Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mene ne mataki na gaba a Gaza bayan sakin waɗanda ake garkuwa da su?
- Marubuci, Tom Bennett
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Jerusalem
- Lokacin karatu: Minti 3
Rundunar sojin Isra'ila ta ce Hamas ta miƙa mata dukkan ƴan ƙasarta da suke raye da ke hannunta domin musayarsu da fursunoni ƴan Falasɗinu a cikin zangon farko na aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da Donald Trump ya jagoranta.
A ranar Juma'a ne yarjejeniyar ta fara aiki, lamarin da ya sa aka fara shigar da kayan agaji zuwa zirin a ƙarshen mako.
Da zarar an kammala aiwatar da zangon farko, za a shiga tattaunawa kan zango na biyu.
Ga wasu abubuwan da muka sani
Su wane ne Isra'ilawan da Hamas ta saka?
A cikin yarjejeniyar dai Hamas za ta saki dukkan Isra'ilawa 48 da suke garkuwa da su kimanin shekara biyu, ciki har da guda 20 da suke raye.
Mutum ɗaya ne kawai ba ya cikin mutum 251 da Hamas ta yi garkuwa da su a harin na ranar 7a ga Oktoban 2023, harin da ya yi ajalin kusan mutum 1,200. Isra'ila ta mayar da martani da luguden wuta, inda ta kashe sama da mutum 67,000 kamar yadda ma'aikatar lafiyar Hamas ta bayyana.
A yau Litinin ne dai Hamas ta miƙa mutum 20 ga ƙungiyar agaji ta International Committee of the Red Cross (ICRC).
Hukumomin Isra'ila sun ce da farko an miƙa Eitan Mor da Gali Berman da Ziv Berman da Omri Miran da Alon Ohel da Guy Gilboa-Dalal da Matan Angrest.
Sai kuma daga baya aka sako Bar Kupershtein da Evyatar David da Yosef-Chaim Ohana a Segev Kalfon da Avinatan Or da Elkana Bohbot da Maxim Herkin da Nimrod Cohen da Matan Zangauker da David Cunio da Eitan Horn da Rom Braslabski da Ariel Cunio.
Sai dai har yanzu ba a ƙarƙare magana ba a kan waɗanda suka mutu a lokacin da suke hannun Hamas ɗin.
Hamas ta mayar da gawarwakin mutum huɗu a ranar Litinin - Guy Illouz da Yossi Sharabi da Bipin Joshi da kuma Daniel Peretz.
"Muna so Hamas ta tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar nan," in ji kakakin gwamnatin Isra'ila, sannan ya ƙara da cewa sojojin ƙasar "ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba har sai sun tabbatar an mayar da dukkan gawarwakin domin ƴanuwanu su musu sutura a Isra'ila."
Wani jami'in gwamnatin Isra'ila ya ce za a kafa kwamitin haɗin gwiwa na ƙasashen duniya domin bincike tare da zaƙulo gawarwakin waɗanda ba su koma ba.
Falasɗinawan da aka saka
Isra'ila ta ce ta saki Falasɗinawa 250 da aka yanke wa hukuncin ɗaurin rai da rai da kuma ƴan Gaza 1,718 da ƙananan yara 15.
Sai dai daga cikikn waɗanda aka saka ba a ga wasu manyan waɗanda ake zargi da kai hari a Isra'ila ba, kamar Marwan Barghouti da Ahmad Saadat - waɗanda Hamas ta nemi a saka.
Isra'ila ta ce kusan mutum 100 cikin 250 za a sake su ne a Gaɓar Yamma, sai 15 da aka tura su Gabashin Jerusalem da kuma 135 da aka mayar Zirin Gaza ko wani wajen daban.
Me zai faru a gaba?
Tuni dai sojojin Isra'ila suka fara janyewa bayan kasancewa suna da iko kan kusan kashi 53 na Gaza.
Dakarun sojoji kusan 200 da Amurka za ta jagoranta ne za su sa ido kan tsagaita wutar, wanda ake tunanin zai ƙunshi dakarun Masar da Qatar da Turkiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
Da zarar kowane ɓangare ya amince da tsare-tsaren guda 20, shi ke nan yaƙin ya zo ƙarshe.
Daga cikin akwai hawa harkokin ƴanbindiga a Gaza, sannan za a kafa kwamitin mulkin Gaza wanda zai yi mulki a ƙarƙashin kulawar kwamitin amintattu ƙarƙashin Trump da ma tsohon Firaministan Birtaniya Tony Blair, kafin daga bisani a miƙa mulkin da gwamnatin Falasɗinu.
Amma an ce Hamas wadda ta mulki yankin tun daga shekarar 2007 ba za ta sa hannu a mulkin zirin ba, kamar yadda tsarin ya nuna.
Za kuma a yi afuwa ga ƴan Hamas ɗin idan suka miƙa wuya, ko kuma a ba su damar ficewa zuwa ƙasashen da suke so.
Muhimman abubuwa
A cikin yarjejeniyar akwai wasu abubuwa da ake tunanin akwai taƙaddama da suke buƙatar ƙarin bayani sosai.
A baya dai Hama ta ƙi amincewa da ajiye makami, inda ta ce ba za ta ajiye makami ba har sai an tabbatar da ƙasar Falasɗinu ƴantacciya.
Duk da cewa Isra'ila ta amince da tsare-tsaren Trump, Firaministan Isra'ila Benjaminn Netanyahu na nanata cewa ba ya so Hamas ta kasance cikin masu ruwa da tsaki a mulkin Gaza.
Wani batun shi ne batun janyewar sojojin Isra'ila daga Gaza, Isra'ila ta ce za ta janyewa amma za ta ci gaba da riƙe iko da kusan kashi 53 na Gaza, amma a cikin tsarin na Trump, kashi 40 za ta ci gaba da iko da ita, daga baya ta sake janyewa ya koma kashi 15.