Dalilai huɗu da suka haifar da wahalar man fetur a Najeriya

    • Marubuci, Yusuf Tijjani
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC
    • Aiko rahoto daga, Abuja

'Yan Najeriya na cikin damuwar matsalar manfetur, wadda tun shekaru suke fama da tsadarsa, amma yanzu ƙarancinsa ya ƙara ta'azzara lamarin.

A gidajen man gwamnati ana sayar da man ƙasa da naira 620, amma a wasu jihohin irin su Sokoto da Kano da Jigawa ana sayar da man har sama da naira 1000, kamar yadda BBC ta tabbatar.

A yadda mutanen ƙasar suka riƙa tsammani a baya, idan aka ƙara farashin man, za a same shi a wadace a kowanne gidan mai.

Sai dai wannan tunani ya saɓa da tunanin mutane. Domin kuwa ana fama da tsadar man kuma ga ƙarancinsa da ya dabaibaye ko'ina.

Shin waɗanne dalilai ne suka janyo tsadar, ta ya ya za'a iya magance wannan matsala? wasu daga cikin tambayoyin da BBC ta yi wa Bashir Ahmad Danmalan kenan shugaban ƙungiyar dillalan man fetur da Iskar Gas ta Najeriya.

Ya zayyana dalilai kamar haka:

Ƙarancin ƙananan jiragen dakon mai

Idan babban jirgin da yake kawo mai daga ƙasashen ƙetare ya isa gaɓar teku, yawanci ba ya samun damar da yake iya isa tasoshin gefen ruwa da ake iya sauke man a defo-defo na manyan dillalai.

Hakan yasa ake amfani da ƙananan jiragen dakon mai da suke iya kai man iyakokin defo kamar na su Bonny Terminal da ke Fatakwal da Escravos Termina da ke Delta da dai sauransu.

"Abin da ya haifar da ƙarancinsu abubuwa ne guda uku, Ɗangote yana buƙatarsu, sannan ga na kamfanin Total da Burtaniya idan suka zo da kayansu, kansu suke wa aiki ba sa yi wa kowa.

"A gefe guda kuma siyasar duniya da ta shafi rikicin Rasha ta sanya babu mai amfani da jiragen ƙasar Rasha, gudun kada a dakatar da kai daga aiki, sakamakon takunkuman da aka sanya wa Rashan," in ji Bashin DanMaalan.

Ya ce idan ka sake ka ɗauki mai a hannun jiragen Rasha to daga ranar na Turai sun daina baka kaya.

"Ko da jirginka ne na kanka, masu iko da shi na Landan ko ƙasashen Turai, idan kana mu'amala da Rasha za su sa a daina mu'amala da kai, a mayar da kai saniyar ware.

Waɗannan na cikin dalilan da suke haifar da ƙarancin samun man da za a yi dakonsa.

'Ƙarin kuɗin ruwa'

An samun ƙari a kuɗin ruwan da ake karɓa a hannun waɗanda suka ranci kuɗi a bankuna, bayan da a watan Fabrairun CBN ya ƙara shi zuwa kashi 24.75 daga kashi 22.75.

Masu gidajen mai da basu da jari da waɗanda jarinsu bai kai ba suna zuwa su ranci kuɗi daga bankunan su sayi mai su sayar su samu riba.

"To wannan kuɗin ruwan na kashi 24.75 na gwamnati ne, amma idan ka yi huldar kudi bankuna suma na kasuwanci ne sai sun nemi riba suma. Hakan ya sa kuɗin ruwan yake kai wa kashi 40 cikin ɗari.

"Idan ƙa hada da naira 60 da kuma kashi 40 da ake da shi za ka ga an samu ƙarin kudi da suka kai naira 100 wadanda kan masu saya man za su koma ɗaiɗaiku," in ji Bashir Danmalan.

'An ƙure mai saya da mai sayar da kayan'

Bashir ƊanMalan ya ce ƙarancin jigilar man ta janyo tsadarsa, kuma wahalhalun da ake yi a kansa sun ƙaru.

"Mutum zai sanya kusan naira miliyan 30 da sayi man da ba zai ci naira miliyan daya ba a cikinsa," in Dan Malan.

Ya ce wannan dalilin ya tilastawa wasu da dama hakura da wannan kasuwanci, domin kuwa a ƙarshe za ka ga aiki suke yi ba tare da samun wata ribar a zo a gani ba.

A cewarsa da mai kuɗin zai sanya miliyan 30 ɗin a wani kasuwanci da zai iya samun ribar da ta zarce wadda yake samu a wannan kasuwanci.

Ta ɓangaren mai saya kuwa abin ba a cewa komai, motar da a baya naira dubu 10 ke cika tankinta a yanzu naira dubu 30 ko sama da haka ne ke cika ta.

"Wannan tsarin tattalin arzikin da muke kai ba zai iya barin mutane su rika sayan man ba yadda suke buƙata.

"Kullum mai saya yana cikin damuwa, saboda zai sanya kuɗaɗe masu yawa ya sayi mai da yake da tsammanin zai ɗauke shi dogon lokaci amma a ƙarshe haka zai ƙare kafin mai amfani da shi ya ankara," in ji Bashir.

A cewarsa "ta ko ina an ƙure mai siya da mai sayarwa".

'Zargin fasa-ƙaurin man a Legas'

Wani abu da masu dakon mai suke zargi shi ne, fasaƙaurin man da suke zargin ana yi na man a Legas.

"Farashin saifa ya yi sama a Benin, idan aka kai man can, ribar da ake samu tana ƙaruwa, hakan yasa muke zargin ana fasa-ƙaurin ma," in ji Dan Malan.

Sai dai masana harkokin yau da kullum na cewa ba za a iya musanta zargin ba kai tsaye, saboda akwai buƙatar a bibiya.

Matsalar man fetur dai lamari da ya daɗe yana ci wa 'yan Najeriya tuwo a ƙwarya, duk kuwa da kasancewarta ƙasar da ta fi kowace ƙasa arzikin man a nahiyar Afirka.