Illoli shida da ke tattare da shan tabar vape da matasa ke rububinta

Asalin hoton, Getty Images
Rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya kan adadin mutanen da suka jarabtu da shan sigari ta zamani na ci gaba da ɗaukar hankalin jama'a.
Cikin rahoton da ta fitar a farkon wannan mako WHO ta ce ta ce aƙalla mutum miliyan 100, ciki har da ƙananan yara miliyan 15 ne suka yi tsananin sabo ko jarabtuwa da shan taba sigari ta zamani da ake kira da vape.
Wani abu da ya fi ɗaukar hankali cikin rahoton shi ne gargaɗin da WHO ɗin ta yi cewa zuƙar tabar ta zamani na da matsala, "saboda ana tallata su ne da cewa ba su da illa sosai, amma a zahiri, suna jefa matasa da ƙananan yara cikin ta'ammali da sinadarin nicotine da ke cikin sigari ne."
Shugaban hukumar lafiyar, Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus ya zargi kamfanonin sigari da yunƙurin jefa ƙananan yara cikin shan sigari ta hanyar zamanantar da shanta.
WHO ta ce wannan sabon salo zai ɓata ƙoƙarin da aka yi gomman shekaru ana yi wajen yaƙi da shan sinadarin nicotine.
Hukumomin lafiya a matakai daban-daban sun jima suna gargadi game da shan taba sigari tare da fito da illolin da take yi wa lafiya da gangar jiki, to sai dai mutane da dama sun ɗauka cewa shan sigarin ta zamani, wato vape' ba ta da illa kamar sigar taba sigari.
'Na fi jin daɗin sigari fiye da vape'

Asalin hoton, Getty Images
Wani matashi da ke shan duka nau'ikan tabar biyu da BBC ta zanta da shi ya ce ya fi ji daɗin taba sigari a maimakon vape.
Ya ce ya zaɓi taba sigari ne saboda ta fi ba shi gamsuwa fiye da vape.
''Amma wataƙila na fison sigari ne saboda ni ba mai yawan son ɗanɗano ba ne, ita kuwa vape tana da ɗanɗano'', in ji shi
Wani dalilin kuma da ya sa ya fi son sigari fiye da vape shi ne shi vape sai an karo mata sinadarin a duk lokacin da ya ƙare, sannan sai ka je wuri na daban.
''Saɓanin sigari, wadda ita kuma a duk lokacin da kake so za ka sha, kuma a ko'ina'', in ji matashin da ke shan duka nau'ikan tabar biyu.
Dangane da yawan kuɗin da ake kashewa a shan duka nau'ikan tabar, matashin ya ce kudin kusan ɗaya ne.
Mene ne bambanci nau'ikan sigarin biyu?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dokta Abdullahi Kabir Sulaiman da Dokta Auwalu Fatihu Abubukar ƙwararrun likitocin ƙwaƙwalwa da iyali ne a Asibitin Mallam Aminu Kano da ke jihar Kano, sun kuma zayyano wasu bambance-bambance da ke tsakanin taba sigari da kuma tabar vape.
- Hanyar shansu:
Dokta Auwalu Fatihu Abubukar ya ce taba sigari da aka jima ana amfani da ita, kunna ta ake yi da wuta sai a riƙa zuƙa, yayin da ita kuma vape ana amfani da na'urar lantarki ne wajen shanta.
''Sannan ita taba sigari ganyen tabako ne ake kunna wa wuta domin a zuƙa, ita kuma vape ganyen ne ake mayar da shi sinadari na ruwa-ruwa domin a zuƙe ta'', in ji Dokta Abdullahi kabir Sulaiman.
- Adadin sinadarin nicotine:
Dokta Auwal ya ce adadin sinadarin nicotine da ke cikin tabar vape ya zarta wanda ke cikin taba sigari yawa, don haka ne ma ya ce ta fi illa ga ƙwaƙwalwa fiye da taba sigari.
- Sauran sinadarai
Haka kuma Dokta Auwalu ya ce tabar vape na ɗauke da wasu sinadarai masu illa ga lafiyar jiki, fiye da taba sigari.
''tana dauke da sinadarin glaserin da flavour, wadda ita kuma taba sigari ba ta da shi'', in ji shi.
- Hayaƙi da tiriri
Masanin lafiyar ya ce masu shan tabar sigari hayaƙi shuke zuka, yayin da su kuma masu shan tabar vape tiriri suke zuƙa.
''Don haka a nan ita taba sigari ta fi illa saboda hayaƙin, tunda bayan sinadarin nicotine da take dauke da shi tana kuma ɗauke da wasu'', in ji shi.
Mene ne illolin tabar vape?

Asalin hoton, Getty Images
Likitan ƙwaƙwalwar ya ce tabar vape na ɗauke da wasu ilolo masu tarin yawa da take yi wa lafiyar masu shanta, waɗanda suka haɗa da:
Tana haifar da cutar kansa
Dokta Abdullahi ya ce shan tabar vape ka iya haifar da cutar kansa a bangarori da dama na jikin ɗan adam, saboda tiririn tabar da ake shaƙa.
''Su waɗannan sinadaran ruwan da ke cikinta, waɗanda ake ɗigawa a ciki suna janyo cutar kansar huhu da kansar ƙwaƙwalwa hanta da kuma kansar zuciya'', kamar yadda ya bayyana wa BBC.
Bugun zuciya
Likitan ƙwaƙwalwar ya kuma ce sinadaran da ke cikin tabar vape na janyo matsalar bugun zuciya.
''Wannan kuma matsala ce da ke iya haifar da cutar hawan jini da sauran cutukan da suka shafi zuciya'', in ji shi.
Ɗaukar hankalin yara da matasa
likitan ya ce daya daga cikin illolin tabar vape shi ne yadda take ɗaukar hankalin kananan yara da matasa.
"Galibi yara sun fi rububinta, kuma matsalar ita ce ƙwaƙwalwarsu ba ta gama nuna ba, to kuma suna danna mata sinadarin nicotine, wadda ke janyo musu jarabtuwa da ƙwaya'', in ji shi.
Zubewar ciki ko haihuwar jarirai da matsala
Dokta Auwalu ya ce shan tabar vape ga mata masu juna biyu na haifar d amatsalar zubewar ciki ko kuma zubar da jini.
''A wasu lokutan ma idan matsalar ta yi yawa, koda a yi barin ciinba, akan iya haifar jariran da wasu lalurori'', in ji shi.
Lalata ƙwaƙwalwar yara
Masanin kiwon lafiyar ya kum ace tabar vape na haifar da matsalar cutukan da suka shafi ƙwaƙwalwa.
''Ita kanta jarabtuwa da shan vape din matslaa ce ta ƙwaƙwalwa, ka ji ba za ka iya rayuwa ba sai ka sha wani abu, ai jaraba ce'', in ji shi.
Buɗe ƙofar shaye-shaye
Dokta Auwal ya ce shan tabar vape na iya zama a matsayin buɗe wa kai ƙofar fara shaye-shaye.
''Duyk wanda ke shan vape, to idan bai samu ba ya samu taba sigari zai sha, daga nan kuma duk wani nau'in shaye-shaye ma zai iya yi, da allurorin da za su ba shi maye, tun da yana neman abin da zai ɗauke masa hankali'', in ji shi.
Me ke janyo jarabtuwa da shan vape?

Asalin hoton, Getty Images
Dokta Auwal ya ce galibi abin da ke janyo mutum ya fara shan vape shi ne tasirin abokai.
''Yaro ne tana tare da abokansa kowanensu yana sha, to sai ya ga idan bai sha ba kamar shi e kawai bai waye ba cikin abokansa'', in ji shi.
To kuma da zarar mutum ya fara sha sai jikinsa ya dauka, har ya kai matsayin da idan bai sha ba ya jin daɗin jikinsa, a cewar likitan
Hanyoyin da za ku bi don raba yaranku da shan vape
- Yawaita yi musu nasiha tare da nusar da su illar shan taba
- Raba su da abokai masu sha
- Zama da abokan da ba sa sha










