ce za ta fara aiki ne kafin ya bar mulki a 2029.

Shugaba Trump ya ce rundunar da ke kare sararin samaniyar Amurka ce za ta kera katafariyar garkuwar wadda za ta lakume dala miliyan dubu 175.

Ya ce garkuwar za ta kunshi sabuwar fasahar da ta hada da abubuwan masu ankararwa kan duk wani hari da kuma tare makamai, domin kare kasar daga duk wani hari na sama daga sauran sassan duniya ko daga sararin samaniya.

Shugaban ya kara da cewa kasar Kanada ma ta nemi shiga cikin aikin kera garkuwar, wadda aka yi tunanin samar da ita daga irin ta Isra'ila, wadda Isra'ilar ke amfani da ita wajen kare kanta daga makaman roka tun 2011.

Daman bayan 'yan kwanaki da komawarsa Fadar Mulkin Kasar – White House, a watan Janairu, ya bayyana aniyarsa ta kera garkuwar da nufin kare duk wata barazanar hari da makamai na zamani ta sama da za a iya kai wa Amurka.

An ware wa aikin jumullar dala miliyan dubu 25 a kashin farko a sabon kasafin kudin kasar – kodayake gwamnatin Amurkar ta yi kiyasin zuwa karshe aikin zai iya cin sama da hakan ma sosai a gomman shekaru masu zuwa.

Jami'ai sun yi gargadin cewa garkuwar da kasar ke da ita a yanzu ba za ta iya kare kasar daga sababbin makamai na zamani da abokan gabar Amurkar ke kerawa ba a yanzu.

Shugaba Trump ya kuma ce Janar Michael Guetlein na rundunar kare sarari samaniyar kasar shi ne zai shugabanci aikin.

Janar Guetlein dai a yanzu shi ne mataimakin shugaban rundunar kare kasar ta samaniya.

Kwana bakwai da kama mulkinsa, Trump ya bayar da umarni ga ma'aikatar tsaro ta kasar da ta mika bayanan shirin samar da garkuwar – wadda zam a gargadi da kuma kariya ga duk wasu hare-hare na sama – abin da gwamnatin Amurkar ta ce ita ce ke zaman babbar barazana da ke fuskantar Amurka a yanzu da ma gaba.

Da yake magana a ofishinsa a ranar Talata, ya ce, garkuwar za ta kunshi fasahohi na zamanin da ke tafe a fannin kasa da ruwa da kuma sararin samaniya.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A lokacin da ya ziyarci Washington a farkon shekarar nan, ministan tsaro na kasar Kanada a lokacin, Bill Blair ya nuna cewa kasarsa na da sha'awar shiga aikin samar da garkuwar – yana mai cewa tunain hakan yana da alfanu sosai kuma aikin ya dace da muradin kasarsa.

Ya kara da cewa ya dace Kanada ta sana bin da ke wakana a yankin kuma ya kasance tana sane da duk wata barazana da yankin zai fuskanta, ciki har da yankin Arctic.

Trump ya kara da cewa garkuwar za ta kasance tana iya tarewa da kama makamai masu linzami da za a harbo daga wani sashe na duniya ko kuma wanda za a harbo daga sararin samaniya.

Garkuwar irin wadda Isra'ila take amfani da ita tun 2011, za ta ninninka ta Isra'ilar girma, za kuma ta fi ta zama ta zamani da girman aiki – inda ko da makami mai gudu kamar walkiya, da ya fi sauti da haske gudu za ta iya kawar da shi, in ji Trump.

Kuma ya ce akwai yuwuwar cimma nasara dari bisa dari ta kerawa da kuma aikin wannan garkuwa.

A baya jami'an Amurka sun ce garkuwar za ta kasance ne da fasahar da za ta iya kare Amurka daga duk wani mataki na makamin da aka harbo mata – kama daga lokacin da aka yi niyyar harba makami da kuma lokacin da aka riga aka harbo mata makamin yake sama – duk garkuwar za ta iya kawar da barazanar.

Ofishin kasafin kudi na majalisar dokokin kasar, ya yi kiyasin cewa a karshe kudin da gwamnati za ta iya kashewa a aikin zai iya kai wa dala miliyan dubu 542 a tsawon shekara 20 a bangaren kayayyakin garkuwar na sama kadai.

Tun da dadewa jami'an hedikwatar tsaron Amurka sun yi gargadin cewa, garkuwar da kasar take da ita a yanzu, ko kadan ba tsarar sababbin makamai masu fasahohi na zamani da Rasha da Amurka ke da su ba.

Jami'an sun yi gargadin cewa, wadannan manyan kasashen biyu – Rasha da China na kera makamansu ne ta hanyar nazarin fannonin da Amurkar ke da gibi ko gazawa a tsaronta.