China ta ba Amurka zaɓi na zaman lafiya ko zaman gaba tsakaninsu

Asalin hoton, Reuters
Ministan harkokin wajen China, Wang Yi ya ce alaka tsakanin kasarsa da Amurka ta fara daidaituwa a ‘yan watannin nan, amma kuma wasu abubuwa da ke haifar da sabani tsakaninsu na karuwa.
Mista Wang ya ce zabi ne tsakanin hada kai na kasa da kasa ko kuma gaba da za ta iya kaiwa ga rikici.
Ministan harkokin wajen na China na magana ne a yayin bude tattaunawar da suke yi da takwaransa na Amurka Antony Blinken, a Beijin, a ziyarar da Mista Blinken ke yi a Chinar.
Mista Wang, wanda ya ce dangantaka wadda take tamkar ta doya ta manja tsakanin manyan kasashen biyu, ta fara daidaituwa a watannin nan, amma kuma wasu abubuwa da ke kara haddasa sabani a tsakaninsu na ci gaba da karuwa.
A don haka ya ce zabi ya rage na ko dai su hada kai a tsakanininsu ko kuma a ci gaba da gaba da fito da fito da ka iya kaiwa ga dauki-ba-dadi.
Ya ce, ''a gaba daya, alakar China da Amurka ta fara daidaita. A fannonin, bangarorinmu biyu tattaunawa ta karu, hada kai da kuma bangaren dangantakar mai kyau. Wannan abu ne da mutanen mu biyu da kuma duniya suka yi maraba da shi. To amma kuma a dai wannan lokaci, abubuwan da ke haddasa sabani a dangantakat na ci gaba da karuwa da habaka.’’
Ministan wajen na China ya kara da gargadin Amurka da kada ta kuskura ta keta haddin iyakar China.
Shi kuwa a nasa bangaren Sakataren harkokin wajen na Amurka Antony Blinken cewa ya yi abu ne mai muhimancin gaske ga kasashen biyu su tattauna bambance-bambancen da ke tsakaninsu domin kaucewa rashin fahimtar sjuna da kuma samun sabani;
''Nan gaba a kan abubuwan da shugabanninmu suka tsara, akwai bukatar diflomasiyya ta sosai, babu zabin da ya fi matsayarmu a kan diflomasiyya ta keke da keke domin ci gaba, amma kuma mu tabbatar mun fayyace komai yadda ya kamata,a kan fannonin da muke da bambance-bambance, domin kauce wa sabanin fahimta domin kaucewa kuskure.’’
Manyan kasashen biyu da suka fi karfi a fannin tattalin arziki da kuma soji a duniya sun rabu a kan batutuwa da dama – kama daga harkokin kasuwanci da fasaha har zuwa ga yakin Ukraine.











