Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko matasa na samun abubuwan da suke so a biranen Najeriya?
Lokacin karatu: Minti 1
Akan gudanar da Ranar Kula da Birane ta Duniya duk 31 ga watan Oktoba.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta sanya taken ranar na wannan sheara a matsayin "jagorancin matasa game da yanayi".
Albarkacin wannan rana, BBC ta tattauna da matasa a Najeriya domin jin ko suna samun abubuwan da suke buƙata a biranen ƙasar.