Nijar ta yi wawan kamun kayan maye a kan iyakarta da Najeriya da Benin

Smuggled drugs

Asalin hoton, Niger Gaya Prefet

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun bayyana damuwa kan ƙaruwar fasa-ƙwaurin miyagun ƙwayoyi a tsakanin iyakar ƙasar da Najeriya da kuma Jamhuriyar Benin.

Hakan na zuwa ne bayan da aka kama ɗaruruwan ɗauri na tabar wiwi da wata ƙwaya nau'in baliyam mai hatsari, da aka yi yunƙurin shigarwa ƙasar a ranar Juma'a daga wata ƙasa mai maƙwabtaka.

Shugaban gundumar Gaya a cikin jihar Dosso, kudu maso yammacin Nijar, Ashimu Abarshi ne ya yi wa BBC ƙarin bayani game da kama miyagun ƙwayoyi na baya-bayan nan.

Ya ce ƙwayoyin da suka kama sun haɗar da tabar wiwi ɗauri 400 da kuma ɗauri 1,260 na wata ƙwaya mai suna Diezepam, da kuma ƙarin ɗauri biyar na ganyen wiwi, da aka yiwo fasa-ƙwaurinsu a cikin kwale-kwale ta Kogin Isa.

Jami'in ya ce a baya-bayan nan, ga alama masu fasa-ƙwaurin ƙwayoyi sun ƙara ƙaimi inda suke amfani da hanyoyin sufuri wajen safarar ƙwayar ta cikin Jamhuriyar Nijar.

Ashimu Abarshi bai bayyana ƙasar da suke hasashen za a shigar da ƙwayar daga Nijar ba, amma ya tabbatar da cewa ana fiton kayan laifin ne a tsakanin Jamhuriyar Benin da Nijar da kuma Najeriya.

"Wanga babban kamu, an yi shi ne bakin ruwa. Jami'an kwastam na ruwa sun zagaya da dare....ƙarfe 10:30 na dare, sai suka ci karo da wani kwale-kwale ya ƙetaro ruwa, ya fito daga wata ƙasa ta maƙwabta", in ji shi.

Ya ƙara da cewa jami'an sun hangi wasu matasa biyu, da suka tsere bayan ganin jami'an hana fasa-ƙwaurin, inda suka zubar da kayan da ake ƙoƙarin yin safararsu.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Shugaban gundumar Gaya, mai nisan kilomita 254 daga Niamey babban birnin Nijar a gaɓar Kogin Isa ko Kwara, ya ce masu safarar ƙwayoyin na amfani da hanyoyin ruwa ne ko motocin bas-bas masu doguwar tafiya, haka kuma suna bin dazuka a kan babura.

"A 'yan kwanakin ga biyu, safarar miyagun ƙwayoyi ta zama ruwan dare gama duniya a nan gundumarmu ta Gaya. Abin da ya kamata a gane, shi ne muna da iyaka da ƙasa biyu na maƙwabta.

Daga yamma muna da iyaka da Jamhuriyar Benin, daga kudu maso gabas, Jamhuriyar Najeriya".

A cewarsa, ana safarar ƙwayoyin ne daga ƙasashen masu maƙwabtaka da Nijar, don yin fito zuwa wata ƙasa a cikinsu ko kuma a wasu ƙasashen na daban.

"Ka san waɗannan ƙwayoyi ana ɗauko su ne, ta wasu ƙasashe na Yammacin Afirka, kuma tilas inda za a wucewa da su, sai an biyo ta nan".

"In ana so a tai ƙasar Najeriya da su dole sai an biyo ta Gaya. In ana a shigo nan Nijer a yi wasu ƙasashe maƙwabta (da su), dole sai an biyo ta Gaya," in ji Ashimu.

smuggled drugs

Asalin hoton, Niger Gaya Prefet

Bayanan hoto, Dazafam (Diazepam) ƙwaya ce dangin baliyam da wasu ke sha a matsayin kayan maye
Smuggled drugs

Asalin hoton, Niger Gaya Prefet

Bayanan hoto, Wani ɓangare na manyan ɗauri-ɗauri na kayan mayen da aka kama kwanan baya a Gaya

Ya ce a wasu lokuta akan ƙetare ƙasashe guda biyu ko uku da irin waɗannan kayan maye, amma idan aka shiga Nijar da su, sai jami'an ƙasar sun kama.

Ashimu Abarshi ya ce a wannan karo, jami'an tsaron Nijar ba su kama masu fasa-ƙwaurin ba, don kuwa da ganin kwastam sai suka gudu, suka tsere.

Sai dai daga farkon shekara ta 2023 zuwa yanzu, jami'an tsaro a yankin Gaya sun kama mutum 46, bisa zargin fataucin ƙwaya.

'Sai an ƙara tashi tsaye a Afirka ta Yamma'

Ashimu Abarshi ya ce cikin waɗanda suka kama bisa zargin fataucin ƙwayoyi har da wasu daga Jamhuriyar Nijar da Najeriya da Benin da 'yan Mali da kuma Jamhuriyar Togo.

Jami'in ya yi zargin cewa irin wannan fataucin ƙwayoyi mai yiwuwa ne akwai hannun wasu manyan gungun masu fasa-ƙwaurin kayan maye da ke aika ƙwayar daga wannan ƙasa zuwa wata ta hanyar wasu 'sojojin haya' da ke yi musu fito.

“Ka san su, yawanci kamar ‘yan Nijar wa’yanda muke cafkewa da wannan kaya, kamar suna sufurinsu ne,” in ji shugaban na Gaya.

Ya ce maganin irin wannan annoba, sai kowa ya tashi tsaye. “In ya zamto mu jami’an tsaronmu ne kawai ke yaƙi, ba lallai a ci nasara ba”.

Wacce ƙwaya ce dazafam?

Wata ƙwayar magani ce dangin baliyam, wadda likitoci ke rubuta wa masu fama da cutukan rashin barci da masu ƙauracewa shan barasa.

Sai dai a cewar, Abubakar Idris Ahmad, kwamandan hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya reshen jihar Kano, a bayan fage mutane suna shan ta, don yin maye.

Ya ce masu sha a matsayin kayan maye, sukan ce tana da ɗan kashe jiki da sanya tunani da sanyi rai. "Duk dai shiririta irin ta matasa.

Amma gaskiya, ƙwaya ce da masu shan maye suka fara amfani da ita".

Ƙwaya ce mai matuƙar hatsari, in ji kwamandan na NDLEA, saboda idan mai sha ya jarabtu, to zai kasance sai ya sha, kafin ya iya barci, alal misali.

Haka zalika, ƙwayar tana iya yin illa ga lakar ɗan'adam, idan mai sha ya yi zurfi.

Sannan takan iya shafar har ƙwaƙwalwa, in ji shi.

"Takan birkita yanayin yadda ƙwaƙwalwa take aiki," Abubakar Idris ya bayyana. Kuma tana iya birkita yanayin rayuwa gaba ɗaya, ta yadda matuƙar wanda ya jarrabu da shan dazafam, bai sha ba, to babu abin da zai iya yi.