Yadda jirgin yaƙin Rasha da na Amurka suka yi arangama a sararin samaniya

Jirgi maras matuƙi

Asalin hoton, EPA

Wani jirgin yaƙin Rasha ya yi arangama da jirgi maras matuƙi mallakin Amurka, lamarin da ya sanya jirgin na Amurka ya faɗa cikin teku.

Wannan dai wata manuniya ce kan yadda lamurra ke ƙara tsami tsakanin Amurka da Rasha tun bayan da Rasha ta ƙaddamar da kutse a Ukraine.

Amurka ta ce jirgin nata maras matuƙi na shawagi ne kamar yadda ya saba a sararin samaniya na ƙasa-da-ƙasa, inda a lokacin wasu jiragen yaƙi na Rasha suka yi ƙoƙarin kaɓo shi.

Rasha ta ce jirgin na Amurka ya faɗa teku ne lokacin da ya yi ƙoƙarin kauce wa jiragen na Rasha, amma a cewar ta ba a samu karo ba a taho-mu-gama ba tsakanin su.

Kuma ma’aikatar tsaron Rasha ta ce jirgin maras matuƙi na tafiya ne yayin da na’urar da ke sanyawa a iya gano inda yake take a kashe.

Lamarin dai ya faru ne a ranar Talata, kamar yadda dakarun Amurka suka tabbatar.

Wata sanarwa da rundunar sojin Amurka ta fitar ta ce “Jirgin MQ-9 na gudanar da shawaginsa ne kamar yadda ya saba a sararin samaniya na ƙasa-da-ƙasa, inda wani jirgin Rasha ya tunkaro shi, wani abu da ya sanya aka samu karo, lamarin ya sanya jirgin na MQ-9 ya salwanta.”

Sanarwar ta ƙara da cewa kafin karon ya faru, jirgin yaƙin na Rasha Su-27, ya rinƙa zubar da mai a kan jirgin Amurkar maras matuƙi.

Tuni dai Amurka ta gayyaci jakadan Rasha a Washington, Anatoly Antonov domin yin bayani, a wani mataƙi na nuna takaici kan abin da ya faru.

Bayan kammala ganawar, kafofin yaɗa labarun Rasha sun ambato Antonov na cewa lamarin wani tsokanar faɗa ne daga Amurka.